Koma baya: APC ta gigice, jiga-jiganta a Katsina, Sokoto da Bauchi sun sauya sheka

Koma baya: APC ta gigice, jiga-jiganta a Katsina, Sokoto da Bauchi sun sauya sheka

  • Igiyar daurin tsintsiyar jam'iyyar APC ya tsinke a wasu jihohin Arewa, inda jiga-jigan 'yan siyasa suka yi mata fitar burgu
  • Bayan kammala zaben fidda gwani, ana zaton kura ta lafa, sai kuma aka fara gane masu zama a jam'iyyar da masu neman wata mafaka
  • A rahoton da muka samo, mun bayyana yadda wasu jiga-jigan APC suka fice daga cikinta saboda dalilai mabambanta

Najeriya - Wasu jiga-jigan jam’iyyar APC guda shida da suka hada da ‘yan majalisa da kuma tsohon mataimakin gwamna sun fice daga jam’iyyar tare da sauya sheka zuwa wasu jam’iyyun siyasa daban-daban a jihar Bauchi.

Ficewar dai babbar illa ce ga burin jam’iyyar na ganin bayan jam’iyyar PDP mai mulki a jihar a zaben gwamna na 2023. Gwamna mai ci Bala Mohammed na neman wa’adinsa na biyu kuma na karshe a matsayin gwamna.

Kara karanta wannan

Poly Bauchi: Babbar ma'aikaciya ta rasa aikinta bisa shiga siyasa da tallata su Tinubu

Yadda APC ta samu rashin karbuwa a jihohin Arewa
Bayan zaben fidda gwani: APC ta gigice, da dama sun sauka sheka Katsina, Sokoto, Bauchi | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Tashin hankalin ficewa daga jam’iyyar APC ya tsallaka jihar Bauchi. A wasu jahohin Arewacin kasar nan ma ‘yan jam’iyyar sun koka kan yawan ficewa da shiga wasu jam’iyyun siyasa.

Yawancin wadanda suka sauya sheka ba su gamsu da yadda aka gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar ba ne, kamar yadda Premium Times ta kawo.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bauchi APC

A jihar Bauchi sanata mai wakiltar mazabar Bauchi ta kudu Lawal Gumau ya sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa jam'iyyar NNPP bayan gaza lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar APC da ya kammala.

Hakazalika, Halliru Dauda – Jika, Sanata mai wakiltar Bauchi ta tsakiya ya sauya sheka bayan da shi ma ya gaza samun tikitin takarar gwamna na jam’iyyar APC.

Har ila yau, Yakubu Shehu, dan majalisar wakilai a mazabar Bauchi, ya fice daga jam’iyyar bayan yunkurin da ya yi na neman tikitin takarar sanata na jam’iyyar. Bai bayyana sabuwar jam'iyyar da ya koma ba.

Kara karanta wannan

Zulum ne ya fi cancanta ya zama abokin takarar Tinubu, in ji kungiyar masu ruwa da tsaki na APC

Ko da yake tsohon mataimakin gwamnan jihar, Abdu daga Katagum, bai tsaya takarar zama wakilin jam’iyyar na wani mukami ba a lokacin zaben fidda gwani, amma bayyana ficewa daga jam’iyyar saboda abin da ya bayyana a matsayin “rashin gadon kai”.

Sauran jiga-jigan da suka bar jam’iyyar a jihar sun hada da Farouq Mustapha wanda ya nemi tikitin takarar gwamna amma ya sha kaye, da kuma tsohon dan majalisar wakilai, Ibrahim Mohammed, wanda ya tsaya takarar Sanatan Bauchi ta Arewa, shi ma ya sha kaye.

APC a Katsina

A jihar Katsina ta su shugaban kasa kuwa, ‘yan majalisar wakilai uku da suka koma jam’iyyar NNPP sun nemi tikitin komawa takara amma duk suka sha kaye.

Wanda ya jagoranci tawagar wajen sauya shekar shine dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar gwamna Masari, Malumfashi/Kafur, Babangida Talau.

Sauran ‘yan majalisar biyu su ne Armayau Kado mai wakiltar Kurfi/Dutsin Ma, da Aminu Ashiru na mazabar Mani/Bindawa.

Kara karanta wannan

Zaben Ekiti: Nasarar Oyebanji ya nuna APC ta karbu sosai a wajen yan Najeriya – Buhari

Daya daga cikin hadiman Kado a majalisa, Bature Ibrahim ya tabbatar da cewa ubangidansa ya koma jam’iyyar NNPP kuma yanzu zai nemi ya tikin sake tsayawa takara a karkashin jam’iyyar ta NNPP.

An ruwaito cewa, Talau ya “lashe” tikitin NNPP na tsayawa takarar Sanatan Katsina ta Kudu.

Tsoffin ‘yan takarar gwamna guda biyu, Umar Abdullahi da Garba Dankani (wanda suka tsaya takara a 2018) su ma sun fice daga jam’iyyar ta APC.

Yayin da Abdullahi wanda ya samu kuri’u takwas a zaben fidda gwani na watan da ya gabata ya koma tsohuwar jam’iyyarsa ta PDP, DanKani kuwa ya koma jam’iyyar AA kuma a yanzu shi ne dan takararta na gwamna a jihar Katsina.

APC a jihar Sokoto

Premium Times ta ce ta samu labarin cewa wadanda suka sauya sheka a jihar Sokoto galibinsu wadanda rikicin cikin gida da shugaban jam’iyyar kuma tsohon gwamna, Aliyu Wamakko ya rutsa dasu ne.

Kara karanta wannan

2023: Ana rikici kan mataimakin Tinubu, Ɗan majalisar tarayya ya fice daga jam'iyyar APC

Dan majalisar mai wakiltar Gwadabawa/Illela/ Abdullahi Salame ya yi baran-baran da Wamakko domin ya samu makulin motar tafiyar da jam'iyyar.

Bayan da hedkwatar jam’iyyar ta kasa ta yanke tare da bayyana tsagin Wamakko a matsayin sahihin tsagi, Salame ya ci gaba da ayyana kansa a jam’iyyar.

Sai dai, bayan da ya sha kaye a zaben fidda gwani na gwamna a hannun dan takarar da Wamakko ke so, Ahmed Aliyu, ya sauya sheka zuwa PDP, jam’iyya mai mulkin jihar a yanzu.

Isa Kurdula, mamba mai wakiltar Gudu/Tangaza, shi ma ya koma jam’iyyar PDP ne bayan da ya kasa samun tikitin sake tsayawa takarar kujerarsa.

Shi ma tsohon ministan al’adu da yawon bude ido Bello Jibril ya koma jam’iyyar PDP amma bai bayyana dalilan ficewarsa ba.

Tasowar NNPP kamar na APC ne, bambancin kadan ne

Wani mai sharhi kan lamurran siyasa kuma malamin jami'a, Haruna Musa Abdullahi ya magantu da wakilin Legit.ng kan wannan batu, inda ya ce ba sabon abu bane jam'iyya ta samu koma baya lokaci guda.

Kara karanta wannan

Akwai ƙura: Ibo sun buɗa wuta, sun ce bai dace Atiku ya dauki Wike a Jam’iyyar PDP ba

A cewarsa:

"Ta yaya jam'iyyar APC din ta faro ne? Ta fara ne lokacin da wasu manya suka kalubalanci yadda PDP ke tafiyar da mulki kuma ta hade da wasu jam'iyyu aka samar da ita. Don haka, idan ka duba yadda NNPP ke samun karbuwa, musamman a Arewa maso Yamma, za ka iya tunawa da farkon APC.
"Bambancin, shi ne yiwuwar samun mulki kasa. Abin lura shi ne, lokacin da APC ta faro, gaba daya an raja'a Buhari ne zai kawo sauyi, don haka talakawa na son sa, kuma manya suka yi amfani da hakan suka cimma manufarsu ta samun kujeru albarkacin Buhari.
"Sai dai, a bangaren NNPP da ake ganin tana taso duk da cewa ba sabuwar jam'iyya bace, ai ta yi takara a 2019, to ina ganin Kwankwaso bai samu karbuwar da Buhari ya samu a kasar nan ba. Wannan shi ne ra'ayi na."

Ba ku da tsari: Dan kashenin Jonathan ya fice daga PDP, ya caccaki tsarin jam'iyyar na 2023

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Shugaban PDP ya bayyana lokacin da za a sanar da abokin tafiyar Atiku

A wani labarin na daban a tsagin PDP, tsohon ministan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Godsday Orubebe, ya yi murabus daga jam'iyyar PDP mai adawa.

Tsohon ministan ya bayyana matakin nasa ne a wata wasika da ya aikewa shugaban jam’iyyar PDP na kasa Iyorchia Ayu.

The Cable ta ruwaito cewa Orubebe ya ce murabus din nasa ya fara tun lokacin fitar da wasikar ficewarsa, inda ya kara da cewa shugaban gundumarsa na karamar hukumar Burutu ta jihar Delta yana sane da matakin da ya dauka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel