Murna Yayin da Gwamnan APC Ya Fara Raba Kayan Tallafi Na Biliyan 5 Ga Mabukata

Murna Yayin da Gwamnan APC Ya Fara Raba Kayan Tallafi Na Biliyan 5 Ga Mabukata

  • Yayin da al'ummar Najeriya ke kokawa saboda tsadar rayuwa da hauhawan farashin kaya, gwamnatin jihar Ogun ta dauki matakin sharewa talakawanta hawaye
  • Gwamna Dapo Abiodun ya ware kudi naira biliyan biyar domin aiwatar da shirin raba kayan tallafi ga dalibai da marasa gata
  • Daliban jami'a, na firamare da sakandare za su samu tallafin kudi sannan za a rabawa iyalai kayan abinci da suka hada da shinkafa, garin kwaki da sauransu

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Ogun - Gwamnatin jihar Ogun ta bayyana aniyarta na fara aiwatar da wani shiri na naira biliyan 5 domin ragewa al'umma radadin halin da ake ciki na matsin tattalin arziki.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa Gwamna Dapo Abiodun, ne ya sanar da hakan a yammacin ranar Laraba, 14 ga watan Fabrairu a wani taron manema labarai na gaggawa a cibiyar labarai ta Olusegun Osoba da ke ofishin gwamna na Oke Mosan.

Kara karanta wannan

Fitaccen malami ya yi hasashen sabon farashin naira kan dala, ya ce buhun shinkafa zai kai 90k

Gwamnan Ogun zai raba tallafi
Ana tsallan murna yayin da gwamnati ta fara rabon kayan tallafi na biliyan 5 ga mabukata Hoto: Mubarak Kolawole Salisu
Asali: Facebook

Gwamna Abiodun ya ce shirin ya shafi bayar da tallafi ga dalibai marasa galihu, tallafin abinci ga gidajen talakawa, inshoran lafiya ga mata masu juna biyu da sauransu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaya za a yi rabon tallafin?

Da yake bayani dalla-dalla, gwamnan na APC ya sanar da cewar za a bayar da tallafin N50,000 ka wanne daga cikin dalibai 27,600 'yan asalin jihar Ogun da ke fadin makarantun jami'a a kasar.

Haka kuma, za a bai wa daliban makarantun firamare da na sakandare 100,000 tallafin N10,000 baya ga takardun rubutu biyar-biyar da za a bai wa daliban makarantun firame da sakandare 850,000, rahoton Nigerian Tribune.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa za a rabawa iyalai 300,000 a jihar kayan abinci da suka hada da garin kwaki, shinkafa da sauransu, yayin da za a ba da naira miliyan 500 duk wata don daidaita kudaden da ake cirewa ma’aikata.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Gwamnan Arewa ya sharewa iyalai 70,000 hawaye, ya raba kayan abinci na miliyan 225

Gwamnan ya kuma yaba juriya, hakuri da fahimtar daukacin al'ummar jihar Ogun yayin da kasar ke fama da matsin tattalin arziki inda ya ce lamarin zai zama tarihi nan ba da jimawa ba.

Ya bayyana cewa duk sadaukarwar da ake yi a yau, 'saboda gobenmu ya inganta ne'.

FG za ta janye tallafin wutar lantarki

A wani labarin kuma, mun ji cewa ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya ce Najeriya ba za ta iya ci gaba da bayar da tallafin wutar lantarki ba, inda ya ce kasar na bukatar fara aiwatar da tsari na daban mai inganci.

Ya ce hakan ya faru ne saboda basussukan da kamfanonin samar da wutar lantarki (Gencos) da na iskar gas ke bin kasar, rahoton The Nation.

Asali: Legit.ng

Online view pixel