Zaman Majalisa Ya Yi Zafi, Sanata Barau da Ningi Sun Gwabza

Zaman Majalisa Ya Yi Zafi, Sanata Barau da Ningi Sun Gwabza

  • ​Majalisar Dattawa ta dakatar da muhawara kan kudirin dokar noma da mataimakin shugaban majalisar, Barau Jibrin, ya gabatar
  • Sanata Abdul Ningi ya nuna damuwa kan yadda kudirin zai yi aiki da hukumomin noma da ake da su
  • Godswill Akpabio ya umarci Barau da ya raba wa dukkan sanatoci kwafin kudirin kafin su ci gaba da muhawara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Majalisar Dattawa ta dakatar da muhawara kan kudirin Dokar Gyaran Noma ta 2026, wanda mataimakin shugaban majalisar, Sanata Barau Jibrin, ya gabatar.

Matakin ya biyo bayan saɓani tsakanin sanatoci kan manufar kudirin da kuma rashin samun kwafinsa ga wasu ’yan majalisar.

Ningi da Barau sun yi cacar baki a ma
Sanata Abdul Ningi da Sanata Barau Jibrin Hoto: Barau I Jibrin, Abdul Ahmed Ningi
Source: Facebook

Sanata Ningi ya nemi ƙarin bayani kan kudirin

Jaridar TheCable ta ce rashin jituwa ya fara ne lokacin da Sanata Abdul Ningi, mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya, ya nuna damuwa kan abubuwan da kudirin ya ƙunsa da kuma yadda zai yi aiki tare da hukumomin da ake da su a ɓangaren noma.

Kara karanta wannan

Atiku ya soki DSS, ya fadi makircin da aka shirya domin hana shi gangamin kamfe a Sokoto

Ningi ya bayyana cewa manufar kudirin tana da kyau kuma ta zo a kan lokaci, amma ya ce akwai buƙatar ƙarin bayani kan manyan manufofinsa da yadda zai magance matsalolin da ke addabar harkar noma.

“Manufar wannan kudiri tana da kyau ƙwarai, abin a yaba ne, kuma ya zo a kan lokaci.” In ji shi.

Sai dai ya nuna mamakinsa kan yadda aka tsara kudirin, yana tambayar ko Barau ne da kansa ya ɗauki nauyin gabatar da shi, la’akari da tsawon lokacin da ya shafe a majalisar.

Ningi ya ce kudirin bai fayyace ko ana son kafa sabuwar hukuma ba ne, ko kuma yin gyara ga dokokin hukumomin da suke kula da harkokin ban-ruwa da samar da injinan noma.

Ya bayyana cewa duk da kyakkyawar manufar kudirin, akwai buƙatar sake duba shi domin tabbatar da cewa an fayyace abubuwan da yake son cimmawa.

Saboda haka, ya ba da shawarar dakatar da muhawarar domin Barau ya samu damar magance matsalolin da aka gano, The Punch ta kawo labarin.

Kara karanta wannan

Abubuwan da ya kamata ku sani game da tallafin N50,000 da aka fara turawa mutane a Najeriya

Barau ya kare matakin gabatar da kudirin

A martaninsa, Barau ya yi amfani da sashe na 79(1) na dokokin gudanar da zaman majalisar, inda ya ce a matakin karatu na biyu, abin da ya kamata sanatoci su tattauna shi ne fa’ida da illolin kudiri gaba ɗaya.

Ya jaddada cewa ba a wannan mataki ake shiga zurfin bayanan kowace ƙa’ida ko tanadin da ke cikin kudiri ba.

Barau ya ce an riga an wallafa kudirin a jaridar gwamnati, sannan an ɗora shi a dandalin WhatsApp na majalisar domin sanatoci su samu damar karanta shi.

Ya ƙara da cewa za a yi cikakken nazari kan dukkan tanade-tanaden kudirin a matakan da za su biyo baya na aikin dokoki.

Akpabio ya shiga tsakani

Rashin jituwar ta ƙara tsananta lokacin da Ningi ya nemi a nuna masa kwafin kudirin, inda ya tambayi Barau inda takardar take.

Barau ya amsa cewa an riga an raba kudirin a dandalin WhatsApp na majalisar, amma Ningi ya dage cewa bai samu kwafinsa ba.

Kara karanta wannan

Majalisa ta tsawaita dakatarwar da ta yi wa shugabannin ƙananan hukumomi 3 a Kano

Ningi ya ce: “Ina kudirin yake? Nuna min kwafi. Nuna min kwafi,”

Daga bisani, shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya shiga tsakani tare da umartar Barau da ya samar da kwafin takardar da za a raba wa dukkan sanatoci.

Akpabio ya ce bai kamata a dogara da dandalin WhatsApp kawai ba, musamman idan wasu sanatocin ba su samu damar ganin takardar ba.

Ya bayyana cewa ya kamata a dakatar da muhawarar har sai an raba wa kowa kwafin kudirin, domin su samu damar karanta shi kafin ci gaba da tattaunawa.

Barau ya yi cacar baki da Ningi
Sanata Barau Jibrin na jawabi a wajen taro Hoto: Barau I Jibrin
Source: Twitter

Akpabio ya yi zargi kan masu sukar Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa Godswill Akpabio, ya yi zargin cewa ana biyan wasu mutane kuɗi domin su riƙa sukar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da magoya bayansa a kafafen sada zumunta.

Shugaban Majalisar Dattawan ya kuma buƙaci matasan Arewa su ƙara ƙaimi wajen wayar da kan jama’a da neman goyon baya ga Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng