Malam Nuhu Ribadu na da Hannu a Shigo da Makamai ga ‘Yan Bindiga? Gaskiya Ta Fito
- NCCSALW ta karyata wani bidiyo da ke zargin Mai Ba Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro, Nuhu Ribadu, da daukar nauyin shigo da makamai ba bisa ka’ida ba
- Hukumar ta ce an kama mutane biyu dangane da makamai 399 da hukumar kwastam ta kama a tashar Tin Can Island
- Shugaban hukumar, DIG Johnson Kokumo mai ritaya, ya ce ana ci gaba da bincike domin gano sauran wadanda ke da hannu a ciki da wajen Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Shugaban hukumar Dakile Yaduwar Kananan Makamai (NCCSALW), DIG Johnson Kokumo mai ritaya, ya karyata zargin Malam Nuhu Ribadu da hannu a shigo da makamai ba bisa ka'ida ba.
Kokuma ya musanta wani bidiyo da ya yadu yana zargin cewa Mai Ba Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro (NSA), Mallam Nuhu Ribadu na da hannu a shigo da makamai ba bisa ka’ida ba ta tashar Tin Can Island.

Kara karanta wannan
Lauya ya tsage gaskiya, an ji dalilin da ya sa Amurka ba ta kama Shugaba Tinubu ba

Source: Facebook
A rahoton Vanguard, Kokumo ya bayyana bidiyon a matsayin labarin karya yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja ranar Talata.
Ya ce shi da kansa ya halarci wurin da Hukumar Kwastam ta Najeriya ta mika makamai iri daban-daban guda 399 da aka kama a tashar Tin Can Island ga cibiyar NCCSALW.
An kama wadanda suka shigo da makamai
Kokumo ya ce mutanen da aka kama dangane da shigo da makaman suna tsare, yayin da bincike ke ci gaba.
Ya ce:
“Na kasance a tashar Tin Can Island tare da Kwanturola Janar na Kwastam. Hukumar Kwastam ta Najeriya ta kama makamai masu sarrafa kansu iri daban-daban guda 399 a tashar.
“An mika wadannan makamai da aka shigo da su ba bisa ka’ida ba ga hukumarmu. Ban je a matsayin wakili ba, ni da kaina na halarta. Kwanturola Janar na Kwastam ma da kansa ya halarta domin mika makaman.”
“Yayin da nake magana da ku yanzu, makaman suna cikin wurin ajiya mai tsaro. Mutane biyu da aka kama dangane da shigo da makaman ba bisa ka’ida ba suna hannun jami’an tsaro.
Kokumo ya karyata hannun Ribadu
Shugaban NCCSALW ya ce zarge-zargen da ke cikin bidiyon wanda ya kunshi alakanta Nuhu Ribadu da wadanda aka kama da shigo da makaman, ba su da tushe.
Ya ce:
“Saboda haka, abin da ke yawo a cikin bidiyon ba gaskiya ba ne, kuma ba zai iya zama gaskiya ba.”

Source: Facebook
Kokumo ya ce gwamnatin tarayya za ta ci gaba da lalata makaman da aka kwato domin hana su sake komawa hannun masu aikata miyagun laifuffuka da kungiyoyin da ba na gwamnati ba, cewar rahoton Gaurdian.
Ya ce lalata makaman da aka kama ya yi daidai da yarjejeniyoyin kasa da kasa da Najeriya ta rattaba hannu a kansu karkashin Majalisar Dinkin Duniya, Tarayyar Afirka da kungiyar ECOWAS.
Nuhu Ribadu ya gargadi yan Najeriya
Kun ji cewa mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu ta yi kira ga ’yan Najeriya su ƙara taka-tsantsan da ɗaukar matakan kariya.
Ribadu ya bayyana cewa akwai buƙatar jama’a su kasance cikin shiri game da yiwuwar sake tabarbarewar matsalolin tsaro a wasu wurare da ke cikin ƙasar nan.
Asali: Legit.ng
