Akwai Kura: An Taso Tinubu a Gaba kan Yunkurin Kinkimo Bashin N11trn
- Kwamitin kamfen ɗin Seyi Makinde ya buƙaci gwamnatin Tinubu ta bayyana cikakkun bayanai kan yarjejeniyoyin bashin da aka ce sun kai Naira tiriliyan 11.2
- Kungiyar ta yi zargin cewa jingina gangar ɗanyen mai miliyan 340 na nan gaba zai iya rage kuɗaɗen shigar Najeriya
- Ta buƙaci Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta gudanar da zaman sauraron ra’ayoyin jama’a domin binciken yarjejeniyoyin da tasirinsu ga ƙasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Kwamitin kamfen ɗin zaɓen shugaban ƙasa na Seyi Makinde, ya buƙaci gudanar da bincike a bayyane kan rahoton cewa gwamnatin tarayya ta jinginar da gangar ɗanyen mai miliyan 340 da Najeriya za ta samar nan gaba domin samun basussukan da aka kiyasta sun kai Naira tiriliyan 11.2.
Ƙwamitin na Makinde-Daura Presidential Campaign Organisation (MDPCO) ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da jinginar kuɗaɗen shigar mai na nan gaba domin biyan basussuka ba tare da isasshen bayani ga jama'a ba.

Kara karanta wannan
"Ku ce ni da Kwankwaso mun gaza"; Peter Obi ya dauki muhimmin alkawari ga 'yan Najeriya

Source: Facebook
An nemi a bayyana bayanan bashin
Jaridar Premium Times ta ce a cikin wata sanarwa da daraktan sadarwa da tsare-tsare na kwamitin, Richard Ihediwa, ya fitar ranar Alhamis, 12 ga watan Nuwamban 2026 ya ce an samo basussukan ne ta yarjejeniyoyin samar da kuɗi guda huɗu.
Yarjejeniyoyin sun haɗa da Project Gazelle, Project Gazelle II, Project Leopard da Project Leopard II. Ya yi gargaɗin cewa irin waɗannan yarjejeniyoyi na iya takura wa kuɗaɗen shigar Najeriya tsawon shekaru masu zuwa.
Kwamitin ya buƙaci gwamnatin tarayya ta bayyana sunayen waɗanda suka bayar da bashin, adadin kuɗin da aka karɓa, kuɗin ruwa, kuɗaɗen gudanarwa da jadawalin biyan bashin.
Ya kuma nemi a bayyana ainihin yawan gangar ɗanyen man da aka jingina a ƙarƙashin kowace yarjejeniya.
Sanarwar ta ce:
“Ya kamata Shugaba Tinubu ya fito ya yi wa jama'a bayani kan yarjejeniyoyin bashin.”
Haka kuma, kwamitin ya buƙaci a bayyana tsarin farashin da za a yi amfani da shi wajen samar da ɗanyen man, basussukan da ake son sake tsara biyan su da kuma cikakken tasirin kuɗi na yarjejeniyoyin.
Gargaɗin illar jinginar da kuɗaɗen shigar mai
Ƙungiyar kamfen ɗin ta bayyana yarjejeniyoyin a matsayin matakin da ba shi da kyakkyawan tsarin kula da kuɗaɗen gwamnati.
Ta ce gwamnati na jinginar da kuɗaɗen shigar da za a samu nan gaba domin biyan buƙatun kashe kuɗi na yanzu, ba tare da nuna irin jarin da aka zuba wajen bunƙasa masana'antu, samar da ababen more rayuwa da inganta rayuwar jama'a ba.
Ta kuma yi gargaɗin cewa yarjejeniyoyin da ke ƙayyade lokacin biyan bashin na iya hana Najeriya cin gajiyar hauhawar farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya.
A cewarta, hakan na iya rage kuɗaɗen shigar da gwamnati za ta samu nan gaba tare da takaita damar da ƙasar ke da ita wajen tsara kashe kuɗaɗenta.

Source: Facebook
Dalilin Makinde na kalubalantar Tinubu a 2027
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana dalilan da suka sa zai kalubalanci Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027 bayan goya masa baya a 2023.
Gwamna Makinde, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa na APM, ya lissafa manyan matsaloli guda hudu da yake ganin sun dabaibaye gwamnatin Bola Tinubu.
Asali: Legit.ng
