El Rufa'i Ya Yi Kaca Kaca da APC, Ya Tono Makircin da ake Kullawa a 2027
- Nasir El-Rufai ya ce akwai bukatar ceto dimokuradiyya a Najeriya yana mai kira ga jam’iyyun adawa su haɗa kai
- Ya yi gargadin cewa ana hasashen kashi 75% na masu kada kuri’a sun yanke shawarar ba za su fita zabe ba a 2027
- Tsohon gwamnan ya ce APC ta kauce wa manufofinta na farko kuma dole ne a dawo da martabar siyasar Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i, ya bayyana damuwarsa kan halin da dimokuradiyya ta tsinci kanta a Najeriya.
El-Rufa'i ya yi kira ga jam’iyyun adawa su hada kai domin kafa dandalin siyasa mai karfi da zai kare dimokuradiyya daga durkushewa.

Asali: Twitter
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa El-Rufa'i ya bayyana haka ne yayin wani taron kasa da aka gudanar domin karfafa dimokuradiyya a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon gwamnan ya ce idan ba a dauki matakan gyara ba, dimokuradiyyar Najeriya za ta iya rushewa gaba daya.
El-Rufa'i: Dimokuradiyya na fuskantar barazana
A cewar Nasir El-Rufa'i, yadda ake shirin rushe jam’iyyun adawa da kuma salon mulkin da ake aiwatarwa a yanzu ya kai ga a dauki matakan gyara da gaggawa.
Tsohon gwamnan ya ce:
“Dole ne mu dauki lamarin da muhimmanci domin kare dimokuradiyya daga lalacewa.”
Ya bayyana wani bincike da ke nuna cewa kashi 75% na masu kada kuri’a a Najeriya ba su da niyyar fita zabe a shekarar 2027.
“Wannan abu ne mai matukar hadari. Muna bukatar mu tashi tsaye, domin mu da muke da shekaru 60 mun san yadda rayuwa karkashin mulkin soja take.
"Ba mu so a koma irin wannan yanayi.”
Ya yi kira ga jam’iyyun adawa su yi koyi da hadin kan da aka yi wajen kafa APC a shekarar 2014, amma ya jaddada cewa dole ne a tabbatar da dimokuradiyya a cikin jam’iyyun tun daga tushe.
Ana kulla makirci ga 'yan adawa - El-Rufa'i
El-Rufa'i ya yi zargin cewa ana gudanar da wata manufa ta musamman domin rushe jam’iyyun adawa, musamman jam’iyyar PDP.
Malam Nasir El-Rufa'i ya ce:
“Akwai mutane da ke aiki a cikin PDP da aka dauka domin ganin jam’iyyar ta rushe.”
Ya kuma kara da cewa wannan bai tsaya ga PDP kadai ba, domin har jam’iyyar LP na fuskantar irin wannar matsalar.
Ya ambaci wata hira da aka yi da tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi, wanda ya bayyana cewa ba shi da masaniya kan abubuwan da ke faruwa a cikin jam’iyyar LP.
El-Rufai ya yi kira da cewa dole ne jam’iyyun adawa su manta da bambance-bambancen su, su hada kai domin kare dimokuradiyya.
El-Rufa'i ya yi kaca kaca da APC
A cewar El-Rufai, jam’iyyar APC ta rasa alkiblarta, kuma ta sauya daga jam’iyyar da aka kafa domin yakar cin hanci da rashawa da kuma kawo gyara.
Ya ce;
“APC ba ta gudanar da wani taro na masu ruwa da tsaki ba tsawon shekaru biyu. Ta zamo kamar tana aljihun wani mutum daya, ko babu shugabanci kwata-kwata.”
Ya bayyana cewa asalin burin kafa APC shi ne samar da jam’iyyar da za ta kawo cigaban kasa ta hanyar kyakkyawan shugabanci.
Ya kara da cewa:
“Ko da yake har yanzu ina cikin APC, amma akwai tazarar da ke kara tsawo tsakanin ni da jam’iyyar saboda abubuwan da ke faruwa.”
Magana kan zaben fitar da gwani
El-Rufa'i ya jaddada bukatar a samar da tsari wajen fitar da shugabannin siyasa da wadanda ke kada kuri’a a zabukan fitar gwani.
“Ba za ka ba jahilai ko wadanda ba su da cikakkiyar kwarewa ba ikon samar da shugabanni kuma ka yi tunanin samun shugabanci mai kyau ba.”
- Nasir Rufa'i
Ya ce idan ba a dauki irin wannan mataki ba, za a ci gaba da samun matsalar shugabanci kamar yadda ake fuskanta a yanzu.

Kara karanta wannan
'Su bar kujerunsu': Atiku ga yan siyasa da ke sauya sheka, ya fadi hanyoyin gyara dimukraɗiyya
A karshe, El-Rufai ya yi kira ga jam’iyyun adawa su kafa dandali mai karfi wanda zai kasance tamkar NPN na jamhuriya ta biyu.
Bayanin Dikko Radda bayan yin kuskure
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Kastina ya yi karin haske kan kuskuren da ya yi wajen ambaton PDP a yayi yakin neman zabe.
Gwamna Dikko Umaru Radda ya bayyana cewa kuskure dabi'a ce ta dan Adam kuma hakan ba ya nuna rashin goyon bayansa ga APC.
Asali: Legit.ng