"Mai Jiran Gado": Martanin 'Yan Najeriya bayan El Rufai Ya Fice daga APC zuwa SDP
- Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya haƙura da ci gaba da zama a matsayin ɗan jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya
- Nasir El-Rufai ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar APC wacce yana daga cikin waɗanda aka assasa ta da su, zuwa SDP mai adawa
- Ƴan Najeriya sun bayyana mabambantan ra'ayoyi kan matakin da tsohon gwamnan ya Kaduna na ɗauka na fice daga APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya kawo ƙarshen zamansa mamba a jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.
Nasir El-Rufai ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar APC zuwa SDP mai adawa.

Asali: Twitter
Malam Nasir El-Rufai ya raba gari da APC
Tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya tabbatar da ficewa daga APC ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Facebook a ranar Litinin, 10 ga watan Maris 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tun a kwanakin baya ne dai aka fara raɗe-raɗin El-Rufai zai fice daga APC duba da yadda yake sukar jam'iyyar a bainar jama'a.
A cikin rubutun da ya yi, El-Rufai ya bayyana cewa ya miƙa takardar murabus ɗinsa ga shugabannin APC na mazaɓarsa da ke Kaduna.
Tsohon gwamnan ya nuna cewa ya fice daga APC ne saboda yadda ta kasa magance matsalolin da suka addabe ta.
Me ƴan Najeriya suka ce kan sauya sheƙar El-Rufai
Hassan Haruna:
"Shugaban ƙasa mai jiran gado, da yardar Allah Maɗaukakin Sarki."
Waheed Ishola Safiu:
"A ƙarshe, Mallam ya binne kansa da kansa a siyasance. Ina ganin zai fi kyau ga Mallam ya fara gwada farin jininsa daga jihar Kaduna."
Abdul Usman:
"El-Rufai ya bar APC saboda gwamnatin Tinubu ta gaza saka masa kan rawar da ya taka wajen tabbatar da BAT a matsayin Shugaban ƙasa."
"Da Tinubu ya ba shi muƙamin minista, da ba zai bar jam’iyyar ba. Yana kare maslaharsa ne kawai, kuma hakan ba laifi ba ne."
Cham Faliya Sharon:
"Masha Allah! Shugaban da jama’a ke bi ya yi magana! Ka yi gaba, mu biyo baya!"
Abdulbasid Dabai:
"Lissafi mara kyau, kujera bala'i ce, rashin ta masifa ne!"
Khalid Muazu Izala:
"A ƙarshe El-Rufai ya bayyana fushinsa kan rashin tabbatar da shi a matsayin minista kuma mamba a cikin majalisar Shugaba Tinubu. Ya kama ƴan Najeriya su fahimta cewa El-Rufai ba ya na faɗa ba ne saboda su!
Awelewa Blessing Olarewaju:
Lol! Da ace an ba ka muƙamin minista, duk yadda jam’iyyar ta taɓarɓare, da ba ka sauya sheƙa ba. Kawai kuna kare abin da za su samu ne. Kai ba ɗan kishin ƙasa ba ne."
Likitan Magani - Pharmacist:
"Ina taya ka murna shugaban ƙasar mu mai zuwa! Alhamdulillah! Yanzu lokaci ne na gina Najeriya irin wacce muke burin samu!
Abubuwan da suka tunzura El-Rufai ya koma SDP
A wani labarin kuma, mun kawo wasu dalilan da suka taka rawa wajen ficewar Nasir El-Rufai daga jam'iyyar APC zuwa SDP.
Tsohon gwamnan na jihar Kaduna dai ya yi ta maganganu tun bayan da gwamnatin Bola Tinubu ta hana shi muƙamin minista.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng