Shirin Pulaku: Gwamnati Ta Dauki Mataki 1 Tak Na Kawo Karshen Fadan Makiyaya da Manoma

Shirin Pulaku: Gwamnati Ta Dauki Mataki 1 Tak Na Kawo Karshen Fadan Makiyaya da Manoma

  • Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya kaddamar da kwamitin aiwatar da wani sabon shirin Shugaba Tinubu mai taken "Pulaku"
  • A ranar Talata yayin kaddamar da kwamitin, Shettima ya ce shirin Pulaku zai kawo karshen fadan makiyaya da manoma a Najeriya
  • Ministan gidaje da raya birane, Arc. Ahmed Musa Dantigawa ne zai jagoranci kwamitin da gwamnonin jihohi matsayin mambobi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Gwamnatin tarayya ta kaddamar da wani kwamitin aiwatar da shirin na ‘Pulaku’, da nufin magance matsalolin rikicin manoma da makiyaya da kuma samar da hadin kan kasa.

'Pulaku' kalmar Fulani ce da ke nufin 'jin kunya'.

Shettima ya kaddamar da 'Shirin Pulaku' don kawo karshen fadan makiyaya da manoma.
Shettima ya kaddamar da 'Shirin Pulaku' don kawo karshen fadan makiyaya da manoma. Hoto: @officialSKSM
Asali: Twitter

A watan Yulin 2023, The Cable to ruwaito mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya ce sojoji kadai ba za su iya magance rikicin yankin arewa maso yammacin kasar ba.

Kara karanta wannan

Hanya 1 tak da jami'an tsaron Najeriya suka dauka don kama 'yan ta'adda cikin sauki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jihohin Arewa ne za su amfana da shirin

Gwamnatin Tinubu ta kafa wannan shiri wanda ba na amfani da makami ba, domin magance matsalolin tada kayar baya, da ‘yan fashi da kuma talauci a yankin Arewa.

A saboda haka, mataimakin shugaban kasar, a ranar Talata, ya kaddamar da kwamitin domin aiwatar da shirin wada ake fatan zai inganta rayuwar ‘yan Nijeriya baki daya.

Jihohin Sokoto, Kebbi, Benue, Katsina, Zamfara, Niger, da Kaduna su ne jihohin da za su ci gajiyar shirin, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Wadanda aka nada domin jagorantar kwamitin

Kwamitin wanda ministan gidaje da raya birane Arc. Ahmed Musa Dangiwa zai jagoranta yana da wakilan gwamnonin jihohin da abin ya shafa a matsayin mambobi.

Sauran mambobin sun hada da Abubakar Kyari, ministan noma da samar da abinci; wakilan gwamnonin jihohi bakwai; da shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC).

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta kafa hukumar kayayyakin masarufi don daidaita farashin kayan abinci

Akwai kuma babban darektan ofishin kasuwancin jama'a (BPP); babban daraktan hukumar bada agajin gaggawa ta kasa (NEMA); Kamfanin Dangote da na BUA.

Karin haske game da shirin Pulako

Da yake jawabi a yayin kaddamarwar, Shettima ya ce shirin Pulako wani aiki ne na kasa don fuskantar barazanar da ta haifar da rashin yarda da rikice-rikice tsakanin al'ummomi da kuma kan iyakokin tarayya.

Mataimakin shugaban kasar ya ce ba a shirya wannan shiri ne domin biyan wata kungiya ko yanki diyya ba, kuma an zabi jihohin da shirin zai shafa bisa cancanta.

Gwamnati ta kafa hukumar daidaita kayayyakin masarufi

A hannu daya kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya kaddamar da hukumar kayayyakin masarufi a Abuja.

Hukumar kamar yadda Shetima ya bayyana, za ta yi aiki tukuru don ganin ta daidaita farashin kayayyakin abinci a kasuwannin Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel