Kungiyar Ansaru Ta Sake Fitar da Sabon Bidiyo kan Kisan Sheikh Masussuka
- Ƙungiyar ta’addanci ta Ansaru ta sake sakin bidiyon farfaganda, inda ta amince da kisan Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka a Katsina
- Ƙungiyar ta yi amfani da hujjojin addini da wasu abubuwan tarihi wajen ƙoƙarin kare kisan malamin
- Ansaru ta kuma yi nuni da kashe mutanen da ake zargi da ɓatanci ga Annabi a Arewacin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar..
Dutsin-Ma, Katsina - Ƙungiyar ta’addanci ta Ansaru ta sake sakin wani bidiyo kan kisan babban malamin Musulunci, Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka.
Kungiyar Ansaru ta ƙara amincewa da hannu a kisan fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka, wanda aka kashe a jihar Katsina.

Source: Facebook
Masussuka: Ansaru ta sake fitar da bidiyo
A cikin bidiyon mai tsawon mintuna tara da Premium Times ta gano wanda aka wallafa ranar 2 ga Nuwamba, 2026, ƙungiyar ta bayyana wasu hujjojin addini da tarihi da take amfani da su wajen ƙoƙarin halatta kisan malamin.
A ranar 26 ga Oktoba, 2026, ne aka harbe Sheikh Masussuka tare da abokinsa, Adamu Abubakar, a wajen gidansa da ke garinsu na Dutsin-Ma a jihar Katsina.
Bayan wasu sa'o'i da faruwar lamarin, Ansaru ta fitar da wani bidiyo mai ɗauke da hoton da ta yi amfani da shi wajen amincewa da kisan malamin.
Ƙungiyar ta yi zargin cewa ta kashe shi ne saboda ya ƙalubalanci wasu hadisai na Annabi Muhammad (SAW), tare da goyon bayan zaman lafiya tsakanin mabiya addinai daban-daban.
Sai dai wasu daga cikin magoya bayan marigayin sun yi watsi da ikirarin Ansaru, inda suka zargi wasu ɓangarori na ƙungiyar Izala da hannu a lamarin. Izala ta yi Allah wadai da kisan tare da musanta duk wata alaƙa da shi.
Ansaru ta yi amfani da hujjojin tarihi
A sabon bidiyon, wani mutum da ya rufe fuskarsa, sanye da kayan sojoji, ya bayyana dalilan da ƙungiyar ta ce suka sa ta kashe Sheikh Masussuka.

Kara karanta wannan
Abubuwan da ya kamata ku sani game da tallafin N50,000 da aka fara turawa mutane a Najeriya
Mutumin, wanda ke karanta bayanai daga wata na'urar Android, ya ce ƙungiyar ba za ta dogara da gwamnatin Najeriya da ya kira ta mai ridda ba wajen hukunta mutanen da ke ɓata wa Annabi suna.
Ya kuma kawo wasu misalai daga tarihin Musulunci, ciki har da kisan Ka'ab bn Al-Ashraf, wani mawaƙin Bayahude da ya rayu a Madina, wanda ya yi wa Musulmi ɓatanci tare da tunzura maƙiyan Annabi Muhammad (SAW).
Haka kuma, mai magana da yawun ƙungiyar ya ambaci wasu bayanai da ya danganta da malamin addinin Musulunci, Ibn Qayyim, domin ƙarfafa hujjojinsa na ƙoƙarin kare kisan.

Source: Original
Ansaru ta kawo misalan kashe mutane a Arewa
A cewar rahoton Premium Times, ƙungiyar ta kuma yi amfani da wasu misalan kisan jama'a da aka yi wa mutanen da ake zargi da ɓatanci ga addini a Arewacin Najeriya.
Ta yi iƙirarin cewa abubuwan da suka faru a baya ba su bambanta da kisan Sheikh Masussuka ba.
Ansaru, wadda aka danganta da hare-haren ta'addanci da dama a Arewacin Najeriya, ta taɓa ayyana marigayin a matsayin kafiri.
Rahotanni sun bayyana cewa Sheikh Masussuka ya shahara da ra'ayin bin Alƙur'ani kawai, inda wasu ke danganta shi da ƙungiyar Quraniyyun.
Masoyan Masussuka sun yi gagarumin taro
A baya, an ji cewa dubban mabiya marigayi Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka da malaman addinai sun halarci taron zaman lafiya na farko a Katsina.
An shirya taron ne domin inganta zaman lafiya da hakuri tsakanin mabiya addinai daban-daban, duk da kashe.
Sheikh Masussuka a gidansa Malaman addinai sun yi kira ga mabiyansa su kwantar da hankalinsu, tare da neman hukumomi su gano wadanda suka kashe shi.
Asali: Legit.ng

