Zaben 2023: Abokin takarar Tinubu na wucin gadi zai iya jefa shi cakwalkwali, hasashen masana a INEC

Zaben 2023: Abokin takarar Tinubu na wucin gadi zai iya jefa shi cakwalkwali, hasashen masana a INEC

  • Jiga-jigai a sanin fannin siyasa da lamurran kasa sun yi hasashe sun ce ana iya samun matsala a APC da LP
  • Ganin yadda jam'iyyun suka zabo abokan takarar, masana sun yi maganganu kan matsalolin da za a iya samu
  • Jam'iyyar APC da LP ne suka zabo 'yan takarar da ake sa ran na wucin gadi ne, wanda ake kuma tunanin zai iya zuwa da matsala

Najeriya - Tsoffin daraktocin hukumar zabe mai zaman kanta da kuma masu hasashe a Najeriya sun yi gargadin cewa jam’iyyun siyasa na iya fuskantar rikici kan zaben fitar da gwanin da suka yi da kuma zabo abokan takarar a zaben shugaban kasa na 2023.

Tsofaffin jami’an alkalan zaben, wadanda suka zanta da jaridar Punch, sun gargadin cewa jam’iyyu da ‘yan takararsu na iya gamuwa da tasgaron rashin nasara a zaben shugaban kasa, idan wanda aka zaba a matsayin abokin takaran wucin gadi ya ki amincewa a sauya shi.

Kara karanta wannan

Musulmi da Musulmi: Zanga-zanga ta barke a sakateriyar APC saboda adawa da zabin Tinubu

Matsalar da Tinubu da APC za su iya shiga
Zaben 2023: Yadda abokin takarar wucin gadi ka iya jefa Tinubu da Obi cakwalkwalin faduwa | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Wani batu da tsofaffin jami’an hukumar zabe ta INEC suka yi shi ne cewa jam’iyyu da ‘yan takararsu na iya rasa tikitin takara idan abokin takarar da bai cancanci zama mataimakin shugaban kasa ba ya ki janyewa daga takarar.

Yadda labarin ya faro

Gabanin wa'adin da INEC ta sanya, da misalin karfe 6:00 na yamma a ranar Juma'a jam'iyyun siyasa da dama sun mika sunayen 'yan takarar shugaban kasa na rikon kwarya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Daga cikin su akwai dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, wanda ya zabi Kabiru Masari, a matsayin abokin gami.

Jam’iyyar Labour ta mika sunan Darakta-Janar na kungiyar yakin neman zaben Peter Obi, Dr Doyin Okupe, a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa na wucin gadi na jam’iyyar.

Dukkanin jam’iyyun siyasa na da kwanaki 30 na janye sunayen wadannan ’yan takarar na wucin gadi tare da musanya su da wasu dalilai.

Kara karanta wannan

Hajjin bana: ‘Yan bindiga sun tare Maniyyata a hanyar filin jirgi, su na shirin zuwa Saudi

Sai dai tsofaffin manyan jami’an hukumar ta INEC da manyan lauyoyi sun bayyana ra’ayinsu game da tsarin.

Gargadi daga masana siyasa da makomar ta

Wani tsohon Daraktan wayar da kan kan masu kada kuri’a a INEC, Nick Dazang, ya bayyana cewa ‘yan takarar na kokarin wucewa ta kofar da dokar zabe ta tanada ne kawai inda ta ce za a iya musanya abokin takara.

A cewarsa, 'yan takarar shugaban kasa suna duba abokan takarar da za su ba da daidaito na kabilanci da addini ga tikitin su ne, suna kuma da kimar zabe da kuma iya kawo kuri'u a zabe.

Dazang ya kuma yi tsokaci kan abin da zai faru da tikitin idan abokin takarar bai cancanci zama mataimakin shugaban kasa ba. Ya bayar da misali da yadda aka kai ruwa rana a zaben gwamna da ya gabata a jihar Bayelsa.

A ranar 13 ga Fabrairu, 2020, Kotun Koli ta soke zaben dan takarar jam’iyyar APC, Mista David Lyon, da abokin takararsa, Biobarakuma Degi-Eremienyo, a jajibirin rantsar da su kan wasu kura-kurai a cikin takardun abokin takara.

Kara karanta wannan

Dangin gwamna: Muhimman abubuwa 8 da baku sani ba game da abokin takarar Tinubu

A bangaren wani tsohon Daraktan wayar da kan masu kada kuri’a a INEC, Oluwole Osaze-Uzi, ya bayyana cewa dokar ba ta amince da batun maye gurbin ba, inda ya kara da cewa “doka ta amince da ‘yan takara ne kawai” wadanda dole ne su cancanci mukaman da suke nema.

Ya kuma bayyana cewa "idan dan takara - wanda kuke kira na wucin gadi - ya ki janyewa, ba za a iya yin komai akai ba."

A cewar Osaze-Uzi, za a iya maye gurbin dan takarar mataimakin shugaban kasa ne kawai idan ya janye da kansa sannan jam’iyya ta sanar da INEC cikin lokacin da doka da hukumar suka kayyade.

Matsayar INEC

Game da cece-kucen, kwamishinan INEC na kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a, Festus Okoye, ya magantu kan matsayar INEC.

Ya ce kowace jam’iyya za ta iya maye gurbin abokan takara ta hanyar rubuta wasika hukumar INEC, da kuma hada wa da takardar shaidar kotu ta yin hakan.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Hatsaniya Ta Barke a Hedkwatar APC Na Kasa, Matasa Na Yi Wa Adamu Barazana

Okoye, wanda ya bayyana haka a wata hira da aka yi da shi a gidan Talabijin na Arise TV a ranar Litinin, ya ce:

“A iya saninmu, babu wani fom da ‘yan takarar shugaban kasa suka kawo inda suka ce sun mika sunan wannan mutum ne a matsayin na wucin gadi."

Kwararrun lauyoyi sun magantu

A halin da ake ciki kuma, wasu lauyoyin sun ce doka ta bai wa ‘yan takarar shugaban kasa damar gabatar da abokan takarar wucin gadi ga INEC tare da maye gurbinsu daga baya.

Shugaban Hukumar Kamfen din Tinubu, Babatunde Ogala, SAN, ya bayyana cewa dokar zabe ta 2022 ta baiwa jam’iyyar siyasa damar sauya abokan takara har zuwa watanni uku kafin zabe.

Ogala, wanda tsohon mashawarcin shari’a ne na jam’iyyar APC, ya ki tabbatar da ko hakan wani shiri ne na juyin siyasa ko kuma Tinubu ya yanke hukunci na karshe kan abokin takararsa.

Wani SAN, Wole Olanipekun, ya bayyana cewa babu wani abu a bisa ka’ida wajen tsayar da ‘yan takarar mataimakin shugaban kasa tare da sauya shi domin kakkabe wa'adi.

Kara karanta wannan

Dalilin da Yasa na Darzo Okowa A Matsayin Abokin Takarata a 2023, Atiku Abubakar

Duk kokarin da aka yi don jin ta bakin sakataren yada labaran jam’iyyar APC Felix Morka ya ci tura. Har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, har yanzu bai amsa kiran waya ba ko sakon Whatsapp.

Da aka tambaye shi dalilin da ya sa jam’iyyar ta mika sunan dan takarar, shugaban jam’iyyar Labour ta kasa, Julius Abure, ya shaida wa Punch cewa ba sabon abu ba ne a harkar siyasa da zabe.

Wakilin Legit.ng Hausa ya tuntubi Haruna Musa Abdullahi, malamin kimiyyar siyasa a jami'ar tarayya kuma mai sharhi kan siyasar Najeriya, ya ce:

"Duk da cewa ba sabon abu bane, ana iya samun matsala, amma dai duba da siyasar Najeriya komai zai iya faruwa na ban mamaki.
Babu wanda ya yi tsammanin ganin Alhaji Kabiru a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa na APC, amma mun ga yadda aka zabe shi, to sauya shi abu ne mai sauki kuma ba lallai ya zama damuwa ba a nawa ra'ayin."

Kara karanta wannan

Mataimakin shugaban kasa: Daga karshe Tinubu ya fayyace gaskiyar lamari kan tikitin Musulmi da Musulmi

Koma baya: APC ta gigice, jiga-jiganta a Katsina, Sokoto da Bauchi sun sauya sheka

A wani labarin, wasu jiga-jigan jam’iyyar APC guda shida da suka hada da ‘yan majalisa da kuma tsohon mataimakin gwamna sun fice daga jam’iyyar tare da sauya sheka zuwa wasu jam’iyyun siyasa daban-daban a jihar Bauchi.

Ficewar dai babbar illa ce ga burin jam’iyyar na ganin bayan jam’iyyar PDP mai mulki a jihar a zaben gwamna na 2023. Gwamna mai ci Bala Mohammed na neman wa’adinsa na biyu kuma na karshe a matsayin gwamna.

Tashin hankalin ficewa daga jam’iyyar APC ya tsallaka jihar Bauchi. A wasu jahohin Arewacin kasar nan ma ‘yan jam’iyyar sun koka kan yawan ficewa da shiga wasu jam’iyyun siyasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel