Jiga Jigan PDP 3 Sun Mutu a Hatsarin Mota a Kaduna yayin Kamfen Siyasa
- Wasu mambobin PDP uku daga karamar hukumar Jema’a a Kaduna sun mutu a wani hatsarin mota a kan hanyar Kaduna zuwa Kafanchan
- Marigayan sun hada da sakataren PDP na Jema’a, Comrade Caleb Ishaya Alot, da wasu mata biyu
- Dan takarar gwamnan Kaduna na ADC, Isa Mohammed Ashiru, ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga jam’iyyar PDP
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Akalla mambobin jam’iyyar PDP uku daga karamar hukumar Jema’a a jihar Kaduna sun rasu a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a kan hanyar Kaduna zuwa Kafanchan.
Rahotanni sun bayyana cewa mutanen uku na kan gudanar da ayyukan jam’iyya a hukumance a lokacin da hatsarin ya rutsa da su.

Source: Twitter
Wakilin Legit Hausa ya gano sakon ta'aziyyar Isa Ashiru Kudan ne a shafinsa na X a yau Laraba 4 ga watan Nuwambar 2026.

Kara karanta wannan
Kotu ta soke tikitin ɗan takarar gwamna a 2027, ta umarci a sake zaben fitar da gwani
An bayyana sunayen wadanda suka rasun da Comrade Caleb Ishaya Alot, sakataren PDP na karamar hukumar Jema’a; Mercy Achi, shugabar mata ta yankin jam’iyyar Wise Women a Jema’a; da Charity Bahago, mamba a kungiyar ta mata.
Isa Ashiru ya yi jimamin rasuwar mambobin PDP
Dan takarar gwamnan jihar Kaduna a karkashin jam’iyyar ADC a zaben 2027, Rt. Hon. Isa Mohammed Ashiru, na cikin wadanda suka fara mayar da martani kan rasuwar mambobin PDP ukun.
Ashiru ya bayyana cewa ya samu labarin rasuwar tasu cikin matukar kaduwa da alhini, inda ya mika sakon ta’aziyya ga shugabannin PDP na jiha, shiyya da karamar hukuma.
Haka kuma, ya jajantawa iyalan mamatan da sauran mambobin jam’iyyar PDP a karamar hukumar Jema’a da jihar Kaduna baki daya.
Ashiru, wanda aka fi sani da Sarkin Bai Zazzau, ya ce rasuwar mutanen ta shafi iyalansu da kuma daukacin tsarin jam’iyyar PDP a yankin.

Kara karanta wannan
2027: Kusoshin jam'iyyar NDC da aka rabu da su alhali Peter Obi yana tsakiyar kamfe

Source: Original
An bayyana mukaman mamatan a PDP
Marigayi Comrade Caleb Ishaya Alot ya kasance sakataren jam’iyyar PDP na karamar hukumar Jema’a, yayin da Mercy Achi ta jagoranci bangaren mata na kungiyar Wise Women a shiyyar.
Ita kuwa Charity Bahago mamba ce a wannan kungiya ta mata ta jam’iyyar mai adawa a Kaduna da Najeriya baki daya.
A cewar sanarwar Ashiru, dukkansu sun rasu ne a lokacin da suke gudanar da ayyukan da suka shafi jam’iyyar.
Sai dai sanarwar ba ta yi cikakken bayani kan yadda hatsarin ya faru ko musabbabinsa ba.
A sakon ta’aziyyarsa, Ashiru ya roki Allah ya jikansu da rahama, ya ba iyalansu hakurin jure wannan rashi, tare da bai wa shugabanni da mambobin PDP karfin zuciyar jure wannan babban rashi.
Ashiru Kudan ya caccaki Gwamna Uba Sani
Mun ba ku labarin cewa Isa Ashiru Kudan yayi bayanin dalilinsa na dagewa wajen neman takarar gwamna a jihar Kaduna.
‘Dan takaran na jam’iyyar ADC ya ce nasara da rashinta daga Allah SWT kuma gare Shi yake nema.
Hon. Isa Ashiru ya ce akwai bambanci sosai tsakaninsa da Uba Sani da yanzu yake kan karaga.
Asali: Legit.ng
