Abin da Gwamnatin Tarayya Take So Mutum Ya Yi idan Aka Tura Masa Sakon Tallafin N50,000

Abin da Gwamnatin Tarayya Take So Mutum Ya Yi idan Aka Tura Masa Sakon Tallafin N50,000

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana abin da mutum ya kamata ya yi bayan an tura masa sakon cewa yana cikin wadanda za a ba tallafin N50,000
  • Gwamnatin ta yi karin haske kan ko akwai ƙayyadadden lokacin da ’yan Najeriya za su amsa saƙon sanar da su cancantar samun tallafin NERSI
  • Za a riƙa aika saƙonnin tunatarwa ga waɗanda ba su ɗauki mataki ba bayan an sanar da su sun cancanci tallafin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria – Gwamnatin Tarayya ta yi karin haske kan tambayoyin da ’yan Najeriya ke yi game da ko akwai ƙayyadadden wa’adin amincewa da tallafin kuɗi na N50,000.

A cewar gwamnati, ba dole ba ne masu cin gajiyar shirin su ɗauki danna amincewa da kudin "Accept" cikin wa'adin kwanaki ba amma ta ƙarfafa musu gwiwa da su amsa saƙon danna lambar amincewa da zarar sun samu sakon.

Kara karanta wannan

Tallafin N50,000: Yadda ake duba cancanta da karbar kudin cikin sauki

Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yana jagorantar taron FEC a Aso Rock da ke Abuja Hoto: Sunday Dare
Source: Twitter

An kayyade wa'adin karbar tallafin?

Punch ta tattaro cewa umarnin gwamnati a bayyane yake: da zarar mutum ya samu saƙon SMS da ke sanar da shi cewa ya cancanta, ya kamata ya danna lambar amincewa da wuri domin a tura masa kudin

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa kamfanin da ke kula da biyan kuɗin zai riƙa aika saƙonnin tunatarwa ga duk wanda bai riga ya amsa ba.

Hakan zai taimaka wajen tabbatar da cewa ’yan Najeriya da suka cancanta ba su rasa tallafin ba saboda kawai ba su danna alamar amincewa nan take ba.

Wannan karin haske ya biyo bayan damuwar da ’yan Najeriya da dama suka nuna kan ko rashin amsa saƙon farko zai hana su samun tallafin.

An ruwaito cewa wasu daga cikin waɗanda suka samu sanarwar sun yi jinkirin amsawa saboda rashin fahimtar yadda tsarin yake aiki ko kuma fargabar cewa saƙon SMS ɗin ba na gaskiya ba ne.

Kara karanta wannan

Hankali ya kwanta: An bayyana dalilin da ya sa wasu ba su samu saƙon tallafin N50,000 ba

Yadda tallafin NERSI yake aiki

Shirin NERSI na daga cikin manyan matakan da Gwamnatin Tarayya ke ɗauka domin rage nauyin matsin tattalin arziki a kan ’yan Najeriya masu rauni.

Matakin na zuwa ne daidai lokacin da ake fuskantar ƙalubalen da suka haɗa da cire tallafin man fetur da tashin farashin kayayyaki da hidimomi.

Waya.
Wata dattijuwa mai shekaru 90 a duniya tana danna lambobin waya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A ƙarƙashin shirin, waɗanda suka cancanta za su riƙa samun tallafin kuɗi kai tsaye na Naira 50,000 duk wata.

Gwamnati ta buƙaci ’yan Najeriya da suka samu saƙon SMS na sanar da cancantarsu da su ɗauke shi a matsayin saƙo na gaskiya, tare da amsawa cikin gaggawa maimakon jiran saƙon tunatarwa.

Yadda ake raba tallafin NERSI

Kun ji cewa Gwamnatin tarayya ta bayyana dalilin da ya sa wasu ba su samu saƙon tallafin N50,000 ba har kawo yanzu

Gwamnati ta ce ana tura wa mutane tallafin N50,000 ne a mataki mataki, kuma ana tura saƙonnin sanarwa ga waɗanda suka cancanta rukuni-rukuni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262