Ana Zargin Tsohon Gwamnan APC da Kawo Cikas a Ziyarar Shettima Fadar Sarki
- Tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Umaru Al-Makura, ya bukaci Sakataren Gwamnatin jihar, Labaran Magaji, ya janye zargin hada shi da tarwatsa ziyarar Shettima
- Al-Makura ya bukaci SSG ya ba shi hakuri a bainar jama'a cikin kwanaki bakwai, ko kuma ya shigar da shi kara a kotu
- Tsohon gwamnan ya musanta hannu a lamarin, yana mai cewa gwamnatin jihar ba ta gabatar da wata hujja da ke alakanta shi da rikicin ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Lafia, Nasarawa - Tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Umaru Tanko Al-Makura, ya yi barazanar daukar matakin shari'a kan Sakataren Gwamnatin jihar (SSG), Labaran Magaji.
Al-Makura ya yi zargin an bata masa suna da alakanta shi da yunkurin tarwatsa ziyarar mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima.

Source: Twitter
Al-Makura ya bukaci Magaji da ya janye kalaman da ya yi kan zargin tare da ba shi hakuri a bainar jama'a cikin kwanaki bakwai. Ya kuma yi gargadin cewa zai garzaya kotu idan SSG din ya ki cika bukatunsa, cewar Premium Times.
Abin da ya jawo rikicin a Nasarawa
Wannan takaddama na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin siyasa ke kara kamari tsakanin magoya bayan Gwamna Abdullahi Sule da na tsohon Sufeto-Janar na 'yan sanda, Mohammed Adamu, gabanin zaben gwamnan Nasarawa na shekarar 2027.
Rikicin ya samo asali ne daga takun-sakar neman wanda zai gaji kujerar Gwamna Sule. Gwamnan na goyon bayan Ahmed Wadada, yayin da Al-Makura ke marawa Mohammed Adamu baya.
Sai dai Wadada ya samu tikitin takarar gwamna na jam'iyyar APC, inda ya doke Adamu. Hakan ya sa tsohon shugaban 'yan sandan ya fice daga APC tare da karbar tikitin takarar jam'iyyar SDP.
Yadda aka samu sabani kan ziyarar Shettima
Takaddamar ta kara kamari ne bayan rahotannin cewa wasu mutane sun kawo cikas ga shirye-shiryen ziyarar da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya kai wa Sarkin Lafia a ranar 4 ga watan Nuwamba.
Bayan faruwar lamarin, gwamnatin Nasarawa ta zargi wasu matasa da ake zargin suna da alaka da Al-Makura da Mohammed Adamu da daukar nauyin rikicin.
A cikin sanarwar da ofishin SSG ya fitar, gwamnatin ta bayyana lamarin a matsayin yunkurin kunyata gwamnatin jihar, tare da umartar jami'an tsaro da su gudanar da bincike domin gano wadanda ke da hannu.
Sai dai makusantan tsohon gwamnan da Mohammed Adamu sun yi watsi da zargin, suna masu cewa siyasa ce ta sa aka yi wannan ikirari.
A cikin wata wasika mai kwanan wata 12 ga watan Nuwamba, wadda lauyansa, Malla Makpa, ya aikewa SSG, Al-Makura ya bukaci a janye zargin da aka yi masa.
Lauyan ya bayyana cewa sakin layi na uku na sanarwar gwamnatin ya ambaci sunan tsohon gwamnan a matsayin daya daga cikin mutanen da ake zargin sun dauki nauyin tarwatsa ziyarar.

Source: Facebook
Bukatun Al-Makura ga gwamnatin Nasarawa
Daga cikin bukatun da tsohon gwamnan ya gabatar akwai janye bangaren sanarwar da ya ambaci sunansa a matsayin wanda ake zargin ya dauki nauyin tarwatsa ziyarar Shettima.
Ya kuma bukaci SSG ya wallafa cikakken uzuri a bainar jama'a, tare da bayyana cewa an yi zargin ne ba tare da gabatar da hujjojin da za su tabbatar da shi ba.
Al-Makura ya bukaci a wallafa uzurin da janyewar zargin a akalla manyan jaridun kasa guda biyu, sannan a sanya su a shafukan intanet da kafafen sada zumunta da gwamnatin ta yi amfani da su wajen yada sanarwar farko.
Haka kuma, ya bukaci gwamnatin ta daina yada irin wadannan zarge-zarge a kansa muddin ba ta da kwararan hujjoji da za ta iya tabbatarwa ta hanyoyin da doka ta tanada.
Wasikar ta ba SSG wa'adin kwanaki bakwai daga lokacin da ya karba domin ya biya bukatun, inda lauyan ya yi gargadin cewa rashin yin hakan zai tilasta wa tsohon gwamnan garzaya kotu.
Matakan da Al-Makura ke shirin dauka sun hada da shigar da karar bata suna, neman diyyar kudi mai yawa da kuma umarnin kotu na dakatar da ci gaba da yada zargin.
Shettima ya umarci raba buhunan taki
An ji cewa Kashim Shettima ya umarci hukumomin gwamnati da masu ruwa da tsaki su gaggauta samar da buhunan taki sama da miliyan 3.
Gwamnatin tarayya na shirin sayen takin da kamfanonin cikin gida suka samar domin sayar wa manoma kan farashi mai sauƙi.
Shettima ya kuma umarci jami’an tsaro da su tabbatar da adalci wajen rabon takin, musamman a yankunan da ke fama da matsalar tsaro.
Asali: Legit.ng


