Gwamna Bala Ya Yi Ta'aziyyar Babban Dan Siyasar da Ya Rasu a Bauchi

Gwamna Bala Ya Yi Ta'aziyyar Babban Dan Siyasar da Ya Rasu a Bauchi

  • Shugaban karamar hukumar Zaki a jihar Bauchi, Mas’ud Umar, ya rasu a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da shi a daren Lahadi
  • Gwamna Bala Mohammed ya bayyana alhininsa kan rasuwar shugaban karamar hukumar, inda ya bayyana shi a matsayin ma'aikacin gwamnati mai kishin al'umma
  • Za a yi sallar jana'izarsa da karfe 2:00 na rana a yau Litinin, 2 ga watan Nuwamba, 2026, a fadar Dagacin Mur Mur da ke karamar hukumar Zaki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi – Shugaban karamar hukumar Zaki a jihar Bauchi, Malam Mas’ud Umar, ya rasu a daren Lahadi sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da shi a kauyen Konkiyal da ke karamar hukumar Darazo.

Rahotanni sun nuna cewa marigayin na kan hanyarsa ta komawa Zaki ne bayan halartar taron manyan masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APM da aka gudanar a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Babban dan siyasa ya yi hadarin mota ya rasu ana shirin 2027

Arise News ta rahoto cewa lamarin ya faru ne makonni biyu kacal bayan wani hatsarin mota da ya yi sanadin mutuwar babban sakataren hukumar kula da inshorar lafiya ta jihar Bauchi, Ibrahim Ladan-Duguri, da yaransa hudu.

Ta'aziyyar gwamna Bala Mohammed

Rahotanni sun nuna cewa gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana matukar alhini da kaduwa kan rasuwar Mas’ud Umar.

A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Mukhtar Gidado, ya fitar, gwamnan ya mika sakon ta'aziyyarsa ga iyalan marigayin, al'ummar karamar hukumar Zaki da masarautar Katagum.

Gwamnan ya bayyana marigayin a matsayin ma'aikacin gwamnati mai kishin kasa, dan siyasa mai jajircewa a matakin kasa da kasa, kuma shugaba mai tausayi wanda gudummawarsa ga ci gaban al'umma ba za ta gushe daga tarihin jihar Bauchi ba.

Ya kuma mika ta'aziyyarsa ga kungiyar shugabannin kananan hukumomi ta ALGON reshen jihar Bauchi, abokai da sauran wadanda rasuwar ta shafa.

Matsayin da marigayin ya rike

Kafin zabensa a matsayin shugaban karamar hukumar Zaki, Mas’ud Umar ya taba rike mukamin Darakta-Janar na hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Bauchi (SEMA).

Sanarwar gwamnan ta bayyana cewa a lokacin da yake jagorantar hukumar, ya nuna himma wajen ba da agajin gaggawa, kula da bala'o'i da tallafa wa al'ummomin da suka fuskanci matsaloli.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya cika shekara 20 a kan karagar mulki

Taswirar jihar Bauchi
Taswirar jihar Bauchi a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Yaushe za a yi jana'izar Mas’ud?

Gwamna Bala Mohammed ya nuna cewa za a yi sallar jana'izar marigayin a yau Litinin, 2 ga watan Nuwamba, 2026, da karfe 2:00 na rana.

Rahotanni sun nuna cewa za a gudanar da sallar ne a fadar Dagacin Mur Mur da ke karamar hukumar Zaki a jihar Bauchi.

Gwamna Bala Mohammed ya yi addu'ar Allah Ya gafarta wa marigayin, Ya jikansa da rahama, sannan Ya ba iyalansa, abokansa da al'ummar Zaki hakurin jure wannan rashi.

An kashe matashi a Bauchi

A wani labarin, mun ruwaito cewa an kashe wani matashi mai suna Ibrahim Jadda yayin da wata takaddamar siyasa ta barke tsakaninsa da abokinsa a wurin aikinsu a birnin Bauchi.

Rahotanni sun bayyana cewa sabanin ya samo asali ne daga wata mahawarar siyasa da suka yi kwana guda kafin faruwar lamarin.

Rundunar 'yan sanda ta kama wanda ake zargi da aikata laifin, Sallau, a unguwar Liman Katagum da ke karamar hukumar Bauchi, inda yake tsare a halin yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng