An Kare Tinubu, an Karyata Alkawarin da Ake Yadawa Ya Yi kafin Ya Hau Mulki

An Kare Tinubu, an Karyata Alkawarin da Ake Yadawa Ya Yi kafin Ya Hau Mulki

  • Tsohon ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, ya yi magama kan alkawarin Bola Tinubu bai yi alkawari kan wutar lantarki
  • Fashola ya ce 'yan Najeriya su tantance nasarar gwamnatin Tinubu kan wutar lantarki bisa irin ci gaban da suka gani a yankunansu
  • Tsohon gwamnan Legas ya bayyana cewa wutar lantarki ta inganta a yankinsa cikin 'yan watannin nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja – Tsohon ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bai yi alkawarin samar da wutar lantarki na awa 24 a Najeriya ba.

Fashola ya ce ya kamata 'yan Najeriya su tantance ayyukan gwamnatin Tinubu a bangaren wutar lantarki bisa irin ci gaban da suka gani a yankunansu.

An dawo da maganar Tinubu na alkawari kan wutar lantarki
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Tsohon gwamnan jihar Legas ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels a daren Talata, inda aka tambaye shi game da alkawarin da Tinubu ya yi a lokacin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Kara karanta wannan

"Tinubu ya fi Buhari kokari"; Tsohon gwamna ya kawo dalili

A lokacin kamfen ɗin, Tinubu ya yi alkawarin cewa 'yan Najeriya za su samu wutar lantarki, sannan ba za su ci gaba da biyan kuɗin lantarki bisa ƙiyasin da kamfanoni ke yi ba.

Fashola ya magantu kan alkawarin Tinubu

A yayin hirar, mai gabatar da shirin ya kunna wani bidiyo da ke nuna Tinubu yana jawabi ga masu zaɓe, inda ya ce idan ya kasa cika alkawarin samar da wutar lantarki da kawo ƙarshen biyan kuɗin ƙiyasin wuta, kada su sake zaɓensa a karo na biyu.

A cikin bidiyon, Tinubu ya ce:

"Dole ne ku samu wutar lantarki. Haka kuma ba za ku sake biyan kuɗin lantarki bisa ƙiyasin da ake yi ba. Alkawari da aka yi, za a cika shi. Idan na kasa cika alkawarin, sannan muka dawo neman wa'adi na biyu, kada ku zaɓe ni."

Da yake mayar da martani, Fashola ya ce ya kamata mai gabatar da shirin ya bari bidiyon ya ƙare domin Tinubu ya ƙara da cewa zai bayar da dalilai masu gamsarwa idan ya kasa cika alkawarin.

Kara karanta wannan

"Alamu da lissafin siyasa sun nuna wanda zai lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2027"

Ya ce:

"Da farko, ina ganin ya kamata ka bari faifan bidiyon ya ƙare gaba ɗaya. Domin daga baya ya ce, 'sai dai idan na ba ku isassun dalilai.' Amma ka dakatar da bidiyon."

Fashola ya bayyana cewa alkawarin Tinubu ya ƙunshi abubuwa biyu, wato samar da wutar lantarki da kuma kawo ƙarshen biyan kuɗin lantarki bisa ƙiyasin da kamfanonin rarraba wuta ke yi.

Fashola ya kare Tinubu kan wutar lantarki
Tsohon gwamnan Lagos, Babatunde Fashola. Hoto: Babatunde Fashola.
Source: Facebook

'Yan Najeriya su tantance ayyukan Tinubu

Tsohon ministan ya ƙara da cewa mutanen da har yanzu ba su ga wani ci gaba ba suna da damar tambayar shugaban ƙasa dalilin da ya sa bai kai ga cika alkawarinsa gaba ɗaya ba.

Lokacin da mai gabatar da shirin ya ce Tinubu ya yi alkawarin samar da wutar lantarki na awa 24, Fashola ya yi watsi da wannan fassarar.

Ya ce:

"Ya ce akwai isasshiyar wutar lantarki. Za mu iya sake kunna bidiyon. Ban ji ya ambaci awa 24 ba."

Kara karanta wannan

Tinubu ya leƙo babbar matsalar ƴan Plateau, ya ɗauka masu alƙawari

Bayan an sake kunna bidiyon, Fashola ya ci gaba da cewa ya kamata a duba irin ci gaban da aka samu wajen samar da wutar lantarki da rarraba na'urorin auna amfani da wuta.

Bashi na barazana ga wutar lantarki

An ji cewa masu ruwa da tsaki a bangaren wutar lantarki sun yi gargadi kan bashin sama da Naira biliyan 639 da ake bin masu samar da iskar gas.

Wani jami'in NNPC ya ce kamfanonin samar da wutar lantarki ba sa samun isassun kuɗaɗen biyan kuɗin iskar gas.

Masana sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta samar da ingantaccen tsarin biyan kuɗi tare da ƙara zuba jari wajen samar da iskar gas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.