Gwamna Ya Sha Alwashin Bai Wa Tinubu Kuri'un Jiharsa Gaba Daya a Zaben 2027

Gwamna Ya Sha Alwashin Bai Wa Tinubu Kuri'un Jiharsa Gaba Daya a Zaben 2027

  • Gwamna Nasir Idris ya tabbatar wa Shugaba Bola Tinubu cewa jihar Kebbi za ta ci gaba da kasancewa tare da APC a zaɓen 2027
  • Dr. Nasir Idris ya ce jihar ba ta taɓa ba Tinubu kunya ba, kuma za ta ƙara masa ƙuri’u fiye da waɗanda ta ba shi a zaɓen 2023
  • Gwamnan ya roƙi Tinubu ya taimaka wajen fara gudanar da ayyukan tashar jigilar kaya ta cikin ƙasa ta Samia da ke Bagoro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kebbi, Nigeria - Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya tabbatar wa Shugaba Bola Tinubu cewa jihar za ta ci gaba da zama daya daga cikin ginshikan da APC ke alfahari da su.

Gwamna Nasir Idris ya kuma ba Tinubu tabbacin cewa Kebbi za ta ba shi gagarumin goyon baya domin ya samu nasarar zarcewa zuwa wa'adi na biyu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Kara karanta wannan

Tinubu ya amince da bukatar da ka gabatar masa a wurin gangamin kamfe a jihar Kebbi

Gwamna Nasir Idris
Gwamnan jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris s fadar gwamnatinsa da ke Birnin Kebbi Hoto: Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu
Source: Facebook

Gwamnan Kebbi ya ba Tinubu tabbaci

Vanguard ta ce gwamnan ya bayar da tabbacin ne ranar Talata yayin da ya karbi bakuncin Tinubu a gangamin yaƙin neman zaɓen APC, inda ya ce Kebbi ta kasance tana goyon bayan shugaban ƙasar kuma za ta ƙara ƙaimi a zaɓe mai zuwa.

“Mai girma Shugaban Ƙasa, jihar Kebbi ba ta taɓa ba ka kunya ba, kuma ba za ta taɓa ba ka kunya ba. A shekarar 2023, mun ba ka cikakken goyon baya. A wannan zaɓen kuma za mu ba ka fiye da haka,” in ji gwamnan.

Ya ƙara da cewa, “Ina tabbatar maka cewa da yardar Allah, jihar Kebbi za ta ba APC duka kuri'unta 100% a zaɓe mai zuwa.”

Nasir Idris ya yi misali da taron kamfe

Gwamnan ya bayyana yawan mutanen da suka halarci gangamin a matsayin wata shaida ta goyon bayan da jihar ke bai wa Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima.

Kara karanta wannan

2027: Sanatan Kano ya faɗawa Tinubu gaskiya kan ƙalubalen da APC za ta fuskanta a Arewa

“Wannan ɗimbin jama’ar da kuke gani a nan shaida ce karara cewa jihar Kebbi ta APC ce, kuma tana tare da Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima,” in ji shi.

Gwamna Idris ya kuma yaba wa shugaban ƙasar kan abubuwan da ya ce gwamnatinsa ta yi wa jihar, musamman a fannonin noma, samar da ababen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya da tsaro.

Gwamna Idris ya hode wa Tinubu

Ya gode wa Tinubu kan shirin Renewed Hope Agenda da kuma tallafin da yake bai wa manoma, wanda ya ce ya taimaka wajen bunƙasa noman shinkafa a Kebbi.

“Muna godiya gare ka kan hanyoyi, makarantu, asibitoci da kuma tallafin tsaro da kake ba mu,” in ji shi.

Gwamnan ya ce gwamnatinsa ma ta zuba jari wajen ƙarfafa tsarin tsaro a jihar, inganta cibiyoyin kiwon lafiya, samar da kayan tallafin noma kyauta ga manoma, da kuma gina hanyoyi a ƙauyuka da cikin garuruwa a faɗin jihar.

Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a wurin kamfen APC a jihar Kebbi Hoto: Barau. I. Jibrin
Source: Facebook

Sai dai Idris ya yi amfani da damar wajen roƙon Tinubu ya taimaka wajen tabbatar da fara cikakken aikin gina tashar jigilar kaya ta tsandauri a Samia, da ke ƙaramar hukumar Bagoro ta jihar.

Kara karanta wannan

‘Dan takara bai rike sirri ba, ya fadi tanadin da ‘yan adawa suke yi wa shugaba Tinubu

Tinubu ya amince da bukatar Kebbi

Kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya amince da kafa tashar jiragen kaya ta tsandauri a jihar Kebbi domin bunƙasa harkokin kasuwanci da tattalin arziƙi.

Tashar jiragen kaya ta tsandauri wata cibiya ce da ke nesa da gabar teku, wadda ake haɗa ta da tashar jiragen ruwa ta teku ta hanyar hanya ko layin dogo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262