Dangin gwamna: Muhimman abubuwa 8 da baku sani ba game da abokin gamin Tinubu

Dangin gwamna: Muhimman abubuwa 8 da baku sani ba game da abokin gamin Tinubu

  • Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki, Bola Tinubu ya zabi abokin takararsa na zaben 2023
  • Babban jagoran jam’iyyar na kasa ya zabi Alhaji Kabir Ibrahim Masari a matsayin abokin takararsa gabannin cikar wa’adin da INEC ta dibarwa jam’iyyu
  • Ana sa ran Tinubu zai tuntubi shugaban kasa Buhari kan lamarin domin zai yi wuya ya samu hadin kan gwamnonin APC wadanda suka mara masa baya ya zama dan takarar jam’iyyar

Asiwaju Bola Tinubu, dan yakarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki, ya gabatar da sunan Alhaji Kabir Ibrahim Masari a matsayin abokin takararsa a zaben shugaban kasa na 2023.

Daily Trust ta rahoto cewa Tinubu ya gabatar da sunan nasa ne gabannin cikar wa’adin da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta dibar wa jam’iyyun siyasa don su gabatar da sunayen yan takararsu na zaben 2023.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Tinubu ya zabi Musulmi a matsayin abokin tafiyarsa a zaben 2023 a APC

Dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu tare da abokin takararsa, Kabir Ibrahim Masari
Dangin gwamna: Muhimman abubuwa 8 da baku sani ba game da abokin takarar Tinubu Hoto: APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

A halin da ake ciki, jam’iyyar ta tsinci kanta cikin cece-kuce yayin da kungiyoyi a cikin jam’iyyar suka mayar da tsarin zabar abokin takara ya koma kamar gasar addini da kabilanci, AIT ta rahoto.

An yarda da mika sunan Masari kamar yadda yake bisa tanadin dokar zabe ta 2022 amma za a sauya sunan nasa bayan an cimma matsaya kan wanda ya fi karbuwa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A wannan zauren Legit.ng ta tattaro maku wasu abubuwa game da abokin takarar Tinubu, Masari.

Ya fito daga jihar Buhari, Katsina

Abokin takarar na dan takarar shugaban kasa na APC ya fito ne daga Masari, wani kauye a karamar hukumar Kafur da ke jihar Katsina, mahaifar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ya kasance dan uwan gwamna

Alhaji Kabir Ibrahim Masari daga jihar Katsina, tsohon sakataren kungiyar magoya bayan Buhari ya kasance dan uwan Rt. Hon. Aminu Bello Masari, gwamnan jihar Katsina mai ci a yanzu.

Kara karanta wannan

Abokin takarar Tinubu: Kungiyar APC ta tsayar da gwamnan Neja, Sani Bello

Ya kasance mamba na hukumar NIPSS

Ya kasance mamba ne a hukumar kula da manufofi da tsare-tsare ta kasa (NIPSS) da ke Kuru, kusa da Jos, babban birnin jihar Plateau.

Ya yi aiki a karkashin Adams Oshiomhole, tsohon shugaban APC

Abokin takarar Tinubun ya yi aiki a matsayin sakataren kula da jin dadin jam’iyyar na kasa a lokacin gwamnatin Kwamrad Adams Oshiomhole.

Ya kasance tsohon jigon PDP

Abokin takarar Tinubun ya kasance dan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a lokacin mulkin marigayi Umaru Musa Yar’Adua.

Ya yi aiki a karkashin mulkin marigayi tsohon shugaban kasa Yar’Adua

Bayan mutuwar Yar’Adua a 2010, Masari ya sauya sheka zuwa jam’iyyar Congress for Progressives Change (CPC), wanda a karkashinta ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi takara a zaben 2011 amma ya sha kaye.

Ya kasance jigon CPC

Gabannin babban zaben 2015, jam’iyyar CPC ta rushe tsarinta inda ta hade da APC sannan Masari ya koma jam’iyyar mai mulki.

Kara karanta wannan

Mataimakin shugaban kasa: Daga karshe Tinubu ya fayyace gaskiyar lamari kan tikitin Musulmi da Musulmi

Ya taka rawar gani a zabe

Ya kuma taka rawar gani a zaben wanda jam’iyyar adawa ta yi nasara kan jam’iyya mai mulki karo na farko a tarihin kasar.

Dole Bola Tinubu Ya Fada Wa Yan Najeriya Yadda Ya Tara Dukiyarsa, In Ji Deji Adeyanju

A wani labarin, Deji Adeyanju, dan gwagwarmayar siyasa kuma shugaban kungiyar 'Concerned Nigerians' ya ce akwai bukatar dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu, ya fada ya yi bayanin yadda ya tara dukiyarsa, The Cable ta rahoto.

Adeyanju ya yi magana ne a baya-bayan nan cikin hira da aka yi da shi ta intanet a shirin 90MinutesAfrica - wanda Rudolf Okonkwo da Chido Onumah suka gabatar.

A ranar 8 ga watan Yuni an sanar da Tinubu matsayin dan takarar APC a zaben 2023 bayan ya lashe zaben fidda gwani da kuri'u 1,271.

Asali: Legit.ng

Online view pixel