Mutanen Kano na cikin Alheri, Gwamna Abba Ya Shirya Rabon Tallafin N50,000

Mutanen Kano na cikin Alheri, Gwamna Abba Ya Shirya Rabon Tallafin N50,000

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ƙaddamar da shirin tallafin N50,000 duk wata ga mata 5,200 a faɗin Jihar Kano
  • Gwamnan ya buƙaci waɗanda za su amfana su yi amfani da kuɗin wajen kafa sana’o’i da faɗaɗa kasuwancinsu
  • Kwamishiniyar Harkokin Mata ta buƙaci mata su goyi bayan APC a dukkan matakan zaɓen 2027 domin ci gaba da shirye-shiryen tallafi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da shirin tallafin kuɗi na N50,000 duk wata ga mata 5,200 a faɗin jihar domin ƙarfafa tattalin arzikinsu da taimaka musu su dogara da kansu.

Gwamna Abba ya ƙaddamar da shirin ne a ranar Litinin, 9 ga watan Nuwamban 2026 a gidan gwamnatin jihar Kano.

Gwamna Abba ya raba tallafi a Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jawabi a wajen rabon tallafin N50,000 Hoto: Isah Muhammad Salisu
Source: Facebook

Wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan, Mustapha Muhammad, ya fitar a ranar Talata, 10 ga watan Nuwamban 2026 ce ta bayyana hakan, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Mustapha Kwankwaso zai dauki matakin sharia kan kwamishinan Abba, ya ba shi zabi

Manufar tallafin ga mata a Kano

Sanarwar ta bayyana cewa an tsara shirin ne domin inganta rayuwar mata ta fuskar tattalin arziki, ta hanyar samar musu da kuɗaɗen da za su iya amfani da su wajen kafa sana’o’i masu ɗorewa.

Haka kuma, shirin na da manufar taimaka wa mata su faɗaɗa kasuwancinsu, samun damar dogaro da kansu da kuma inganta walwalar iyalansu.

Da yake jawabi yayin ƙaddamar da shirin, Gwamna Abba ya buƙaci waɗanda za su amfana da tallafin su yi amfani da kuɗin yadda ya kamata.

Ya shawarce su da su zuba kuɗaɗen cikin sana’o’i masu amfani da sauran harkokin kasuwanci da za su riƙa samar musu da kuɗin shiga.

A cewarsa, yin hakan zai taimaka wajen inganta rayuwarsu da samar wa iyalansu kyakkyawar makoma.

Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta samar da ingantaccen tsari domin tabbatar da cewa tallafin ya isa ga matan da aka tsara shirin domin taimaka musu.

Kara karanta wannan

Tallafin N50,000: SERAP ta jero tambayoyin da ke bukatar amsa daga gwamnatin Tinubu

Ya kuma jaddada cewa za a gudanar da shirin bisa gaskiya, adalci da kuma riƙon amana, domin tabbatar da cewa an cimma manufar da aka sanya a gaba.

Sarkin Gaya ya yaba da shirin

A nasa jawabin, Sarkin Gaya, Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir, ya bayyana shirin a matsayin wani muhimmin mataki da zai taimaka wajen inganta tattalin arzikin mata da iyalansu a jihar.

Ya yaba wa gwamnatin jihar kan ayyukan raya ƙasa da kuma shirye-shiryen tallafa wa al’umma da take gudanarwa a sassa daban-daban na Kano.

Sarkin ya ce waɗannan shirye-shirye na samar da tasiri mai ma’ana a matakin ƙananan hukumomi da sauran al’ummomin karkara.

Gwamna Abba ya raba tallafi a Kano
Sarkin Gaya tare da Gwamna Abba a wajen rabon tallafin Hoto: Isah Muhammad Salisu
Source: Facebook

Kwamishinar ta yi kira a zaɓi 2027

A nata jawabin, Kwamishinar Harkokin Mata, Yara da Mutanen da ke da Buƙatu na Musamman, Hajiya Amina Abdullahi, ta buƙaci waɗanda za su amfana da shirin su mara wa APC baya a dukkan matakan zaɓen 2027.

Kwamishiniyar ta bayyana cewa sake zaɓen APC zai ba jam’iyyar damar ci gaba da shirye-shiryen inganta walwalar mata da kuma rayuwar iyalai a faɗin jihar.

Ta kuma jaddada cewa ci gaba da mulkin APC zai ba gwamnati damar faɗaɗa shirye-shiryen tallafa wa mata da sauran manufofin inganta rayuwar al’umma.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta fadi abubuwa 3 da masu son samun tallafin N50,000 za su kiyaye

Gwamna Abba ya ba 'yan Najeriya hakuri kan Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya buƙaci ’yan Najeriya su kara haƙuri da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Gwamna Abba ya yi ikirarin cewa nan ba da daɗewa ba yan ƙasar za su fara farin ciki saboda sun fara cin moriyar sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Tinubu ta aiwatar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng