Shin Tallafin N50,000 da Aka Fara Turawa Yan Najeriya Bashi ne ko Kyauta? An Samu Bayani

Shin Tallafin N50,000 da Aka Fara Turawa Yan Najeriya Bashi ne ko Kyauta? An Samu Bayani

  • Gwamnatin Tarayya ta fara tura wa yan Najeriya masu karamin karfi tallafin N50000 duk wata karkashin shirin NERSI
  • Sai dai tun bayan fara raba wannana tallafi mutane suka fara tambaya da nuna shakku gydu kada kudin su kasance rance ne
  • Ma’aikatar Jin ƙai da Rage Talauci ta Tarayya na zaɓar waɗanda za su amfana ta hanyar amfani da bayanan shaidar ɗan ƙasa da rajistar jinƙai ta ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Najeriya - Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta fara gudanar da wani shirin tallafi mai suna National Emergency Relief and Stabilisation Intervention (NERSI).

Gwamnatin ta kirkiro wannan shiri ne domin taimaka wa gidaje matalauta da masu rauni wajen fuskantar hauhawar tsadar rayuwa da ake fama da ita a kasar nan.

Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yana rattaba hannu kan doka a fadar Aso Rock Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da gwamnatin tarayya ta fitar ta hannun ma'aikatar jin kai, da aka wallafa a shafin NERSI na yanar gizo.

Kara karanta wannan

Tallafin N50,000: Gwamnatin tarayya ta yi bayani kan ko wakili zai iya karba

Ma’aikatar Jinƙai da Rage Talauci ta Tarayya ce ke kula da shirin, wanda ke aika kuɗin tallafin N50,000 kai tsaye zuwa asusun wayar hannu na waɗanda aka zaɓa duk wata.

Shin tallafin N50,000 bashi ne ko kyauta?

An zabi kamfanonin hada-hadar kudi kamar Opay da Moniepoint wajen tura wa mutane wannan tallafi kai tsaye zuwa asusun da suka bude da lambobin wayoyinsu.

Dukkan kuɗin N50,000 na shiga asusun duk wanda aka zaba domin ya amfana ba tare da cire wani kaso ba.

Duk da ruɗanin da ya yaɗu tsakanin ’yan Najeriya game da wannan kudi, gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa kudin ba bashi ba ne.

Sanarwar da aka fitar da nuna cewa kudin tallafi ne da Gwamnatin Tarayya ke bayarwa a kyauta, don haka babu wanda za a tilasta ya mayar da kuɗin.

Ma’aikatar ba ta karɓar buƙatun neman shiga shirin NERSI daga kowa kai tsaye. Maimakon haka, ana tantance waɗanda za su amfana ta hanyar amfani da ingantattun bayanan shaidar ɗan ƙasa da kuma rajistar jinƙai ta ƙasa.

Kara karanta wannan

Yadda Opay ke turawa mutane tallafin N50,000 na gwamnatin tarayya

An tsara tsarin zaɓen ne domin gano gidajen da aka ware a matsayin matalauta da masu rauni.

Yadda ake tuntubar wadanda suka cancanta

Sakamakon ana tantance cancantar mutum ne ta amfani da bayanansa da gwamnati take d su, maimakon mutum ya miƙa sunansa da kansa, ’yan Najeriya ba za su iya neman tallafin kai tsaye ba.

Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yana aiki a ofis a fadar Aso Rock, da hoton takardun kudi daga gefen dama Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook

Ana tuntuɓar waɗanda suka cancanta ne ta hanyar tsarin da gwamnati ta riga ta tanada.

Ma’aikatar Jinƙai da Rage Talauci ta Tarayya ta wallafa bayanai kan shirin a shafinta na intanet na hukuma domin jama’a su samu ƙarin bayani game da yadda tallafin ke gudana.

Wani zai iya karbar tallafin dan uwansa?

Kun ji cewa Gwamnatin tarayya ta ce za a biya tallafin Naira 50,000 kai tsaye ga wanda aka yi wa rajista, ta hanyar lambar wayarsa

Ɗan uwa ko amintaccen mutum zai iya taimaka wa mai cin gajiyar tallafin wajen latsa lambar shiga, amma shi ne zai shigar da PIN ɗinsa domin cire kudin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262