Abin Ya Zo: NCDC Ta Gano Mutum 2 da Ake Zargin Sun Kamu da Cutar Ebola a Arewacin Najeriya
- Hukumar NCDC ta gano mutum biyu da ake zargin sun kamu da cutar Ebola a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya
- An killace mutanen, yayin da ake gano waɗanda suka yi mu’amala da su tare da gudanar da gwaje-gwajen ƙwayoyin cuta
- Hukumar yaki da cututtukan ta yi gargaɗin cewa ba a tabbatar da kamuwa da cutar ba sai an samu sakamakon gwaje-gwaje
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hukumar Kula da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Ƙasa (NCDC) ta gano mutum biyu da ake zargin sun kamu da cutar Ebola a yankin Arewa maso Gabas na Najeriya.
Hukumar ta bayyana cewa an killace mutanen biyu, yayin da ake ci gaba da gano sunayen waɗanda suka yi mu’amala da su da kuma gudanar da gwaje-gwaje a dakunan binciken ƙwayoyin cuta.

Kara karanta wannan
Baƙuwar cuta ta ɓulla a ƙananan hukumomi 2 a Najeriya, mutane sun fara shiga wani hali

Source: Getty Images
Hakan na kunshe ne a cikin wani sako da hukumar NCDC ta wallafa a shafinta na X yau Asabar, 31 ga watan Oktoba, 2026 wanda ya shafi halin da ake ciki game da cutar Ebola.
An gano karin mutum 2 a Arewa
Hukumar NCDC ta ce:
"An gano mutane biyu da ake zaton suna dauke da cutar Ebola a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya."
"An killace su duka biyu, ana kuma ci gaba da gano tare da rubuta sunayen mutanen da suka yi tuntuɓe ko hulɗa da su, sannan ana gudanar da gwaje-gwajen bincike a dakin gwaje-gwaje."
NCDC na jiran sakamakon gwaje-gwaje
A cikin bayanin, NCDC ta gargaɗi jama’a da kada su ɗauki waɗannan mutanen a matsayin waɗanda aka tabbatar sun kamu da cutar, inda ta ce sai an samu sakamakon gwaje-gwaje kafin tabbatar da hakan.
“Kasancewar an ware mutane a matsayin waɗanda ake zargin sun kamu da cutar ba yana nufin an tabbatar da cewa suna ɗauke da Ebola ba nd; tabbatarwa zai dogara ne da sakamakon gwaje-gwajen ƙwayoyin cuta,” in ji hukumar.

Kara karanta wannan
"Kamar yana raye," Abubuwan da aka ji mabiyan Sheikh Masussuka na fada a wurin jana'iza

Source: Twitter
Shawarar NCDC ga ’yan Najeriya
NCDC ta buƙaci ’yan Najeriya su ci gaba da kula da tsaftar hannu, tabbatar da tsaftar muhalli tare da bin shawarwari da umarnin hukumomin kula da lafiyar jama’a domin kauce wa yiwuwar kamuwa da cutar
Hukumar ta ƙara da cewa za ta ci gaba da sanar da jama’a sababbin bayanai yayin da ta samu sahihan bayanai da aka tantance kan yaduwar Ebola a kasar nan.
Bakuwar cuta ta bulla a Zamfara
A wani labarin, kun ji cewa ma’aikatar lafiya ta jihar Zamfara ta ce an samu mutum 38 da suka kamu da wata bakuwar cuta da ba a gano asalinta ba a kananan hukumomi 2.
Ma’aikatar lafiya ta ce ta tura tawagar gaggawa mai ƙwararru daga fannoni daban-daban, ƙarƙashin jagorancin Daraktan Kiwon Lafiyar Jama’a, Dakta Yusuf Abubakar.
An tura tawagar ne domin binciken cutar da aka ruwaito, tare da ƙarfafa ayyukan sa ido da kuma ɗaukar matakan gaggawa a al’ummomin da abin ya shafa.
Asali: Legit.ng