Yadda aka yi Arangama da 'Yan Adawa a Wajen Kamfen Din Tinubu
- An samu karamin tashin hankali a wajen gangamin yaƙin neman zaɓen jam'iyyar APC da aka gudanar a jihar Nasarawa
- Magoya bayan Mohammed Abubakar Adamu, sun yi wa magoya bayan Sanata Ahmed Aliyu Wadada martani da kirarin neman kujerar gwamna
- Jami'an tsaro sun shiga tsakani tare da tarwatsa masu yin kirarin hamayya domin dawo da zaman lafiya a wurin taron
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Lafia, Nasarawa – An samu ɗan takun-saka tsakanin magoya bayan 'yan takarar gwamnan jihar Nasarawa na jam'iyyun APC da SDP a wajen gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC da aka gudanar ranar Laraba.
Lamarin ya faru ne lokacin da Gwamna Abdullahi Sule ya jagoranci kirarin goyon bayan ɗan takarar gwamnan APC, Sanata Ahmed Aliyu Wadada, inda ya riƙa cewa, “Wadada Gwamna”.

Kara karanta wannan
2027: Yadda mutane suka riƙa rera 'Tinubu must go' yayin tarbar Atiku ya ja hankali

Source: Facebook
Daily Trust ta rahoto cewa magoya bayan ɗan takarar SDP, tsohon sufeto janar na 'yan sanda, Mohammed Abubakar Adamu, da ke wajen taron sun mayar da martani da kirarin, “IG Gwamna”.
Yadda aka yi cacar baki
Bayan magoya bayan tsohon IGP sun fara kirarin goyon bayansa, magoya bayan Wadada su ma suka ƙara ƙaimi wajen maimaita kirarin “Wadada Gwamna”.
Hakan ya haifar da hayaniya tsakanin ɓangarorin biyu, inda kowannensu ke ƙoƙarin rinjayar ɗayan da kirarin goyon bayan ɗan takararsa.
Jami'an tsaro da ke wajen taron sun yi gaggawar shiga tsakani, inda suka ture masu yin kirarin hamayya domin dawo da zaman lafiya da ba a samu cikas ga gudanar da taron ba.
Dalilin zuwan 'yan SDP taron
Duk da haka, magoya bayan tsohon IGP Adamu sun bayyana cewa ba su halarci taron ba ne domin tayar da hankali ko kawo cikas ga shirin jam'iyyar APC.
Sun ce sun je wajen ne domin nuna goyon bayansu ga ƙoƙarin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na neman wa'adi na biyu a zaɓen shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan
Takardun kotu sun fito, an ga dalilin cire Aminu Gwarzo daga jerin 'yan takarar gwamnan Kano
Sun ƙara da cewa duk da goyon bayansu ga ɗan takarar SDP, Mohammed Abubakar Adamu, a zaɓen gwamnan Nasarawa, suna kuma goyon bayan sake zaɓen Tinubu.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin bai hana ci gaba da gudanar da taron ba, domin Gwamna Sule ya ci gaba da jawabinsa, inda ya buƙaci magoya bayan APC su zaɓi 'yan takarar jam'iyyar daga sama har ƙasa.

Source: Facebook
'Yan APC sun koma ADC
A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi maraba da wasu magoya bayan Shugaba Bola Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima da suka sauya sheƙa zuwa jam'iyyar ADC.
Atiku ya bayyana cewa ya kamata 'yan Najeriya su tambayi dalilin da ya sa mutanen da suka kafa gida suka yanke shawarar ficewa daga cikinsa, yana mai cewa sun gaji da yunwa da rashin tsaro a yankin Arewa maso Gabas.
Ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC ya ce yana fatan karɓar waɗanda suka sauya sheƙar a hukumance, tare da yin alƙawarin magance matsalolin tsaro da tsadar rayuwa idan jam'iyyar ta samu nasara.
Asali: Legit.ng