Abin Tausayi: Yan Bindiga Sun Tare Magidanci da Ya Dauko Gawar Matarsa daga Jihar Kano
- ’Yan bindiga sun yi garkuwa da wani mutum da wasu mutum biyar da ke jigilar gawar matarsa daga Kano zuwa garinsu na Okpoga a Jihar Benue
- Maharan sun bar gawar matar a cikin motar bayan sun tafi da mutanen shida a yankin Adoka na ƙaramar hukumar Otukpo
- Masu garkuwar sun tuntubi iyalan waɗanda abin ya shafa, inda suka buƙaci Naira miliyan 15 a matsayin kuɗin fansa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zamfara, Nigeria - Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da wani magidanci da wasu mutum biyar da ke tafiya da gawar matarsa daga Jihar Kano zuwa garinsu na Okpoga da ke ƙaramar hukumar Okpokwu a Jihar Benue.
An ruwaito cewa maharan sun sace mutanen ne a daren ranar Juma’a a yankin Adoka da ke ƙaramar hukumar Otukpo, yayin da suka bar gawar matar a cikin motar da suke ciki.

Kara karanta wannan
An kama mutum 3 kan zargin ƙona motar yan tawagar yakin neman zaben jam'iyyar APC

Source: Original
Leadership ta ruwaito cewa lamarin ya sake tayar da hankalin al’umma kan matsalar tsaro a hanyar Otukpo–Ogobia–Adoka, inda makamancin haka ya faru da wasu masu jigilar gawar mamaci a ƙasa da watanni biyar da suka gabata.
Yan bindiga sun sace masu rakiyar gawa
Wani rahoto da jaridar Daily Trust ta wallafa ya ce maharan sun tare mutanen ne da misalin ƙarfe 8 na dare, lokacin da suke gab da isa inda za su je.
Rahoton ya ƙara da cewa tafiyar tasu ta katse saura kusan awa ɗaya kafin lokacin da ake sa ran za su isa.
Mazauna yankin sun ce sun gano wata mota a yashe a gefen hanya da safiyar ranar Asabar, inda suka tarar da gawar wata mata a cikinta.
Daga baya ne suka fahimci cewa waɗanda ke cikin motar sun faɗa hannun masu garkuwa da mutane.
An ce jami’an Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) sun isa wurin, inda suka kwashe gawar matar zuwa ɗakin ajiye gawa da ke garin Adoka.
Yan bindiga sun nemi N15m
Da yake tabbatar da sabon lamarin, shugaban ƙaramar hukumar Otukpo, Prince Maxwell Ogiri, ya bayyana sace mutanen a matsayin abin takaici da kuma tashin hankali.
Ogiri, wanda ya ce direban motar abokinsa ne, ya tabbatar da cewa masu garkuwar sun nemi a ba su Naira miliyan 15 domin sakin mutanen.
Sai dai ya ce jami’an tsaro sun fara gudanar da ayyukan ceto domin tabbatar da dawowar waɗanda aka sace cikin aminci.

Source: Twitter
Wane mataki yan sanda suka dauka?
Haka kuma, kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Benue, DSP Peter Aondongu, ya tabbatar da sace mutanen, inda ya ce lamarin ya faru ne ranar Juma’a.
Aondongu ya ƙara da cewa jami’an tsaro na ƙoƙarin ganin sun ceto mutanen shida da aka yi garkuwa da su.
Yan bindiga sun kashe mutum 6
Kun ji cewa yan bindiga da ake zargin Fulani Makiyaya ne sun kai sababbin hare-hare kan wasu al’ummomi a Ƙaramar Hukumar Ukum ta Jihar Benue.
An ruwaito cewa an kashe aƙalla mazauna yankin shida a sababbin hare-haren da aka kai garuruwan Tse-Nyaku, Biliji da wasu kaiyuka a Mbatian da Mbazum.
Asali: Legit.ng
