Yanzu: Hatsaniya a Hedkwatar APC Yayin Da Masu Zanga-Zanga Ke Yi Wa Adamu Barazana

Yanzu: Hatsaniya a Hedkwatar APC Yayin Da Masu Zanga-Zanga Ke Yi Wa Adamu Barazana

  • Wasu fusatattun matasa sun tada hatsaniya a hedkwatar jam'iyyar All Progressives Congress, APC, da ke birnin tarayya Abuja
  • Matasan da ake ce daga Jihar Kogi suke suna ta ihu suna furta kalaman suka ga shugaban jam'iyyar APC na kasa Sanata Abdullahi Adamu
  • Matasan suna zargin shugabannin jam'iyyar mai mulki a kasa da kwace tikitin takara da mai gidansu ya ci ta bawa wani dan takarar daban

Abuja - Hatsaniya ta barke a hedkwatar jam'iyyar APC na kasa da ke Abuja, a yayin da wasu gungun matasa suka shigo harabar jam'iyyar suna wakokin nuna kiyayya ga shugaban jam'iyyar na kasa Sanata Abdullahi Adamu.

Daily Trust ta rahoto cewa an ce matasan daga Jihar Kogi suke suka kutsa hedkwatar jam'iyyar yayin da ake taron kwamitin ayyuka na jam'iyyar, NWC.

Sakatariyar APC na kasa da ke Abuja.
Hatsaniya a Hedkwatar APC Yayin Da Masu Zanga-Zanga Ke Yi Wa Adamu Barazana. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Dalilin da yasa matasan ke zanga-zangar

Suna ikirarin cewa an kwace tikitin mai gidansu da ya ci takarar Majalisar Wakilai na tarayya an bawa wani daban.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A yayin da matasan ke yi wa Adamu barazana cewa ba zai fito daga sakatariyar ba, jami'an tsaro sun yi gagawan rufe kokan shiga hedkwatar.

Bayan afkuwar hakan, jami'an tsaron sun tura yan jarida wajen sakatariyar.

Amma, daga bisani, an bukaci yan jaridar sun nuna katin shaidan aikinsu saboda tsaro kafin aka bari suka shiga ciki.

Sanatan APC Ya Saka Wa Daliget Da Kujerun Hajji Bayan Sun Dawo Masa Da Kudinsa Don Ba Su Zabe Shi Ba

A wani rahoton, Sanata Smart Adeyemi wanda ya wakilci Kogi West a Majalisar Tarayya, ya bada kujerun Hajji ga mutum biyar cikin daligets din da ya bawa kudi amma ba su zabe shi ba a zaben fidda gwani na APC.

Adeyemi ya rasa damar komawa majalisar ne a yayin da ya samu kuri'u 43 a zaben fidda gwanin, hakan yasa ya zo na uku.

Sunday Karimi, wanda ya samu tikitin jam'iyyar ya samu kuri'u 288, yayin da Muyiwa Aina wanda ya zo na biyu ya samu kuri'u 73.

Asali: Legit.ng

Online view pixel