Dillalai, Masu Haya Za Su Faɗa Lukutar Masifa, Gwamnatin Tinubu Ta Gargaɗe Su
- Gwamnatin Tarayya ta yi gargadin cewa duk wanda ya ba ’yan ta’adda gidaje haya zai iya fuskantar hukunci
- NSA ya ce duk wanda ya taimaka wa ’yan ta’adda zai iya fuskantar hukuncin daurin shekara 20 a gidan yari
- Gwamnati ta kuma yi gargadi ga kamfanonin da ke karbar kudaden da suka shafi ta’addanci, tana mai cewa za a iya ci tararsu Naira miliyan 200
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Gwamnatin Tarayya ta gargadi masu gidaje da ke ba ’yan ta’adda hayar gidajensu, tana mai cewa yin hakan laifi ne da ka iya kai mutum ga fuskantar hukunci a karkashin dokar yaki da ta’addanci ta shekarar 2022.
Daraktan bangaren shari’a na ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Mijinyawa Zakari, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja.

Source: Twitter
Ya ce dokar ta haramta ayyuka daban-daban da suka shafi ta’addanci, ciki har da shirya ayyukan ta’addanci da kuma bayar da tallafi ga kungiyoyin ’yan ta’adda, cewar Vanguard.
An tanada masu hukuncin daurin shekara 20
Zakari ya bayyana cewa duk wanda aka samu yana taimaka wa ’yan ta’adda zai iya fuskantar hukuncin daurin akalla shekara 20 a gidan yari.
Ya kara da cewa ba da gidan haya ga dan ta’adda ma laifi ne, ko da kuwa ba a samu wanda ya aikata wani hari ko wani mummunan aiki ba.
A kalamansa:
“Idan aka karanta dokar hana ta’addanci ta shekarar 2022 da kyau, za a fahimci cewa sassa na 11 zuwa 33 sun kunshi laifuffuka daban-daban, ciki har da ayyukan shirya ta’addanci.
“Manufar ita ce tabbatar da cewa an fadada bincike zuwa dukkan bangarori. Idan ana maganar wadanda ke taimaka wa ’yan ta’adda, ana duba abin da bincike ya gano.

Kara karanta wannan
PRP ta yi kaca kaca da shirin Tinubu, ta taɓo batun kisan Sheikh Yahaya Masussuka
“Misali, taimaka wa ta’addanci yana jawo hukuncin daurin akalla shekara 20. Ba wa dan ta’adda gidan haya ma laifi ne. Ba lallai sai an samu wani hari ko mummunan aiki ba, duk wadannan abubuwa, ciki har da gudanar da taron shirin ta’addanci, laifuffuka ne.”
Ya bukaci ’yan Najeriya, musamman ’yan jarida da sauran masu ruwa da tsaki, da su karanta dokar domin fahimtar abubuwan da ake dauka a matsayin laifuffukan da suka shafi ta’addanci.
Gwamnati ta yi gargadi ga kamfanoni
Haka kuma, Zakari ya gargadi kamfanonin da ke karbar kudaden da suka fito daga ayyukan tallafa wa ta’addanci, yana mai cewa za su iya fuskantar hukunci mai tsanani.
Ya ce ko da kuwa ba a yi amfani da kudin wajen aikata wani laifi ba, kamfanin da ya karba zai iya fuskantar tarar Naira miliyan 200.
A cewarsa, za kuma a gurfanar da shugabannin kamfanin a gaban kotu, yayin da akwai yiwuwar rufe kamfanin gaba daya.
Ya bayyana cewa gwamnati na kara karfafa karfin hukumomin bincike domin gano mutanen da ke taimaka wa ta’addanci da kuma masu daukar nauyin ayyukan ’yan ta’adda.
Zakari ya ce yayin da ake kara inganta bincike, jama'a za su ga karin tuhume-tuhume a kan mutanen da ke da hannu a wadannan ayyuka, cewar Punch.
Ribadu ya fadi hanyar dakile ta'addanci
A wani labarin, an ji cewa Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro (ONSA), Nuhu Ribadu ya gano abubuwan da suka hana magance matsalar yan bindiga.
Nuhu Ribadu ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwar al’umma da haɗa kai tsakanin hukumomin tsaro domin kawo ƙarshen matsalar.
ibadu ya ce dole ne hukumomin tsaro su bambanta manyan masu aikata laifuffuka da masu fama da talauci wadanda za a iya yaudar.
Asali: Legit.ng

