Isa Ashiru Mai Takara a Jam’iyyar ADC a Kaduna Ya Tona wa Gwamnatin Uba Sani Asiri
- Isa Ashiru Kudan yayi bayanin dalilinsa na dagewa wajen neman takarar gwamna a jihar Kaduna
- ‘Dan takaran na jam’iyyar ADC ya ce nasara da rashinta daga Allah SWT kuma gare Shi yake nema
- Hon. Isa Ashiru ya ce akwai bambanci sosai tsakaninsa da Uba Sani da yanzu yake kan karaga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kaduna - Isa Ashiru Kudan wanda yake neman takarar gwamnan jihar Kaduna ya yi wa gwamnatin Uba Sani kaca-kaca.
Hon. Isa Ashiru Kudan ya koka game da yadda Mai girma Uba Sani yake jagorantar Kaduna tun da ya shiga ofis a 2023.

Source: Facebook
Bambancin Isa Ashiru da Uba Sani
Da yake hira da DCL Hausa a makon nan, ‘dan takaran na jam’iyyar ADC ya ce ya sa bam-ban sosai da Gwamna Uba Sani.
Na farko ya ce shi ya san Kaduna saboda haifaffen jihar ne kuma ya yi aikin gwamnatin jiha har ta kai ya gama yana cin fansho.

Kara karanta wannan
Mutuwar uwa, fadan ‘ya ‘yansa da abubuwa 10 da suka faru da El Rufai da yake tsare
Baya ga haka, yana tunkaho da cewa ya yi ‘dan majalisar dokoki da ‘dan majalisar wakilan tarayya na shekara da shekaru.
Gwamna Uba Sani bai zama a Kaduna?
Isa Ashiru Kudan ya ce shi Gwamna Uba Sani kuwa bai san Kaduna ba kuma duk da yana gwamna, bai cika zama a jihar ba.
Yake cewa:
Bai san ta ba. Yaushe rabon shi ma da Kadunar.
Mutum yana jiha sati biyu an tafi kuma sai bayan sati biyu a dawo. Wannan ai ba shi ne sanin jihar Kaduna.
Ya ce Kaduna tana bukatar wanda ya san ta saboda tana dauke da kabilu rututu da mutane masu bin addinai dabam-daban.
Isa Ashiru ya soki mulkin Uba a Kaduna
Duk da wahalar da APC ta sha a zaben 2023, Sanata Uba bai shirya zama gwamna ba, yana ganin a sama ya samu mulki.
Ya yi zargin cewa Gwamnatin APC ta lalata bangarori dabam-dabam, yana mai bada misali da harkar noma a jihar Kaduna.
Ashiru Kudan ya ce sai kwanakin baya da damina ta zo karshe ne aka raba mutane takin da ya kamata a ba su kafin noma.
A hirar, ya yi magana game da yadda ake yawan garkuwa da mutane har a cikin birnin Kaduna.
Isa Ashiru: 'Akwai matsalar tsaro har a Kaduna'
Game da batun tsaro, ya yi watsi da maganar da ake yi cewa a yanzu an samu zaman lafiya a yankuna irinsu Birnin gwari.
‘Dan adawan yana ganin cewa duk bidiyoyin da aka gani na mutane na bin hanyar bogi ne, ba haka abin da yake a zahiri ba.
‘Dan takaran ya ce yana da labarin halin da ake ciki, babu zaman lafiya musamman a yankunan da ke kan iyaka da Zamfara.
Kudan ya fake da cewa yana da abokai da suke yawan bin hanyar birnin Gwari zuwa Kagara kuma ya taba yin aiki a yankin.
Duba ayyukan majalisa sun rika kai shi wannan yanki a lokacin da ya wakilci Kudan da Makarfi.
Dalilinsa na dagewa wajen neman mulkin Kaduna
‘Dan siyasar wanda tun 2015 yake son zama gwamna ya ce ya fahimci mulki na Ubangiji ne kuma a wajen Sa yake nema.
Isa Ashiru yake cewa:
"Mulki na wane ne? Na Allah ne!"
Tunda ban samu yadda nake so a lokacin da na ke so ba, ni na fi son zabin Allah dama."
Ya ce saboda ya yi taimakai rayuwar jama’a ya nace wajen ganin ya zama gwamna a Kaduna don haka yake rokon a zabe shi.
Matsalolin da Nasir El-Rufai ya fuskanta a 2026
Mutuwar mahaifiyarsa a Maris 2026 na cikin abubuwan takaici da suka faru da Nasir El-Rufai da aka kama kamar yadda muka rahoto.
Iyalinsa sun yi maganganu musaman kan zargin hana kai masa abinci da kin bari su gan shi a ICPC tun farkon kama shi da aka yi.
Kafin a daina jin duriyarsa, a bainar jama’a aka samu aka Bashir El-Rufai yana cin mutuncin yayan da Bello da Malam yake hannu.
Asali: Legit.ng

