Tashin Hankali: Jirgin Sama Ya Gamu da Hatsari Yana tsakiyar Tafiya, Ya Fado a Cikin Gari

Tashin Hankali: Jirgin Sama Ya Gamu da Hatsari Yana tsakiyar Tafiya, Ya Fado a Cikin Gari

  • Mutum tara da ke cikin wani ƙaramin jirgin kasuwanci sun mutu bayan jirgin ya faɗo a unguwar da mutane ke rayuwa a jihar Florida ta Amurka
  • Jirgin ya faɗo ne kusa da Cresthaven da misalin ƙarfe 12.50 na rana, inda ya haddasa babbar gobara kusa da gidaje da babbar hanya
  • Har yanzu hukumomi na binciken musabbabin hatsarin, yayin da ba a tabbatar ko wani mutum a ƙasa ya jikkata ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Amurka - Rahotanni sun nuna cewa mutum tara sun mutu bayan wani ƙaramin jirgin kasuwanci ya faɗo a unguwar da mutane ke rayuwa a jihar Florida da ke kasar Amurka.

Jirgin samfurin Learjet ya faɗo ne kusa da yankin Cresthaven da misalin ƙarfe 12.50 na rana bisa agogon yankin, inda ya haddasa wata babbar gobara kusa da gidaje da kuma babbar hanyar mota.

Kara karanta wannan

An kama mutum 3 kan zargin ƙona motar yan tawagar yakin neman zaben jam'iyyar APC

Jirgin sama
Jirgin sama yana tsakiyar tafiya a sararin samaniya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Sakataren Sufuri na Amurka, Sean Duffy, ya tabbatar da mutuwar mutanen tara da ke cikin jirgin, tare da miƙa ta’aziyyarsa ga iyalansu da masoyansu, kamar yadda jaridar Strait Times ta ruwaito.

“Cikin jimami muna yi wa iyalai da masoyan waɗanda muka rasa a wannan hatsari alhini da addu’a,” in ji Duffy.

Jirgin ya tashi daga Texas

Bayanai sun nuna cewa jirgin ya tashi ne daga filin jirgin sama na Austin-Bergstrom da ke jihar Texas, inda yake kan hanyarsa ta zuwa filin jirgin sama na North Eleuthera a ƙasar Bahamas lokacin da hatsarin ya afku.

Hotunan bidiyon da suka nuna yadda lamarin ya faru sun nuna jirgin yana gangarowa daga sararin samaniya da hancinsa a ƙasa kafin ya fashe, kuma ya haifar da wata babbar gobara kusa da motocin da ke wucewa.

Rahotanni sun ce hatsarin ya bar wani babban rami a saman hanya, yayin da jirgin ya kusa faɗawa kan gidajen da ke kusa da wurin.

Kara karanta wannan

Bincike ya gano shan fitsari da sauran azabar da mutanen da suka mutu hannun NSCDC suka sha

Jirgin ya taba mutanen gari?

Har yanzu ba a tabbatar ko akwai mutanen da suka jikkata a cikin matafiya ko mazaunin yankin sakamakon hatsarin ba.

Wata mata da ke aiki a yankin ta ce wutar lantarki ta ɗauke kusan sa’o’i biyu bayan faruwar lamarin, kamar yadda jaridar Leadership ta kawo a rahotonta.

Hukumomi na ci gaba da bincike domin gano yanayin da ya haddasa hatsarin da kuma dalilin faɗuwar jirgin.

Hatsarin jirgi.
Yadda jami'an agaji suka rufe titin da jirgin sama ya fado a Amurka Hoto: Saul Martinez
Source: AFP

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a samu cikakken bayani kan sunayen waɗanda suka mutu ko girman barnar da aka yi wa gidajen da ke kusa da wurin ba.

Jirgin sama ya yi hatsari a Kenya

Kun ji cewa jirgin sama mai saukar ungulu ya yi hatsari a Dutsen Ololokwe da ke Samburu a Kenya, inda dukkan mutane shida da ke cikinsa suka mutu.

Jami'an kula da hadurran jiragen sama sun tabbatar da cewa dukkanin mutane shida da ke cikinsa suka rasa rayukansu a hatsarin.

KCAA ta ce jirgin da hatsarin ya rutsa da shi samfurin Eurocopter EC130 B4 ne, inda ta ce tana hada kai da hukumomin da abin ya shafa wajen gudanar da ayyukan ceto da bincike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262