Jerin Sanatoci 45 da Aka Zaba Domin Aikin Kwaskwarimar Kundin Tsarin Mulki a Majalisa

Jerin Sanatoci 45 da Aka Zaba Domin Aikin Kwaskwarimar Kundin Tsarin Mulki a Majalisa

  • An kafa kwamiti na musamman wanda za a ba alhakin aikin yin gyara a kundin tsarin mulkin Najeriya a majalisar dattawa
  • A ranar Laraba, shugabanmajalisar dattawan kasar nan, Godswill Akpabio, ya sanar da wannan cigaba da aka samu a Abuja
  • Kamar yadda Sanata Godswill Akpabio ya yi bayani, an zabi Sanata da zai wakilci kowace jiha, sai kuma aka kara wakili a yanki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abuja - Majalisar dattawa ta kafa wani kwamitin mutum 45 wanda zai yi aikin gyara da kwaskwarima a kundin tsarin mulkin kasa.

The Cable ta rahoto cewa shugaban majalisar dattawa na kasa, Godswill Akpabio, ya sanar da haka yayin zaman ranar Larabar nan.

Majalisar dattawa
Majalisar dattawa za ta gyara doka Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Jibrin zai rike kwamitin kwaskwarima a Majalisa

Godswill Akpabio ya ce mataimakinsa, Sanata Barau Jibrin zai shugabanci kwamitin.

Kara karanta wannan

Murna yayin da gwamnan APC ya fara raba kayan tallafi na biliyan 5 ga mabukata

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban majalisar yake cewa akwai bukatar ayi wa tsarin mulkin da ake amfani da shi garambawul saboda sauyin da ake samu.

Tsohon gwamnan na jihar Akwa Ibom ya ce lokaci ne yanzu da ake ganin canji a duniya musamman ta fuskar kimiyya da fasaha.

Majalisar tarayyar ta na so dokokin Najeriya su zama daidai da zamanin da ake ciki a yau.

Yadda aka zakulo Sanatocin a Majalisa

A matsayinsa na wanda zai jagoranci aikin, Barau Jibrin zai gayyaci shugabannin majalisun dokokin jihohi, ya tattauna da su.

Tribune ta ce an zakulo ‘yan kwamitin ne daga kowace jiha, sannan aka kara hada da wakili daga kowane yanki da kuma Abuja.

A kowace jiha an dauki Sanata guda ne, idan an samu kari shi ne wanda zai wakilci yankinsa, a haka aka tara mutane har 45.

Shugaan majalisan ya ce babu wata jam’iyya ko shiyya da aka manta da shi a kwamitin.

Kara karanta wannan

Shirin Pulaku: Gwamnati ta dauki mataki 1 tak na kawo karshen fadan makiyaya da manoma

Sunayen Sanatocin da ke kwamitin

1. Barau Jibrin

2. Opeyemi Bamidele

3. Oyelola Ashiru

4. Ali Ndume

5. Nwebonyi Onyeka

6. Abba Moro

7. Osita Ngwu

8. Oyewunmi Olalere

9. Sani Hanga

10. Enyinnaya Abaribe

11. Binus Dauda Yaroe

12. Bassey Etim Akpan

13. Ifeanyi Ubah

14. Abdul Ningi

15. Seriake Dickson

16. Agom Jarigbe

17. Ned Nwoko

18. Adams Oshiomole

19. Danjuma Goje

20. Osita Izunaso

21. Abdulhamid Ahmed

22. Khalid Mustapha

23. Sani Rufai

24. Mutari Dandutse

25. Yahaya Abdullahi

26. Natasha Akpoti-Uduaghan

27. Adebule Oluranti

28. Ugodiya Akwashiki

29. Sani Musa

30. Adeola Olamilekan

31. Adeniyi Ayodele

32. Abdulfatai Buhari

33. Simon Lalong

34. Aliyu Wamako

35. Shuaibu Lau

36. Ahmed Lawan

37. Sahabi Alhaji Ya’u

38. Ireti Kingigbe

39. Ipalibo Banigo

Sanatoci masu wakiltar yanki

40. Adamu Aliero (Arewa maso yamma)

41. Orji Uzor Kalu (Kudu maso gabas)

42. Francis Fadahunsi (Kudu maso yamma)

43. Bomai Mohammed (Arewa maso gabas)

44. Barinada Mpigi (Kudu maso kudu)

45. Umar Sadiq Sulaiman (Arewa maso tsakiya)

Kiran PDP ga Gwamnatin Tinubu

Muddin Bola Tinubu bai tashi tsaye ba, an ji labari Gwamnonin PDP sun ce Najeriya za ta bi tafarkin kasar Venezuela ta fuskar tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Hanya 1 tak da jami'an tsaron Najeriya suka dauka don kama 'yan ta'adda cikin sauki

Venezuela kasa ce mai arziki amma sai ga shi ana fama da rushewar tattali, Bala Mohammed ya ce Najeriyata kama wannan hanya a yau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel