An Yi wa Tinubu Ihun 'ba ma yi' da Ya Je Masallacin Juma'a a Abuja

An Yi wa Tinubu Ihun 'ba ma yi' da Ya Je Masallacin Juma'a a Abuja

  • Wasu masu ibada sun yi wa Shugaba Bola Tinubu ihu tare da kiraye-kirayen adawa da shi bayan ya idar da sallar Juma’a a Abuja
  • Wasu daga cikinsu sun rika cewa “Tinubu Must Go”, yayin da wasu ke cewa “Ba mu yi, ba ma so” saboda rashin jin dadin matakan tsaro da aka dauka
  • Shaidun gani da ido sun ce an hana wasu masu ibada shiga masallacin, yayin da aka kuma hana wasu fita har sai tawagar shugaban kasar ta bar wajen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya fuskanci hayaniya da kiraye-kirayen adawa daga wasu masu ibada bayan ya idar da sallar Juma’a a babban masallacin Shehu Shagari da ke Abuja.

Bidiyo ya nuna wasu mutane suna ihu da kalaman adawa da shugaban kasar yayin da tawagarsa ke barin harabar masallacin.

Kara karanta wannan

Abin da ake zargi ya tabbata, jagoran ƴan bindiga ya faɗi dalilansu na ɗaukar makami

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Leadership ta wallafa cewa wani ganau da ya halarci sallar ya danganta lamarin da matakan tsaro da aka dauka, wadanda suka takaita zirga-zirgar masu ibada a lokacin ziyarar shugaban kasar.

An hana wasu shiga masallacin

Ganau din ya ce Tinubu ya isa masallacin da misalin karfe 1:49 na rana, kuma a lokacin tuni jami’an tsaro suka takaita shiga harabar wajen.

Ya bayyana cewa jami’an tsaro sun hana wasu mutane shiga masallacin bayan isowar shugaban kasar, yayin da aka tare hanyoyin da ke kaiwa wajen.

Wasu jami’an tsaro sun kuma hau katangar da ke kewaye da masallacin domin tabbatar da tsaro.

A cewarsa, takunkumin bai tsaya a lokacin sallar ba, domin an hana wasu masu ibada fita daga harabar har sai tawagar shugaban kasar ta tashi.

Mutane sun yi wa Tinubu ihu

Premium Times ta rahoto cewa wani ganau ya ce wasu daga cikin mutanen da matakan tsaron suka shafa sun nuna fushinsu ta hanyar furta kalaman “Ba mu yi, ba ma so”.

Kara karanta wannan

An yi harbe harbe a kusa da White House da Donald Trump yake zama

Wasu kuma sun yi ta cewa “Tinubu Must Go”, kalaman da ake amfani da su wajen nuna adawa da sake tsayawar shugaban kasar takarar shugaban kasa.

Wata majiya a masallacin ta ce hayaniyar ta samo asali ne daga yadda aka yi wa masu ibada katanga, inda aka bar wasu a waje ba tare da sun samu damar shiga ba.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaba Bola Tinubu a wajen kamfen a Jigawa. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Har zuwa lokacin hada rahoton, kokarin jin ta bakin fadar shugaban kasa bai yi nasara ba, domin mai magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga, bai amsa kiran waya ba.

Shugaban kasar ya halarci sallar ne tare da mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu; mai ba shi shawara kan harkokin siyasa, Ibrahim Masari; shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila da Abdullahi Ganduje.

Ga bidiyon da aka masa ihu a kasa:

ADC ta caccaki APC

A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta zargi jam'iyyar APC mai mulki da kokarin raunana jam'iyyun adawa ta hanyar shigar da kararraki a kotu gabanin zaben 2027.

Sakataren yada labaran ADC na kasa, Bolaji Abdullahi, ya ce jam'iyyarsa ta shafe tsawon lokaci tana fuskantar shari'o'i maimakon gina rassanta da shirya yakin neman zabe.

Ya yi zargin cewa manufar APC ita ce ta raunana jam'iyyun adawa, domin Shugaba Tinubu ya shiga zaben 2027 ba tare da fuskantar abokan hamayya masu karfi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng