Sanata Barau Jibrin: Muhimman Abubuwan Sani Dangane Da Sabon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa

Sanata Barau Jibrin: Muhimman Abubuwan Sani Dangane Da Sabon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa

A yau Talata, 13 ga watan Yuni, Sanata Barau Jibrin, ya zama mataimakin shugaban majalisar dattawa ta 10 ba tare da abokin hamayya ba.

Ɗan siyasan wanda ya fito daga jihar Kano, wanda shi ne karonsa na uku yana zuwa majalisar dattawa, ya samu ƙwarewa tun daga majalisar wakilai.

Abubuwan sani dangane da Sanata Barau Jibrin
Sanata Barau Jibrin, mataimakin shugaban majalisar dattawa Hoto: @Baraujibrin
Asali: Twitter

Ga wasu muhimman abubuwa dangane da sabon mataimakin shugaban majalisar dattawan.

Ranar haihuwa

Sanato Barau Jibrin, ɗan asalin garin Kabo cikin ƙaramar hukumar Kabo ta jihar Kano, an haife shi ne a shekarar 1959, cewar rahoton Biographical Legacy and Research Foundation.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Karatunsa

Barau yana da digiri a fannin lissfin kuɗi. Mataimakin shugaban majalisar dattawan yana da digirin digir a fannin 'Financial Management and pricing' da MBA.

Kara karanta wannan

Abubuwa 5 da Ya Kamata ku sani Game da Akpabio, Sabon Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya

Ya yi karatu a ƙasar Amurka inda ya samu satifiket a fannin 'Financial Management for business decisions' daga jami'ar Cornell.

Siyasa

Barau ya fara siyasa ne a shekarar 1999 lokacin da aka zaɓe shi ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Tarauni daga jihar Kano.

A lokacin da yake majalisar wakilai, Sanata Barau ya shiga cikin kwamitoci da dama inda ya shugabanci wasu daga ciki.

Bayan ya bar majalisar wakilai, an naɗa shi kwamishinan kimiyya da fasaha na jihar Kano.

Barau a majalisar dattawa

Shekara 16 bayan fara siyasarsa a jihar Kano, Sanata Barau ya yi takarar sanatan Kano ta Arewa a shekarar 2015 inda ya samu nasara a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Ya sake lashe zaɓen sanata a karo na biyu a shekarar 2019. Kamar yadda Premium Times ta rahoto, Barau ya sake lashe zaɓen sanata a karo na uku a watan Fabrairun 2023.

Kara karanta wannan

Bayan Ganawa da Tinubu, Gwamnan APC Ya Faɗi Sanatan da Zai Zama Shugaban Majalisar Dattawa

Yunƙurin zama gwamna

A cewar jaridar The Guardian, Sanata Barau ya bayyana aniyarsa ta gadar gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje a shekarar 2023, inda fastocinsa suka karaɗe ko ina a Kano.

Barau ya yi rikicin siyasa da mataimakin gwamna Nasiru Yusuf Gawuna (wanda ya zama ɗan takarar gwamnan APC) da tsohon kwamishinan ƙananan hukumomi da harkokin masarautu, Murtala Sule Garo.

Daga baya Sanata Barau ya janye takarar gwamna inda ya amince da zaɓin Nasir Yusuf Gawuna a matsayin ɗan takarar gwamnan jihar.

Abubuwa 6 Masu Muhimmanci Dangane Da Tajudeen Abbas

Rahoto ya zo kan muhimman abubuwan sani dangane da sabon shugaban majalisar wakilai ta 10, Tajudeen Abbas.

Tajudeen Abbas wanda ya fito daga jihar Kaduna ya zama sabon kakakin majalisar wakilan ne bayan ya tiƙa Idris Wase da Sani Jaji da ƙasa a zaɓen da aka gudanar ranar Talata, 13 ga watan Yuni.

Wannan ne karo na uku da sabon kakakin yake wakiltar mazaɓar Zaria daga jihar Kaduna a majalisar wakilai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng