Hanya 1 Tak da Jami’an Tsaron Najeriya Suka Dauka Don Kama ’Yan Ta’adda Cikin Sauki

Hanya 1 Tak da Jami’an Tsaron Najeriya Suka Dauka Don Kama ’Yan Ta’adda Cikin Sauki

  • A yayin da matsalar tsaro ta kara ta'azzara a Najeriya, hukumomin tsaro za su fara amfani da NIN, BVN wajen kama masu aikata laifi
  • Hukumomin tsaron sun cimma wannan matsayar ne a wata ganawar sirri da suka yi da majalisar dattawa a ranar Talata
  • Hakazalika hukumomin tsaron za su samu lasisin kutsawa cikin rumbun adana bayanan 'yan kasa a duk lokacin da suka bukata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Jami’an tsaron Najeriya sun yanke shawarar yin amfani da lambar tantancewa ta kasa (NIN) da kuma lambar BVN wajen zakulo masu aikata laifuka da kuma kama su.

Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Yemi Adaramodu ne ya bayyana hakan a ranar Talata.

Kara karanta wannan

AFCON: Tinubu ya aika muhimmin sako ga Super Eagles bayan ta yi rashin nasara a wasan karshe

Za a fara amfani da BVN da NIN wajen kama masu aikata laifi
Hafsoshin tsaro sun gana da majalisar da dattawa kan tabarbarewar tsaro a kasar. Hoto: @NGRSenate
Asali: Facebook

Shugabannin tsaron sun bayyana a gaban majalisar dattawa a ranar Talata, tare da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, da kuma ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Leadershipt ta ruwaito cewa ministan kudi kuma ministan tattalin arziki Olawale Edun da ministan harkokin ‘yan sanda Ibrahim Geidam na cikin mahalarta taron.

Abubuwan da aka tattauna a wajen taron

Taron tsaron dai an yi shi ne a bayan fage wanda aka kwashe kusan awanni 9 ana yi.

Kakakin Majalisar dattijai ya yi wa manema labarai karin haske jim kadan bayan kammala taron na sirri a Abuja kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Ya ce wani bangare na kudurorin da aka cimma a taron shi ne za a gano masu laifi da tsarin lambobin tantancewa.

“Mun yi magana kan yadda za mu kama masu laifi ta hanyar VIAM, BVN, NIN da sauransu domin mu hada dukkan shaidu yayin gurfanar da su.

Kara karanta wannan

An ji kunya: Matasa masu karfi a jika sun kashe zuciyarsu, sun sace fanka a masallaci

"Yana nufin cewa a karamin lokaci, za mu iya gano bayanan mutum ta yadda ba wani dan kasa da zai aikata laifi ace an rasa bayanansa a kundi."

- A cewar Adaramodu

An warware sabanin da ke tsakanin hukumomin tsaro

Kudurin dai na nufin dukkan hukumomin tsaro za su samu damar shiga rumbun adana bayanan ‘yan Najeriya tare da hada kai a tsakaninsu.

An gano adawa tsakanin hukumomin tsaro da rashin hadin kai tsakanin su ya haifar da kalubale wajen samar da tsaro a Najeriya.

Matsalar tsaro ta kara ta'azzara a sassa da dama na Najeriya inda a kullum ake samun rahotannin kashe-kashe da garkuwa da mutane.

Majalisa za ta duba yiwuwar kirkirar sabbin jihohi 3

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa wani dan majalisar tarayya, Oluwole Oke, ya gabatar da kudirin kirkirar sabbin jihohi uku a shiyyar Kudu maso Yamma.

Kara karanta wannan

Gasar AFCON: An shiga karancin rigunan Super Eagles a Kano, 'yan kwasuwa sun kwashi ganima

Oke-Ogun, Ijebu da Ife-Ijesa su ne sunayen jihojin da Mista Oke ya ke so majalisar ta kirkira.

Idan har kudirin ya zama doka, shiyyar Kudu maso Yamma za ta fi kowacce shiyya yawan jihohi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel