"Yadda Tsohon Shugaban Kasa Ya Roki Tinubu Ya Goyi bayan Diyarsa Ta Zama Gwamma"
- Ayodele Fayose ya bayyana abin da ya sa tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya fara sukar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu
- Fayose ya ce Obasanjo ya fara sukar gwamnatin Tinubu ne bayan an ƙi amincewa da buƙatarsa ta ganin ɗiyarsa, Iyabo, ta zama gwamnar Ogun
- Iyabo Obasanjo ta dakatar da burinta na neman kujerar gwamnar Ogun bayan APC ta amince da Solomon Adeola a matsayin ɗan takararta na masalaha
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ogun, Nigeria - Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya ce tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya fara sukar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ne bayan an ƙi amincewa da buƙatarsa.
Ya yinikirarin cewa rashin amincewar Tinubu da bukatar Obasanjo ta ganin ɗiyarsa, Iyabonta zama gwamnar jihar Ogun ne asalin dalilin da ya sa ya fara sukar gwamnati mai ci.

Source: Facebook
Fayose ya bayyana hakan ne ranar Litinin, 16 ga watan Nuwamba, 2026 yayin wata hira da tashar talabijin ta TVC.
QA yayin tattaunawar, an nemi tsohon gwamnan ya mayar da martani kan sukar da ake yi wa gwamnatin Tinubu, musamman kalaman Obasanjo na cewa gyare-gyaren da shugaban ƙasar ke yi sun jefa ’yan Najeriya cikin talauci da 300%
Da yake martani, Fayose ya ce ana ɗaukaka Obasanjo fiye da kima, yana mai cewa tsohon shugaban ƙasar ya saba neman laifin wasu.
Fayose ya kuma lura cewa Obasanjo ya taɓa sukar gwamnatocin marigayi Umaru Musa Yar’Adua da Goodluck Jonathan.
“Mun fiye kambama Obasanjo fiye da yadda ya kamata, wannan ita ce gaskiya, haka halinss yake, a rayuwa, babu wanda yake ganin ya fi Obasanjo iya yin komai. Idan wani zai yi magana, ko dai Obasanjo ne ko kuma babu kowa.
“Obasanjo har yanzu yana son a riƙa kula da shi, kuma ba ya ganin wani abu mai kyau a wurin kowa. Wannan ita ce gaskiya. Idan ka duba Obasanjo, ya soki Yar’Adua da Jonathan.
“A zahiri, ya mayar da kansa maƙiyin Jonathan, saboda Jonathan ba ya neman izininsa a kullum, Obasanjo ya shiga damuwa.”
Fayose ya ƙara da cewa a watan Afrilun 2026, Obasanjo na cikin waɗanda suka tarbi Tinubu a Ogun lokacin ƙaddamar da filin jirgin saman jigilar kaya na ƙasa da ƙasa na Gateway.
Ya ce Obasanjo ya sanya kaya masu kama da na Tinubu a lokacin ziyarar shugaban ƙasar jihar Ogun, sannan ya yi masa yabo sosai.
Fayose ya yi zargin cewa Obasanjo ya tuntuɓi tsohon gwamnan Ogun, Olusegun Osoba, domin ya taimaka masa wajen shawo kan Tinubu ya goyi bayan takarar ɗiyarsa, Iyabo Obasanjo, a matsayin gwamnar jihar.
Ya ce Obasanjo ya tarbi Tinubu a Ogun ne saboda burin ɗiyarsa na zama gwamna.
“Sakamakon wannan buƙata ba ta yiwu ba, sai Obasanjo ya tuna da abin da Osoba ya rubuta game da shi a cikin littafinsa, sannan ya je ya mayar masa da martani saboda abin da yake so bai samu ba.
Ba a ga maciji tsakanin Fayose da Obasanjo, inda mutanen biyu suka shafe kusan shekaru goma suna musayar zarge-zarge da kalaman cin zarafi a kafafen yaɗa labarai.

Kara karanta wannan
2027: Gwamna ya ce nasarorin da ya samu za su taimaka masa wajen zama shugaban ƙasa
Obasanjo ya soki yawan ciyo bashi
Kun ji cewa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya soki Bola Tinubu kan sake karbo basuka wanda ke cutar da kasar.
Obasanjo ya kuma nuna damuwa kan yadda ake tafiyar da tattalin arzikin Najeriya, inda ya tuna cewa lokacin da ya fara gonarsa shekaru 47 da suka wuce, Naira ta fi karfin dala.
Asali: Legit.ng

