Hajjin bana: ‘Yan bindiga sun tare Maniyyata a hanyar filin jirgi, su na shirin zuwa Saudi

Hajjin bana: ‘Yan bindiga sun tare Maniyyata a hanyar filin jirgi, su na shirin zuwa Saudi

  • Wasu miyagun ‘yan bindiga ake zargin sun kai wa maniyyatan jihar Sokoto hari a kan hanyarsu
  • Maniyyatan su na hanyar filin jirgi domin tashi zuwa kasa mai tsarki ne sai aka buda masu wuta
  • Jami’an tsaro sun yi namijin kokari wajen takaita harin, an wuce da maniyyatan zuwa fadar Hakimi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Sokoto - Wani labari mara dadi ya zo mana cewa ‘yan bindiga sun bude wuta ga wasu Bayin Allah da suke shirin zuwa sauke faralin aikin hajji a kasa mai tsarki.

Jaridar 21st Century Chronicle ta rahoto cewa wannan lamari ya auku a ranar Litinin, a lokacin da maniyyatan suke hanyarsu ta zuwa filin tashin jirgin sama.

A safiyar Talatar nan, 21 ga watan Yuni 2022 ake sa ran cewa maniyyatan jihar Sokoto za su tashi.

Kara karanta wannan

Kaduna: 'Yan bindiga sun sako shugaban kauye don ya tara N100m ya karbi mutanensa 30

Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa masu niyyar aikin hajjin su na tare da jami’an tsaro a tawagarsu a sa'ilin da wadannan ‘yan bindiga suka auko masu.

An kubutar da Maniyyata

Miyagun sun yi kwanton bauna ne a hanyar jejin Gundumi, amma jami’an tsaron ‘yan sanda ka-da-ta-kwana suka yi maza suka bankado mugun nufin na su.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An yi nasarar tsare wadannan Bayin Allah daga harin, aka wuce da su zuwa fadar Sarkin Gobir Isa. A yanzu Legit.ng Hausa ba ta da labarin halin da ake ciki.

Hajji
Masu zuwa aikin Hajji Hoto: orientalnewsng.com
Asali: UGC

Daily Trust ta ce an yi yunkurin tuntubar Sakataren din-din-din na hukumar kula da Alhazai na jihar Sokoto, Malam Shehu Dange wanda ya tabbatar da labarin.

Dange ya ce babu shakka an kai wa maniyyata hari, amma babu cikakken labarin abin da ya auku. Shi ma jami'in yana sauraron labarin yadda ake ciki ne.

Kara karanta wannan

Mutanen gari sun yi farin ciki, an tsinci gawawwakin ‘yan ta’adda jibge a cikin rafi

“Mu na so mu san halin da maniyyata suke ciki, shin an ceto dukkaninsu, ko wani a cikinsu ya samu rauni a lokacin da aka kai harin.” - Shehu Dange.

Ba mu da labari - 'Yan Sanda

Mai magana da yawun bakin ‘yan sanda na jihar Sokoto, DSP Sanusi Abubakar ya ce bai da masaniya domin abin ya faru ne a wajen jihar da suke da iko.

Legit.ng Hausa ta fahimci a dalilin matsalar tsaro a wasu jihohin, hukumar alhazai ta kawo sababbin tsare-tsare domin gujewa aukuwar irin wannan lamari.

Wannan shekara mun samu rahoto cewa wasu maniyyatan ba za su samu tashi daga jihohinsu ba.

Jawabin da Kwamishina ya fitar

Wata sanarwa da ta fito daga bakin Kwamishinan yada labarai na Sokoto, Isah Bajini Galadanchi ta tabbatar da cewa ba a taba ko maniyyaci guda daga garin Isa ba.

Galadanchi ya ce jami'an gwamnati sun karbi wadannan mutane da 'yan bindiga suka kawowa farmaki, kuma ana kokarin ganin jirginsu ya tashi zuwa kasar Saudi.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: An farmaki tawagar dan takarar shugaban kasa, Tinubu a jiharsa Legas

Abdussalami ya warke

Dazu mu ka ji tsohon shugaban Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar (rtd) ya baro asibitin Landan inda aka kwantar da shi na wasu ‘yan kwanaki.

Janar Abubakar ya ce Likitocinsa su ka ba shi shawarar ya tafi kasar waje domin a duba gwiwarsa, wannan ya sa ya ziyarci kwararrun Likitoci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel