An Budewa Tinubu Dakin Ka'aba Ya Shiga, 'Yan Najeriya Sun Yi Martani
- Rahoton shigar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu cikin Ka'aba, wuri mafi tsarki a Musulunci, ya jawo martani mabambanta daga 'yan Najeriya a kafafen sada zumunta
- Yayin da wasu suka bayyana farin cikinsu da ganin shugaban ƙasar ya samu wannan dama, wasu sun nuna damuwa kan shingayen da aka kafa a kusa da Ka'aba
- Wasu daga cikin masu sharhi sun kuma yi tambaya kan yadda ake ba shugabannin siyasa damar shiga wannan wuri mai tsarki, alhali sauran Musulmi ba sa samun irin wannan dama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Rahoton shigar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu cikin Ka'aba da ke cikin Masallacin Harami a birnin Makka na ƙasar Saudiyya ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta.
Wasu 'yan Najeriya sun bayyana farin cikinsu da wannan dama da shugaban ƙasar ya samu, yayin da wasu suka nuna rashin jin daɗinsu kan yadda aka tsara shigar tasa da kuma shingayen da aka kafa a kusa da wurin.

Source: Facebook
Legit ta samu bayanai da suka nuna an budewa shugaban kasar dakin Ka'aba ne a wani sako da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya wallafa a Facebook.
An yi murna da shigar Tinubu Ka'aba
Wani mai amfani da shafin X mai suna Shaekih ya bayyana farin cikinsa da rahoton shigar shugaban ƙasar cikin Ka'aba, yana mai cewa hakan abin alfahari ne ga 'yan Najeriya.
Leadership ta wallafa cewa ya rubuta cewa:
"Ina jin alfahari a matsayina na ɗan Najeriya saboda Allah ya ba shugabana damar shiga Ka'aba."
Martaninsa ya nuna yadda wasu daga cikin 'yan Najeriya suka ɗauki wannan dama a matsayin abin farin ciki da daraja ga shugaban ƙasar.
An soki shingayen da aka kafa
A gefe guda, wata mai amfani da shafin X mai suna Ribbah ta soki yadda aka tsara shigar shugaban ƙasar, tana mai cewa bai kamata a samu bambanci tsakanin masu mulki da sauran Musulmi wajen samun damar kusantar wannan wuri mai tsarki ba.
Ta rubuta cewa:
"Abin kunya ne. Ya kamata Ka'aba ta kasance ga kowa da kowa. Yanzu an ware masu hannu da shuni daga talakawa."
Haka kuma, Ahmed Shah ya nuna damuwa kan yadda ake amfani da damar shiga Ka'aba wajen ɗaukaka matsayin shugabannin siyasa, yana mai cewa bai kamata a mayar da wannan dama wata hanyar ƙara darajar siyasar wani shugaba ba.

Source: Facebook
Abin sani game da Ka'aba
Ka'aba tana cikin Masallacin Harami da ke birnin Makka na ƙasar Saudiyya, kuma ita ce alkiblar da Musulmi a faɗin duniya ke fuskanta yayin gudanar da sallolinsu.
Haka kuma, Musulmi na yin ɗawafi a kewayen Ka'aba yayin gudanar da aikin Hajji da Umara.
Bayo Onanuga, ya wallafa hoton da ke nuna Sheikh Dahlulah Muthawal na Masallacin Harami, Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jami'in kula da harkokin ladabi na gwamnati, Ahmad Zafeer, yayin buɗe Ka'aba domin shugaban ƙasar a ranar Lahadi.
APM ta soki Tinubu

Kara karanta wannan
"Kamar yana raye," Abubuwan da aka ji mabiyan Sheikh Masussuka na fada a wurin jana'iza
A wani labarin, mun ruwaito cewa ƙungiyar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa ta Makinde-Daura (MDPCO), ƙarƙashin jam'iyyar APM, ta buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya janye daga takarar 2027.
Daraktan yaɗa labarai da dabarun sadarwa na ƙungiyar, Richard Ihediwa, ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani kan yawan tafiye-tafiyen da shugaban ƙasar ke yi zuwa ƙasashen waje.
Ƙungiyar ta yi zargin cewa Tinubu ba shi da ƙarfin da ake buƙata domin ci gaba da gudanar da mulki, tana mai cewa Najeriya na buƙatar shugaba mai kuzari da ƙwarewar jagoranci.
Asali: Legit.ng

