Musulmi da Musulmi: Zanga-zanga ta barke a sakateriyar APC saboda adawa da zabin Tinubu

Musulmi da Musulmi: Zanga-zanga ta barke a sakateriyar APC saboda adawa da zabin Tinubu

  • Wasu matasa da aka ce 'yan jam'iyyar APC ne sun mamaye farfajiyar sakateriyar jam'iyyar a babban birnin tarayya Abuja
  • Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, sun taru ne domin nuna adawa da shirin Bola Tinubu na zabo musulmi abokin takara
  • Rahoton ya kuma ce, ba a biya matasan da suka zo zanga-zangar ba, lamarin da ya tunzura su suka shiga rawan sanyi

Abuja - Daruruwan masu zanga-zanga ne suka mamaye sakateriyar APC a ranar Talata domin nuna adawa da ba da tikitin mataimakin shugaban kasa a jam'iyyar, Punch ta ruwaito.

A wani mataki na gaggawa, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Bola Tinubu, zai bayyana musulmi a matsayin mataimakinsa, inda ya zabi Alhaji Kabir Ibrahim Masari a matsayin wanda zai tsaya masa a takarar shugaban kasa a 2023.

Kara karanta wannan

Zulum ne ya fi cancanta ya zama abokin takarar Tinubu, in ji kungiyar masu ruwa da tsaki na APC

Matakin dai bai yiwa ‘yan Najeriya da dama dadi ba, ciki har da malaman addini da kungiyoyi irin su kungiyar kiristoci ta Najeriya, wadda ta gargadi jam’iyyun siyasa da gudun tafarkin nuna son kai.

An yi zanga-zangar nuna adawa da tsarin Tinubu
Musulmi da Musulmi: An mamaye sakateriyar APC saboda adawa da zabin Tinubu | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Bulaliyar Majalisar Dattawa, Orji Uzor Kalu, ya nuna cewa tunda tsohon Gwamnan Jihar Legas ya samu tikitin takarar shugaban kasa, to ko babu wani zabi illa ta tsayar da Musulmi a matsayin mataimakinsa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kalu, wanda ya goyi bayan tsarin Tinubu da jam’iyya mai mulki, ya kuma yi ikirarin cewa jam’iyyar za ta yi gwagwarmayar lashe zaben shugaban kasa idan har ta yanke shawarar yin watsi da ra’ayin.

Da suke kalubalantar matakin a ranar Talata, masu zanga-zangar da dama sun taru a gaban Sakateriyar jam’iyyar APC suna ta kururuwa dauke da tutoci da ke nuna ‘Yan Najeriya ba za su zabi shugabanni Musulmi da Musulmi a zaben 2023 ba.'

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Tinubu ya zabi Musulmi a matsayin abokin tafiyarsa a zaben 2023 a APC

Masu zanga-zangar, wadanda suka isa cikin motocin bas guda uku na alfarma, sun dura hedikwatar jam’iyyar ne yayin da jami’an tsaro da cikakken bayani a sakatariyar suka yi barazanar tarwatsa su idan suka wuce gona da iri.

Zanga-zangar ta dauki tsawon sa'o'i, jim kadan aka ga wasu daga cikin masu zanga-zangar suna tsugunne a karkashin wata bishiya da ke kusa da sakatariyar, suna rawar sanyi.

Wasu kuma sun nemi mafaka a Cocin ECWA da ke kusa da su yayin da suke ci gaba da jiran motocin bas din da a baya suka sauke su su dawo.

An ji daya daga cikin masu zanga-zangar, mai suna Yakubu, yana kukan cewa ba a biya su kudin zanga-zangar da suka yi ba.

Ya ce:

“Mutanen nan sun bar mu cikin ruwan sama ba tare da sun dawo ba. Wasu daga cikinmu sun taho ne tun daga Maraba, Suleja da Dei-Dei domin nuna goyon bayansu ga wannan zanga-zangar.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Hatsaniya Ta Barke a Hedkwatar APC Na Kasa, Matasa Na Yi Wa Adamu Barazana

"Har yanzu wadanda suka shirya zanga-zangar ba su yi wani shiri na daukarmu ko biyan mu ba."

Wata tsohuwa da ta yi magana da Independent ta ce:

“Sun kawo mu daga wurare daban-daban daga wajen Abuja. Ni 'yar Dei-Dei ce, wasu daga Suleija wasu kuma daga Maraba.

"An gaya mana cewa za mu samu dubu uku kowanne bayan zanga-zangar amma tunda muka gama babu wanda da ya yi magana da mu, bas din ma da ta kawo mu bata dawo ba.”

Zaben 2023: Abokin takarar Tinubu na wucin gadi zai iya jefa shi cakwalkwali, hasashen masana a INEC

A wani labarin, tsoffin daraktocin hukumar zabe mai zaman kanta da kuma masu hasashe a Najeriya sun yi gargadin cewa jam’iyyun siyasa na iya fuskantar rikici kan zaben fitar da gwanin da suka yi da kuma zabo abokan takarar a zaben shugaban kasa na 2023.

Kara karanta wannan

Dalilin da Yasa na Darzo Okowa A Matsayin Abokin Takarata a 2023, Atiku Abubakar

Tsofaffin jami’an alkalan zaben, wadanda suka zanta da jaridar Punch, sun gargadin cewa jam’iyyu da ‘yan takararsu na iya gamuwa da tasgaron rashin nasara a zaben shugaban kasa, idan wanda aka zaba a matsayin abokin takaran wucin gadi ya ki amincewa a sauya shi.

Wani batu da tsofaffin jami’an hukumar zabe ta INEC suka yi shi ne cewa jam’iyyu da ‘yan takararsu na iya rasa tikitin takara idan abokin takarar da bai cancanci zama mataimakin shugaban kasa ba ya ki janyewa daga takarar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel