Iran Ta Rataye Hoton Barazanar Kashe Donald Trump a Tehran

Iran Ta Rataye Hoton Barazanar Kashe Donald Trump a Tehran

  • Gwamnatin Iran ta ƙaddamar da wani babban allo a birnin Tehran mai ɗauke da saƙon barazanar kashe Shugaban Amurka, Donald Trump
  • Hoton ya nuna Trump a bayan gidan yari, yayin da wasu hotuna suka nuna shi da mataimakinsa da wasu jami'an Amurka da Isra'ila cikin jini
  • Masu zanga-zanga sun taru a dandalin Enghelab suna ɗaga tutoci ja tare da neman ɗaukar fansar kisan Ayatollah Ali Khamenei

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Tehran – Iran ta ƙara tsananta kalaman barazana ga Shugaban Amurka, Donald Trump, bayan ta ƙaddamar da wani babban allo da hotuna masu ɗauke da saƙon cewa za ta kashe shi a birnin Tehran ranar Talata.

Babban allon da aka rataye a dandalin Enghelab mai cunkoson jama'a ya nuna hoton Trump a bayan gidan yari, kansa a sunkuye, tare da rubutun da ke cewa: “Za mu kashe Trump.”

Kara karanta wannan

Abubuwan da ya kamata ku sani game da tallafin N50,000 da aka fara turawa mutane a Najeriya

Shugaba Donald Trump
Hotunan Trump da jami'an Amurka da aka kafa a Iran. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An saka hotunan Trump a Iran

The Hindu ta rahoto cewa wani allon da aka kafa kusa da na farko ya nuna Trump tare da mataimakinsa, JD Vance, wakilin musamman Steve Witkoff da Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu.

An nuna su cikin kaya yagaggu da fuskokinsu cikin jini, a gaban tutocin Amurka da Isra'ila da suka lalace.

Mutane da dama sun taru a dandalin suna kaɗa tutoci ja da ɗauke da hotuna masu rubutun “Jini zai zuba”, yayin da suke kira da a ɗauki fansar kisan tsohon jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei.

An kashe Khamenei ne a hare-haren haɗin gwiwar Amurka da Isra'ila a ranar 28 ga watan Fabrairun 2026, lamarin da ya haddasa yaƙin Gabas ta Tsakiya.

Shugaban Amurka, Donald Trump
Shugaba Donald Trump zai shiga jirgi. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An ƙara hotunan barazana a Tehran

Rahotanni sun nuna cewa a kwanakin baya, an riƙa kafa sababbin alluna da hotunan a sassan birnin Tehran domin yin ba'a ga Trump, barazanar ɗaukar fansa da kuma nuna cewa Iran ta yi nasara a yaƙin da Amurka.

Kara karanta wannan

Donald Trump ya sa sojojin Amurka kai sababbin hare hare Iran

A dandalin Tajrish da ke Arewacin Tehran, an shirya wani baje kolin zane-zane a fili, inda aka nuna hotunan Trump a salo daban-daban.

Ɗaya daga cikin zanen ya nuna Trump kwance a ƙasa fuskarsa cikin jini, yayin da ƙafa ke danne kansa. Wani kuma ya nuna bam ya rufe fuskarsa.

Haka kuma, an ajiye wani samfurin ɗakin gidan yari mai girman gaske, inda wani ɗan wasa da ke kwaikwayon Trump ya shafe yini a ciki. Wani allo kusa da wurin ya nuna hotunan barnar da hare-haren Amurka suka yi a Iran.

Ga bidiyon allon da Roya News ta wallafa a X:

Amurka ta kai hari Iran

A wani labarin, mun ruwaito cewa Amurka ta kai hare-hare a tsibirin Qeshm da ke mashigar ruwan Hormuz, kamar yadda jami'an Amurka suka shaida.

Jami'an sun bayyana hare-haren a matsayin waɗanda aka takaita kuma aka kai domin kare kai, bisa zargin cewa dakarun rundunar juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) sun harbi wani jirgin saman Amurka.

Biyo bayan hare-haren, kamfanin dillancin labaran gwamnatin Iran ya bayar da rahoton fashewar abubuwa a tsibirin Qeshm a daren Litinin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng