'Za Ku Dawo Sayen Fetur a N200 idan Kuka Zabe Ni,' Dan Takarar SDP
- Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar SDP, Adewole Adebayo, ya yi alkawarin rage farashin litar fetur zuwa N200 idan jam’iyyarsa ta kafa gwamnati
- Adebayo ya ce za a cimma hakan ne ta hanyar yaki da cin hanci da rashawa da kuma inganta yadda ake tafiyar da harkokin man fetur
- Yayin da ya je kamfen Nasarawa, ya kuma bukaci ’yan Najeriya su yi amfani da zaben 2027 wajen sauya gwamnati ta hanyar kada kuri’a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Nasarawa – Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar SDP, Adewole Adebayo, ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta sayar da litar fetur kan N200 ba tare da tallafin mai ba idan ya lashe zaben 2027.
Adebayo ya bayyana hakan ne a wajen taron tattaunawa da shugabanni, ’yan takara da magoya bayan jam’iyyar a Lafia, jihar Nasarawa, ranar Juma’a.

Kara karanta wannan
"Dan takarar haɗakar adawa zai iya kayar da Tinubu a zaben shugaban ƙasa na 2027"

Source: Twitter
Punch ta wallafa cewa ya kuma bukaci ’yan Najeriya su daina takaita kansu ga sukar gwamnati, su shiga harkar zabe domin sauya shugabanci idan ba su gamsu da yadda ake tafiyar da kasa ba.
Adebayo ya bukaci a kada kuri'a
Dan takarar ya ce kada kuri’a ce hanya mafi inganci da jama’a za su bi wajen sauya gwamnati, ba zagi ko ihu ba.
Ya ce:
"Gwamnati mara kyau ba za ta sauka saboda kuna zaginta ko yi mata ihu ba. Abin da ke sa gwamnati ta sauka shi ne kada kuri’a. Gwamnati ba ta damu da zagin da kuke yi mata ba, amma tana damuwa da kuri’ar da za ku kada. Don haka dole ne ku kada kuri’a."
Adebayo ya ce babban abin da ke gaban ’yan Najeriya a zaben 2027 shi ne ko kasar ta jama’a ce ko kuma ta wasu tsirarun mutane da ke da karfin siyasa da tattalin arziki.

Kara karanta wannan
Zance ya ƙare, El Rufai ya tsage gaskiya a gaban kotu kan zargin kutse a wayar Nuhu Ribadu
Fetur zai dawo N200
A bayanin da ya yi a kan tattalin arziki, Adebayo ya ce gwamnatin SDP za ta rage farashin litar fetur zuwa N200 ba tare da tallafin gwamnati ba.
Ya bayyana cewa za a cimma hakan ne ta hanyar dakile cin hanci da rashawa da kuma inganta ayyukan bangaren man fetur.
A cewarsa, matakin zai ba kamfanin NNPCL damar ci gaba da samun riba ba tare da bukatar gwamnati ta rika kashe kudade wajen tallafa wa cin hanci ba.
Batun noma, ilimi da almajirai
Dan takarar ya ce jihar Nasarawa da jihohin da ke makwabtaka da ita na da karfin noma da zai iya taimaka wa Najeriya da sauran kasashen Afirka wajen samar da abinci.
Ya ambaci Nasarawa, Plateau, Kogi, Kaduna da Abuja a matsayin yankunan da ke da damar samar da abincin da zai wadatar da nahiyar Afirka.

Source: Facebook
A bangaren ilimi, Adebayo ya yi alkawarin samar da ilimi kyauta, tilas kuma mai inganci, musamman ga yaran da ba sa samun damar zuwa makaranta.
A kan almajirai kuwa ya ce:
"Ba za ku ga almajirai a kan titi suna yawo ba, za su koma zama a makarantun Islamiyya, za su koma zama a makarantu,'
ACF ta caccaki Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa kungiyar ACF ta ce tabarbarewar rayuwa, karuwar talauci da matsalar tsaro na daga cikin abubuwan da ke jawo fushin jama’a kan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Mai magana da yawun kungiyar, Tukur Mohammed-Baba, ya ce rashin jin dadin jama’a ba ya shafar Arewa kadai, domin matsalolin sun bazu a sassan Najeriya.
A wata sanarwa da ya fitar, Mohammed-Baba ya yi gargadin cewa bai kamata a danganta fushin jama’a da bambancin addini ko yankin da suka fito ba.
Asali: Legit.ng
