Dan Majalisar Kano Ya Faɗi Lokacin da Mulki Zai Dawo Arewa, Ya Roƙa wa Tinubu Alfarma

Dan Majalisar Kano Ya Faɗi Lokacin da Mulki Zai Dawo Arewa, Ya Roƙa wa Tinubu Alfarma

  • Abubakar Kabir Bichi ya bukaci ’yan Arewa su goyi bayan sake zaben Tinubu a 2027, yana mai cewa mulki zai koma yankin bayan wa’adinsa na biyu
  • Dan majalisar ya ce Arewa ta yi shekaru takwas karkashin Buhari, don haka ya kamata Kudu ta kammala nata shekaru takwas kafin sauyin mulki
  • Bichi ya bayyana ayyukan tituna, ruwa da ban ruwa da gwamnatin Tinubu ta gudanar a jihohin Arewa, yana mai cewa yankin ya amfana sosai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Shugaban kwamitin kasafin kudi na Majalisar Wakilai, Abubakar Kabir Bichi, ya yi kira ga al'ummar Arewa da su marawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya domin sake zabensa a shekarar 2027.

Dan majalisar ya bayyana cewa damar shugabancin Najeriya za ta koma hannun Arewa ne bayan Tinubu ya kammala wa’adinsa na biyu, kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

Kara karanta wannan

'Ku duba darajar mahaifinsa': Gwamna ya nema wa Yusuf Buhari alfarma a 2027

Dan majalisar Kano ya roƙi a sake zaben Tinubu
Dan Majalisar Tarayya a Kano, Abubakar Kabir Bichi. Hoto: Abubakar Kabir Bichi.
Source: Twitter

Bichi ya ce bai kamata Arewa ta nemi karbar mulki daga hannun Kudu a yanzu ba, domin yankin bai kammala wa’adin shekaru takwas da aka ware masa ba, cewar Daily Trust.

Bichi ya fadi dalilin Arewa na goyon bayan Tinubu

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, dan majalisar mai wakiltar mazabar Bichi ta jihar Kano ya bayyana hakan ne yayin wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Dutse, babban birnin jihar Jigawa, ranar Lahadi.

Ya ce Arewa ta shafe shekaru takwas tana mulki karkashin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, yayin da gwamnatin Tinubu ta Kudu ta yi shekaru hudu kacal.

A cewarsa, ya kamata Arewa ta bari Tinubu ya kammala wa’adinsa na biyu kafin ta sake neman shugabancin kasar.

Bichi ya ce:

“Me ake nufi da wannan? Mun yi shekaru takwas a karkashin marigayi tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari. Yanzu su ma sun yi shekaru hudu, bari su kammala nasu domin mu ci gaba.

Kara karanta wannan

"Atiku Abubakar zai lashe jihohin Arewa 13 a zaben shugaban ƙasa na 2027"

“Bari Shugaba Tinubu ya kammala wa’adinsa na biyu, daga nan mulki zai dawo Arewa. Shugaba Tinubu yana kaunar Arewa kuma ya yi wa yankin abubuwa masu kyau.”
An bukaci marawa Tinubu baya a Arewa
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Source: Getty Images

Bichi ya kare Tinubu game da Arewa

Bichi ya kuma yi watsi da ikirarin cewa gwamnatin Tinubu ta yi watsi da Arewa, inda ya ce yankin ya samu tagomashi ta fuskar ayyukan more rayuwa da tsare-tsaren gwamnati.

Ya bayyana cewa yadda jama'a ke fitowa a tarukan yakin neman zaben jam'iyyar APC a yankin wata alama ce ta goyon bayan da suke bai wa shugaban kasar.

A cewarsa, gwamnatin Tinubu ta gudanar da ayyukan raya kasa a dukkan jihohin Arewa, ba tare da barin wata jiha a baya ba, cewar Punch.

Ya ce:

“Akasin ikirarin wasu cewa Tinubu bai damu da Arewa ba, shugaban kasar ya nuna jajircewarsa wajen bunkasa yankin ta hanyar manyan ayyukan more rayuwa da sauran shirye-shirye.
“Yawan mutanen da ke halartar tarukan APC a Arewa abin lura ne, kuma hakan na nuna cewa jama'a sun gamsu da abubuwan da shugaban kasa ya yi zuwa yanzu.”

Bichi ya bukaci Arewa ta rama wa Tinubu

Kara karanta wannan

Tinubu ya leƙo babbar matsalar ƴan Plateau, ya ɗauka masu alƙawari

Dan majalisar ya bayyana kwarin gwiwar cewa al'ummar Kano za su yaba da gudunmawar da Tinubu ya bayar wajen ci gaban jihar.

Ya kuma yi alkawarin bayyana karin bayanai kan ayyukan da aka gudanar a Kano karkashin gwamnatin shugaban kasar.

Bichi ya bukaci al'ummar Arewa da su mayar da martani kan abin da ya kira kokarin Tinubu wajen bunkasa yankin ta hanyar goyon bayan sake zabensa.

Alherin Tinubu ga Buhari - Abubakar Bichi

Mun ba ku labarin cewa Abubakar Kabir Bichi ya ce Muhammadu Buhari ya lashe zaɓen 2015 ne saboda goyon bayan Bola Tinubu.

Saboda haka ya buƙaci ’yan Arewa su rama wannan alheri ta hanyar zaɓen shugaban Najeriyan a takarar 2027.

Hon. Bichi ya ce manyan APC a Kano ta Arewa sun sa burin samun ƙuri’u miliyan ɗaya a zaben shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.