Nuhu Ribadu Ya Jero Abubuwa 4 da Suka Hana Magance Matsalar 'Yan Bindiga a Najeriya
- Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro (ONSA), Nuhu Ribadu ya gano abubuwan da suka hana magance matsalar yan bindiga
- Nuhu Ribadu ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwar al’umma da haɗa kai tsakanin hukumomin tsaro domin kawo ƙarshen matsalar
- Nuhu Ribadu ya ce dole ne hukumomin tsaro su bambanta manyan masu aikata laifuffuka da masu fama da talauci wadanda za a iya yaudara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu ya gano dalilin da suke kara ta'azzara matsalar yan bindiga a Najeriya.
Nuhu Ribadu ya ce gibin bayanan sirri, raunin tsaron iyakoki, safarar makamai ba bisa ƙa’ida ba da kuma ɗaukar matasa masu rauni aikin ta'addanci su ne manyan abubuwan da ke ƙarfafa ayyukan ’yan bindiga.

Source: Facebook
Tribune Nigeria ta ruwaito cewa sakamakon haka, ya yi kira da a ƙarfafa sa hannun al’umma da haɗa kai tsakanin hukumomin tsaro domin fatattakar masu aikata laifuffukan.
Ribadu ya yi jawabi kan yan bindiga
Nuhu Ribadu, wanda Daraktan Ayyukan Shari’a a ofishinsa, Lauya Zakari Usman Mijinyawa, ya wakilta, ne ya bayyana hakan a wani babban jawabi yayin taron tattaunawa kan hanyoyin shawo kan matsalar ’yan bindiga.
Ƙungiyar Sokoto Advancement Forum ce ta shirya taron tare da haɗin gwiwar Cibiyar Nazarin Zaman Lafiya ta Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato, a ranar Asabar.
Taron ya haɗa jami’an tsaro, sarakunan gargajiya, masana ilimi, wakilan gwamnati da ƙungiyoyin farar hula domin samar da hanyoyin magance matsalar rashin tsaro da ke ci gaba da addabar al’ummomi a faɗin jihar.
Yadda ayyukan ’yan bindiga suka sauya
Ribadu ya ce ayyukan ’yan bindiga sun wuce satar shanu, fashi da garkuwa da mutane, inda suka koma ƙwace iko da wasu yankuna, karɓar haraji ba bisa ƙa’ida ba daga mutanen karkara da kuma kawo cikas ga harkokin tattalin arziki.

Kara karanta wannan
Yan Najeriya sun maida martani da Tinubu ya ce ba zai iya zuwa kamfe wasu jihohi ba
Ya ce bayyanar ƙungiyar Lakurawa, wadda Gwamnatin Tarayya ta ayyana a matsayin ƙungiyar ta’addanci, na nuna yadda matsalar tsaro ke ƙara alaƙantuwa da hanyoyin sadarwar masu tsattsauran ra’ayi na ƙasashen waje da ke aiki a yankin Sahel.
Ribadu ya ce:
“Kusancin Sakkwato da Jamhuriyar Nijar da kuma faɗin yankin Sahel ya ƙara sanya matsalar ta shafi tsallaka iyakokin ƙasashe.
“Saboda haka, dole ne mu haɗa ayyukan tsaro da suka dogara da bayanan sirri, ingantaccen kula da iyakoki, haɗin gwiwar ƙasashen yankin da kuma ci gaba da ɗaukar matakai kan samar da makamai ba bisa ƙa’ida ba."

Source: Facebook
Sojoji kaɗai ba za su iya ba
Ya jaddada cewa ayyukan soji kaɗai ba za su samar da zaman lafiya mai ɗorewa ba idan ba a samu tattara bayanan sirri, amincewar jama’a, farfaɗo da tattalin arziki da dawo da gwamnati a yankunan da aka ƙwato daga hannun ’yan bindiga ba.
Nuhu Ribadu ya ce dole ne hukumomin tsaro su bambanta manyan masu aikata laifuffuka da mutanen da ke cikin mawuyacin hali waɗanda za a iya yaudarar su su shiga ƙungiyoyin ’yan bindiga.
Nuhu Ribadu ya nuna damuwa
Kun ji cewa Nuhu Ribadu ya bayyana damuwarsa kan yadda ƙungiyoyin 'yan ta'adda ke ƙara dogaro da fasahohin zamani irin su AI, Kirifto, da jirage marasa matuka wajen gudanar da ayyukansu.
Ribadu ya ƙara da cewa Najeriya tana aiki kafada da kafada da ƙungiyar AU domin mayar da cibiyar NCTC ta zama zakara a fannin yaƙi da ta'addanci a yankin Yammacin Africa da Sahel.
Asali: Legit.ng
