Majalisa Ta Tsawaita Dakatarwar da Ta Yi Wa Shugabannin Kananan Hukumomi 3 a Kano
- Majalisar Dokokin Jihar Kano ta tsawaita dakatarwar shugabannin ƙananan hukumomin Rogo, Bagwai da Bebeji
- Ta kuma ƙara wa kwamitin da ke binciken zarge-zargen da ake yi wa shugabannin wa’adin gudanar da aikinsa da watanni uku
- An dakatar da shugabannin ne tun da farko bisa zargin karya ƙa’idojin gudanar da harkokin kananan hukumomin da suke jagoranta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Majalisar Dokokin Jihar Kano ta tsawaita wa'adin dakatarwan da ta yi wa shugabannin ƙananan hukumomin Rogo, Bagwai da Bebeji da watanni uku.
Haka zalika, Majalisar ta kara wa kwamitin da ta kafa domin bincike kan zarge-zargen da ake wa ciyamomin lokaci da watanni uku domin gudanar da aikinsa yadda ya kamata.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Mai magana da yawun Majalisar dokokin jihar Kano, Kamaluddeen Sani-Shawai, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.
Ciyamomin da Majalisa ta dakatar
Shugabannin ƙananan hukumomin da abin ya shafa sun haɗa da Bello Abdullahi-Gadanya na Bagwai, Alhassan Salisu na Bebeji da Abubakar-Mustapha na Rogo.
A cewar sanarwar, majalisar ta yanke shawarar tsawaita dakatarwar shugabannin ne domin bai wa kwamitin wucin gadi da aka kafa damar ci gaba da binciken ƙorafe-ƙorafen da aka gabatar a kansu.
Haka kuma, majalisar ta ƙara wa kwamitin wa’adin aiki da watanni uku domin ya samu damar gudanar da cikakken bincike, nazarin dukkan ƙorafe-ƙorafen da kuma gabatar da rahoto ga ‘yan majalisar.
Dalilin ƙarin wa’adin dakatarwan
Kamaluddeen Shawai ya bayyana cewa tun da farko Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano ya bai wa kwamitin watanni uku domin gudanar da bincike mai zurfi kan zarge-zargen da ake yi wa shugabannin ƙananan hukumomin uku.
Ya ce bayan cikar wa’adin farko, majalisar ta ga bukatar ƙara wa kwamitin lokaci domin ya kammala aikinsa tare da miƙa rahotonsa.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Katsina ta fadi gaskiyar abin da ya faru da aka kona motocin APC a kamfe
A cikin sanarwar, Kamaluddeen ya ce:
“Yayin da wa’adin farko ya ƙare, majalisa ta tsawaita dakatarwar shugabannin da kuma wa’adin aikin kwamitinta da watanni uku."
Wannan na nufin cewa shugabannin ƙananan hukumomin uku za su ci gaba da kasancewa a dakatarwa yayin da kwamitin ke gudanar da ƙarin bincike kan batutuwan da aka gabatar a gabansa.

Source: Facebook
Zargin karya ƙa’idoji aiki
Leadership ta rawaito cewa majalisar ta dakatar da shugabannin ne tun da farko sakamakon zarge-zargen karya ƙa’idojin gudanar da ayyukan shugabanci a ƙananan hukumominsu.
Zarge-zargen sun shafi yadda shugabannin ke gudanar da harkokin hukumominsu, musamman batun bin ƙa’idojin da suka dace wajen aiwatar da ayyukan gudanarwa.
Majalisar Kano ta amince da nadin mutum 6
Kun ji cewa Majalisar dokokin jihar Kano ta tabbatar da naɗin mutum shida da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gabatar domin zama kwamishinoni.
Ta amince da sababbin kwamishinonin ne bayan wani ƙuduri da shugaban masu rinjaye, Lawan Hussaini, ya gabatar, wanda shugaban marasa rinjaye, Usman Abubakar, ya mara wa baya.
Sababbin kwamishinonin sun yi alƙawarin inganta tsaro, yaɗa ilimin kimiyya da fasaha da kuma yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi
Asali: Legit.ng
