Babu Ladabi: 'Yan TikTok Sun Yi Rashin Kunya ga Sheikh Daurawa a Kano
- Hukumar Hisbah ta Kano ta kama matasa uku masu amfani da TikTok bisa zargin wallafa kalaman cin zarafi ga hukumar da shugabanta
- Waɗanda aka kama sun haɗa da Ahmad Usman mai shekaru 25, Muhammad Aliyu mai shekaru 20 da Zainab Abubakar mai shekaru 19
- Hisbah ta ce tana gudanar da bincike, kuma za ta gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala binciken
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama wasu matasa uku masu amfani da manhajar TikTok bisa zargin amfani da shafukansu na sada zumunta wajen cin zarafin hukumar da Kwamanda Janar ɗinta, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa.
Waɗanda ake zargin sun haɗa da Ahmad Usman, mai shekaru 25, wanda aka fi sani da Ortega, da Muhammad Aliyu, mai shekaru 20.

Kara karanta wannan
Dambarwar neman sakin matar Gwamna Abba ya jefa wasu mutane a matsala, an samu bayanai

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto a ranar Litinin, 16 ga watan Nuwamban 2026 cewa dukkan wadanda ake zargin mazauna yankin Kurna ne da ke cikin birnin Kano.
Mutum na uku ita ce Zainab Abubakar, mai shekaru 19, ’yar asalin Jihar Ogun da ke zaune a unguwar Dorayi ta Kano.
Hisbah ta tabbatar da kama matasan
Mataimakin Kwamanda Janar na hukumar, Dr Mujahid Aminudeen, ne ya tabbatar da kamen matasan, inda ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.
Ya bayyana cewa hukumar za ta gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala binciken da take gudanarwa.
Bidiyon da ya bazu a kafafen sada zumunta
Rahotanni sun nuna cewa an ga matasan a wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta, inda ake zarginsu da furta kalaman cin zarafi ga jami’an Hisbah.
An ce lamarin ya faru ne bayan hukumar ta hana su gudanar da wani taro a kusa da titin Zoo Road da ke birnin Kano.
Bayan faruwar hakan ne aka ga bidiyon nasu yana yawo a kafafen sada zumunta, wanda ya jawo hankalin hukumar.
Sai dai har yanzu ba a bayyana cikakken bayani kan sakamakon binciken da kuma takamaiman tuhumar da za a gabatar a gaban kotu ba.

Source: Original
Karanta wasu labaran kan Sheikh Aminu Daurawa
- Zance ya ƙare: Sheikh Daurawa ya yi magana kan ɗan takarar da zai yi wa kamfe a 2027
- An sanya Sheikh Daurawa da wasu manyan malaman Musulunci 3 a kwamitin kamfen APC
- Sheikh Daurawa ya rubuta zungureriyar wasikar da za ta sa matasa su shiga taitayinsu
Hisbah ta cafke matashi kan aure a Kano
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar Hisbah ta jihar Kano ta cafke wani matashi bisa zargin kulla aure ta hanyar da bai dace ba lamarin da ya jawo maganganu a jihar.
Jami'an na hukumar Hisbah sun cafke matashin ne mai suna mai suna Sunusi Sabi’u Zakariyya da ya auri budurwar da ake kira Zainab bayan ta tsere daga Kebbi zuwa jihar Kano.
Rahotanni sun nuna cewa Zainab ta shaida wa masu bincike cewa ta baro Birnin Kebbi ne bayan samun labarin cewa mahaifinta na shirin tilasta mata yin auren da ba ta so. Re
Asali: Legit.ng
