Gwamna zai Fara Bayar da Tallafin N70,000 don Rage Radadin Tsadar Sufuri

Gwamna zai Fara Bayar da Tallafin N70,000 don Rage Radadin Tsadar Sufuri

  • Gwamnatin jihar Kebbi ta ce ta shirya fara biyan ma'aikata N70,000 a matsayin alawus ɗin sufuri domin rage musu raɗaɗin tsadar rayuwa
  • Gwamna Nasir Idris ya bayyana cewa ya kafa kwamiti ƙarƙashin jagorancin shugaban ma'aikatan gwamnati domin duba yadda za a aiwatar da shirin
  • Gwamnatin Kebbi ta amince da mafi ƙarancin albashi na Naira 75,000 ga ma'aikatan jihar, tare da ƙarin Naira 17,650 ga malamai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kebbi – Gwamnatin jihar Kebbi ta ce tana shirin fara biyan ma'aikatan jihar alawus ɗin sufuri na Naira 70,000 da gwamnatin tarayya ta amince da shi domin rage tasirin tsadar sufuri sakamakon cire tallafin man fetur.

Da aka tambaye Nasir Idris ko gwamnatinsa za ta biya ma'aikata wannan alawus da aka amince da shi ga ma'aikatan tarayya, gwamnan ya ce tuni ya kafa kwamiti domin fara aikin aiwatar da shirin.

Kara karanta wannan

Abubuwan da ya kamata ku sani game da tallafin N50,000 da aka fara turawa mutane a Najeriya

Gwamna Nasir Idris
Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris. Hoto: Nasir Idris
Source: Facebook

GVanguard ta wallafa cewa gwamna Nasir Idris ne ya bayyana hakan ranar Talata yayin wata tattaunawa da manema labarai a birnin tarayya Abuja.

Gwamnan Kebbi ya kafa kwamiti

Gwamna Idris ya ce ya kafa kwamiti ƙarƙashin shugaban ma'aikatan gwamnati domin duba yadda za a fara biyan alawus ɗin.

Ya bayyana damuwarsa kan yadda matsin tattalin arziki ya rage ƙarfin sayen kayan masarufi na ma'aikata, duk da mafi ƙarancin albashin da ake biya a yanzu.

Gwamnan ya ce yana ganin ya zama wajibi a ɗauki matakai domin inganta walwalar ma'aikatan jihar, yana mai cewa kasancewarsa tsohon shugaban ƙungiyar ƙwadago ya sa ya fahimci buƙatun ma'aikata.

A cewarsa:

“Na san abin da gwamnatin tarayya ta yanke shawarar yi wa ma'aikata. Ku sani cewa kasancewata tsohon shugaban ƙwadago, dole ne a yi wani abu ga ma'aikatan jihar Kebbi.
“Na riga na kafa kwamiti ƙarƙashin shugaban ma'aikatan gwamnati, kuma suna aiki. Na sha bayyana cewa idan gwamnatin tarayya ta ƙara albashin ma'aikata, Kebbi za ta kasance cikin jihohin farko da za su aiwatar da hakan.”

Kara karanta wannan

Shugaban EFCC ya ga abin mamaki a kan gwamnan Zamfara

Mafi karancin albashi a Kebbi

Gwamnan ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu bisa amincewa da N70,000 a matsayin tallafin sufuri ga ma'aikatan tarayya.

Ya ce shugaban ƙasar ya fahimci yadda matsin tattalin arziki ya shafi ƙarfin sayen kayayyaki na ma'aikata, shi ya sa aka amince da tallafin kafin a kammala tattaunawa kan sabon mafi ƙarancin albashi.

Idan za a tuna, gwamnatin jihar Kebbi ta amince da mafi ƙarancin albashi na Naira 75,000 ga ma'aikatan gwamnati, tare da ƙarin Naira 17,650 ga malamai.

Taswirar jihar Kebbi
Taswirar jihar Kebbi a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Gwamna Idris ya ce gwamnatinsa ta fara ayyukan gina gidaje domin ma'aikata, ciki har da aikin gidaje 155 da wani aikin gidaje 250.

Tinubu ya raba tallafi

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta kammala rabon Naira biliyan 75 ga masu masana'antu 104 domin ƙarfafa samar da kayayyaki a cikin gida.

Haka kuma, gwamnati ta raba Naira biliyan 65.8 ga ƙananan 'yan kasuwa 15,018 domin faɗaɗa harkokinsu da samar da ayyukan yi.

Ministar Masana'antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Jumoke Oduwole, ce ta bayyana hakan, inda ta ce tallafin na cikin shirye-shiryen gwamnati na bunƙasa kasuwanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng