Haduran mota a Najeriya
Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci jihar Jigawa domin jaje bayan hadarin tankar man fetur. Buhari ya ba da tallafi Naira miliyan 10 a Jigawa.
Wata motar haya da ta kuccewa direba ta daki bakin gada, ta faɗa kogi a karamar hukumar Njaba da ke jihar Imo, duka fasinjojin cikin motar sun kwanta dama.
Allah ya yi wa tsohon mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Kwara, Hon Christopher Ayeni rasuwa sakamakon wani mummunan hatsari da ya rutsa da shi.
Wani dan acaɓa ya rasu bayan karo da ya yi da tirelar Dangote a jihar Legas. Motar kamfanin Dangote ta markaɗa ɗan acaɓan har lahira yayin da suka yi karo.
Wasu sojojin saman Najeriya sun gamu da hatsarin mota yayin sa suke kan hanyar zuwa babban birnin tarayya Abuja. Sojoji biyar sun kwanta dama a hatsarin.
Hukumar kiyaye haɗurra FRSC ta ƙasa rashen jihar Filato ta tabbatar da mutuwar baki ɗaya fasinjojin wata mota da ta gamu da hatsari a Hwan Kibo yau Talata.
Wani direban mota ya ce a yanzu ya koma sayen gas din CNG na N7,000 a rana a madadin N30,000 da yake kashewa don sayen man fetur a aikinsa na tuki.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya kafa tarihi a Jihar Jigawa inda ya fara dura jihar domin mika tallafin N100m ga wandanda tankar mai ta kona a garin Majiya.
Wata mota mai amfani da iskar gas na CNG ta fashe a wani gidan mai da ke jihar Edo. Lamarin ya jawo firgici yayin da wasu mutane suka samu raunuka.
Haduran mota a Najeriya
Samu kari