Tallafin N50,000: Yadda Ake Duba Cancanta da Karbar Kudin cikin Sauki
- Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa tallafin N50,000 na shirin NERSI kyauta ne, ba bashi ba, kuma babu buƙatar wanda ya karɓa ya mayar da kuɗin
- An zaɓi waɗanda za su amfana ne daga rajistar talakawa ta ƙasa da bayanan tantance katin shaida, bisa la’akari da buƙata
- Masu cin gajiyar tallafin za su iya karɓar kuɗin ta wayar hannu, cirewa a POS ko tura su zuwa asusun banki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta fitar da cikakken bayani kan yadda ’yan Najeriya da aka zaɓa domin cin gajiyar tallafin N50,000 za su tabbatar da cancantarsu, amincewa da tayin, karɓar kuɗin da kuma cire shi.
Gwamnatin ta kuma gargaɗi waɗanda za su amfana da shirin da su yi hattara da ’yan damfara da ke ƙoƙarin amfani da damar domin yaudarar mutane.

Kara karanta wannan
Moniepoint ya fitar da hanya mai sauki ta duba waɗanda za su samu tallafin N50,000

Source: Getty Images
Bisa ga tambayoyi da amsoshin da aka wallafa a shafin shirin, waɗanda Legit Hausa ta gani a ranar Alhamis, 5 ga watan Nuwamban 2026 tallafin ba bashi ba ne, kuma ba sai mutum yana da wayar zamani ko intanet ba kafin ya karɓe shi.
Ga muhimman bayanai da masu cin gajiyar shirin ya kamata su sani:
1. Menene shirin NERSI, kuma nawa za a bayar?
NERSI wani shiri ne na Gwamnatin Tarayya da aka ƙirƙira domin taimaka wa iyalai wajen fuskantar tsadar rayuwa.
A ƙarƙashin shirin, kowane mutum da aka zaɓa zai karɓi N50,000 ta asusun kuɗi na wayar hannu.
Gwamnatin ta ce za a tura cikakken kuɗin ga waɗanda aka zaɓa ba tare da cire wani kaso ba.
Haka kuma, gwamnati ta jaddada cewa tallafin kyauta ne, ba bashi ba, don haka babu wanda zai biya kuɗin bayan karɓa.
2. Su waye suka cancanci tallafin, kuma yaya aka zaɓe su?
Gwamnati ta ce an zaɓi waɗanda za su amfana ne daga Rajistar Talakawa ta Ƙasa da bayanan katin shaida da aka tantance.
Ta bayyana cewa babu wanda zai iya neman shiga cikin shirin da kansa, haka kuma babu wanda ke da ikon saka wani cikin jerin waɗanda za su amfana.
An zaɓi mutane ne bisa la’akari da buƙatunsu, tare da tabbatar da cewa an samu wakilci daga dukkan yankunan siyasa shida na ƙasar.
Gwamnatin ta ce ba a ware kowa saboda addininsa, ƙabilarsa ko jam’iyyarsa ta siyasa ba. Sai dai za a riƙa biyan kuɗin ne a matakai daban-daban, don haka ba kowa ne zai samu saƙon sanarwa a lokaci guda ba.
3. Me ya sa aka zaɓe ni, kuma daga ina aka samo lambar wayata?
Gwamnati ta ce an gano waɗanda suka cancanta ne ta amfani da bayanan da ke cikin Rajistar Talakawa ta Ƙasa da sahihan bayanan katin shaida.
Ta bayyana cewa daga waɗannan bayanai ne aka samo lambobin wayoyin mutanen da aka zaɓa.
Bayanan masu cin gajiyar shirin za a miƙa su ne kawai ga kamfanonin da aka amince da su domin su biya kuɗin tallafin.
Gwamnatin ta kuma tabbatar da cewa za ta kare bayanan sirrin waɗanda za su amfana bisa tanadin Dokar Kare Bayanai ta Najeriya ta 2023.
Ta jaddada cewa jami’an shirin ba za su taɓa neman lambar sirrin banki (PIN), kalmar sirrin amfani sau ɗaya (OTP) ko lambar tantance asusun banki (BVN) ba.
4. Ta yaya waɗanda aka zaɓa za su san cewa sun cancanta?
Waɗanda suka cancanta za su samu saƙon waya daga ɗaya daga cikin kamfanonin biyan kuɗi guda biyar da gwamnati ta amince da su.
Kamfanonin sun haɗa da ALAT, MoMo PSB, NairaGram, OPay da Moniepoint.
Saƙon zai sanar da mutum cewa an zaɓe shi, tare da ba shi lambar USSD da zai kira domin amincewa da karɓar tallafin.
Haka kuma, mutum zai iya amfani da lambar USSD ta kamfanin da zai biya shi domin bincika ko ya cancanta.
Gwamnati ta ce saƙonnin da suka fito daga shirin na gaskiya za su zo ne ta sunayen kamfanonin da aka amince da su.
5. Ta yaya za a amince da karɓar tallafin N50,000?
Dole ne wanda aka zaɓa ya kira lambar USSD da ke cikin saƙon da aka tura masa, sannan ya bi umarnin da za a ba shi.

Kara karanta wannan
Shin tallafin N50,000 da aka fara turawa 'yan Najeriya bashi ne ko kyauta? An samu bayani
Wannan mataki zai buɗe masa asusun kuɗi na wayar hannu, bayan haka za a tura N50,000 ɗin zuwa gare shi tare da saƙon tabbatar da biya.
Gwamnati ta jaddada cewa ba za a tura wa mutum kuɗin ba sai ya fara amincewa da karɓar tallafin.
Ta shawarci waɗanda suka samu sanarwa su amince da wuri, inda ta ƙara da cewa kamfanonin biyan kuɗin za su riƙa tunasar da su.
Idan mutum ya zaɓi ƙin karɓar tallafin bisa kuskure, zai iya sake kiran lambar sannan ya zaɓi amincewa.
6. Shin waɗanda ba su da wayar zamani ko intanet za su iya karɓar kuɗin?
Eh. Gwamnati ta ce ba sai mutum yana da wayar zamani ko intanet ba kafin ya karɓi tallafin. Wayar hannu ta yau da kullum ta isa, domin lambobin USSD da kamfanonin biyan kuɗin suka bayar suna aiki ba tare da intanet ba.
Sai dai abokan cinikin MoMo PSB, OPay da Moniepoint za su iya amfani da manhajojin kamfanonin domin shiga asusun kuɗinsu da gudanar da hada-hadar kuɗi.
7. Ta yaya za a cire tallafin N50,000?
Gwamnati ta ce masu cin gajiyar shirin za su iya cire kuɗinsu ta hannun masu POS, ta hanyar tura kuɗin daga jakar wayarsu zuwa asusun wakilin POS sannan su karɓi kuɗin hannu.
Haka kuma, kowane kamfani na da wasu hanyoyin cire kuɗi ko tura su zuwa wani asusu.
ALAT: Za a iya amfani da lambar 94523Account NumberAmount# domin tura kuɗi zuwa asusun mai POS ko na bankin mutum. Haka kuma, ana iya zuwa reshen Wema Bank.
MoMo PSB: Ana iya zuwa wurin wakilansa ko masu POS, kiran 6710# ko amfani da manhajar MoMo NG.
NairaGram: Ana iya kiran 72600# sannan a bi umarnin tura kuɗi zuwa asusun mai POS ko na banki.
OPay: Ana iya amfani da 95520# ko manhajar OPay.
Moniepoint: Ana iya amfani da 557327# ko manhajar Moniepoint.
Gwamnati ta ce mutum zai iya cire dukkan kuɗin ko wani kaso daga ciki, sannan sauran su ci gaba da kasancewa a asusun kuɗinsa.
Haka kuma, ana iya tura kuɗin zuwa asusun bankin mutum ko na wani ta amfani da lambobin USSD ko manhajojin kamfanonin.
8. Shin akwai kuɗin caji wajen karɓa ko cire tallafin?
Gwamnati ta ce amincewa da tallafin, karɓar kuɗin da kuma amsa saƙonnin shirin duk kyauta ne. Ta gargaɗi jama’a da kada su biya wani mutum domin ya taimaka musu su samu tallafin ko ya saka sunansu cikin jerin waɗanda za su amfana.
Sai dai ta bayyana cewa masu POS na iya karɓar kuɗin cajin da suka saba karɓa idan mutum ya cire kuɗinsa ta hannunsu.
Saboda haka, gwamnati ta shawarci masu cin gajiyar shirin su fara tambayar nawa za a cire musu kafin su gudanar da hada-hadar.
9. Me ya kamata mutum ya yi idan bai samu saƙon waya ba?
Gwamnati ta ce mutanen da ba su samu saƙon sanarwa ba kada su ɗauka kai tsaye cewa ba a zaɓe su ba.
Ta bayyana cewa ana biyan tallafin ne a matakai, kuma kamfanonin da aka amince da su za su riƙa aika saƙonni ga waɗanda aka zaɓa a rukuni-rukuni.
Sai dai gwamnati ta kuma yi bayanin cewa ba kowa ne zai samu tallafin a wannan matakin ba, domin shirin na da adadin iyalai da aka tsara za a tallafa wa a kowane lokaci.

Source: Twitter
Batun wani ya karbar maka tallafin N50,000
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta fayyace cewa babu wanda zai iya karɓar tallafin Naira 50,000 na wata-wata a madadin wani mutum.
Gwamnatin ta yi bayanin cewa ana tura kuɗin ne ta hanyar lambar wayar wanda aka yi wa rajista domin samun tallafin.
Asali: Legit.ng



