Ana Dakon Bayani daga NCDC da Wata Bakuwar Cuta Ta Kashe Mutane 30 a Najeriya
- Ana ci gaba da dakon bayani daga hukumar Kula da Cututtuka ta Ƙasa (NCDC) kan wata bakuwar cuta d ta yi ajalin mutum kusan 30 a Jihar Zamfara
- Masana kiwon lafiya a jihar sun ce har yanzu ba a gano musabbabin cutar ba, yayin da ake zargin tana da alamun zazzaɓin cizon sauro
- An tura tawagar gaggawa zuwa yankin tare da aika samfurin jinin marasa lafiya dakin gwaje-gwaje domin gano cutar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zamfara, Nigeria - Hukumar Kula da Cututtuka ta Ƙasa (NCDC) ta yi gum da bakinta kan wata sabuwar cuta da ta barke a wasu yankunan jihar Zamfara.
An fara sukar NCDC kan rashin bayar da sahihin bayani cikin lokaci game da cutar, wacce har yanzu ba a gano ba, a ba a gano ba, da ta barke a ƙaramar hukumar Shinkafi ta Jihar Zamfara.

Kara karanta wannan
Abin tausayi: Yan bindiga sun tare magidanci da ya ɗauko gawar matarsa daga jihar Kano

Source: Twitter
Cuta ta kashe mutane a Zamfara
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa zuwa yanzu ana zargin bakuwar cutar ta yi sanadin mutuwar mutum kusan 30, kuma har yanzu babu wani bayani daga NCDC.
Duk da yadda jama’a ke nuna damuwa da kuma hasashen da ake yi na cewa cutar na iya kasancewa Ebola, hukumar da ke kula da sa ido kan yaɗuwar cututtuka a ƙasa ba ta fitar da cikakken bayani kan lamarin ba.
Hakan ya sa har yanzu ake da tambayoyi kan irin cutar da ake fama da ita, yawan mutanen da ta shafa da kuma matakan da ake ɗauka domin shawo kan matsalar.
Sai dai masanin cututtuka na Jihar Zamfara, Dakta Ahmad Muhammad Gusau, ya yi watsi da rahotannin da ke cewa an samu ɓarkewar cutar Ebola a jihar.
Duk da haka, ya tabbatar da cewa an samu mutuwar mutum kusan 30 tun bayan bullar cutar da ba a gano ba.

Kara karanta wannan
Ciyaman ya sha da ƙyar da miyagun yan daba suka farmaki wurin zaɓen fitar da gwanin APC
Har yanzu ba a gano sunan cutar ba
Gusau, wanda ya tattauna da Leadership, ya ce har yanzu ba a gano musabbabin cutar ba, inda ya bayyana cewa mutanen da ta kama suna nuna alamun da suka yi kama da na zazzaɓin cizon sauro.
Ya ce Ma’aikatar Lafiya ta Zamfara ta tura tawagar gaggawa zuwa Shinkafi domin gudanar da bincike, yayin da aka tattara samfurori daga marasa lafiya aka aika da su zuwa Babban Dakin Gwaje-gwaje na Ƙasa domin yin gwaje-gwaje.
A cewarsa, sakamakon gwaje-gwajen ne zai taimaka wajen gano ko cutar zazzaɓin dengue ce, chikungunya ko kuma wata cuta da ke haddasa zazzabi.
Ya jaddada cewa jihar ba za ta iya bayyana takamaiman cutar da ake fama da ita ba har sai an samu sakamakon gwaje-gwajen.
Mutanen da suka mutu da cutar
Masanin cututtukan ya kuma bayyana cewa wasu daga cikin mutanen da aka ruwaito sun mutu suna da wasu cututtuka da suka daɗe suna fama da su, ciki har da ciwon suga da hawan jini.

Kara karanta wannan
Tashin hankali: Jirgin sama ya gamu da hatsari yana tsakiyar tafiya, ya faɗo a cikin gari

Source: Original
Ya ce kasancewar waɗannan cututtuka na ƙara wahalar tantance ko duk mace-macen da aka samu sun samo asali ne kai tsaye daga cutar da ba a gano ba.
Sai dai rashin samun takamaiman sakamakon bincike ya ƙara nuna muhimmancin buƙatar NCDC ta fito ta yi wa jama’a cikakken bayani kan halin da ake ciki.
Ana zargin mutum 2 sun kamu da Ebola
Kun ji cewa hukumar NCDC ta gano mutum biyu da ake zargin sun kamu da cutar Ebola a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.
Hukumar ta bayyana cewa an killace mutanen biyu, yayin da ake ci gaba da gano sunayen waɗanda suka yi mu’amala da su da kuma gudanar da gwaje-gwaje
Asali: Legit.ng