Bakuwar Cuta Ta Ɓulla a Kananan Hukumomi 2 a Najeriya, Mutane Sun Fara Shiga Wani Hali

Bakuwar Cuta Ta Ɓulla a Kananan Hukumomi 2 a Najeriya, Mutane Sun Fara Shiga Wani Hali

  • Ma’aikatar lafiya ta jihar Zamfara ta ce an samu mutum 38 da suka kamu da wata bakuwar cuta da ba a gano asalinta ba
  • An fi samun masu fama da cutar a ƙaramar hukumar Shinkafi, yayin da aka kuma samu wasu a garin Moriki da ke ƙaramar hukumar Zurmi
  • Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana cewa ta tura tawagar gaggawa domin binciken cutar da hana ta yaɗuwarta a cikin al'umma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zamfara – Ma’aikatar lafiya ta jihar Zamfara ta ce an samu mutum 38 da suka kamu da wata bakuwar cuta da ba a gano asalinta ba, inda aka fi samun masu fama da ita a ƙaramar hukumar Shinkafi.

Haka kuma, an samu wasu masu cutar a garin Moriki da ke ƙaramar hukumar Zurmi ta jihar da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Matasa sun shiga babbar matsala da suka jefi magoya bayan APC a tawagar gwamna

Dauda Lawal.
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal yana magana a wurin taroa Gusau Hoto: Dauda Lawal
Source: Facebook

Tashar Channels ta ce tahoton da Cibiyar Kula da Ayyukan Gaggawa kan Lafiyar Jama’a (PHEOC) ta ma’aikatar ta fitar ya nuna cewa an gano mutanen da suka kamu da cutar ne zuwa ranar 29 ga Oktoban 2026.

Hakan ya sa ma’aikatar ta tura tawagar gaggawa domin binciken halin da ake ciki tare da ɗaukar matakan hana cutar ci gaba da yaɗuwa.

Alamomin cutar da aka gano

Ma’aikatar lafiya ta ce ta tura tawagar gaggawa mai ƙwararru daga fannoni daban-daban, ƙarƙashin jagorancin Daraktan Kiwon Lafiyar Jama’a, Dakta Yusuf Abubakar.

An tura tawagar ne domin binciken cutar da aka ruwaito, tare da ƙarfafa ayyukan sa ido da kuma ɗaukar matakan gaggawa a al’ummomin da abin ya shafa.

A wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na ma’aikatar ya fitar, an bayyana cewa mutanen da cutar ta shafa na fama da alamomi da suka haɗa da zazzabi, ciwon kai, rashin cin abinci, amai, ciwon jiki da kuma raunin jiki.

Kara karanta wannan

'Ba dalilin zaɓenka ba kenan': Ƴan Najeriya sun fusata da Tinubu ya je Makka addu'a

Ana ci gaba da binciken cutar

Binciken farko da likitoci suka gudanar ya nuna yiwuwar wasu cututtuka da suka haɗa da zazzaɓin cizon sauro, ciwon ciki da kuma cutar sankarau.

Sai dai ma’aikatar ta ce akwai buƙatar ci gaba da binciken samfuran da aka ɗauka a dakin gwaje-gwaje domin gano ainihin cutar da ke addabar mutanen.

A halin yanzu, tawagogin likitoci suna duba marasa lafiya a cibiyoyin kiwon lafiya da ke Moriki da Shinkafi, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Likitocin suna kuma bayar da muhimman magunguna da kayan aikin jinya, tare da tattara samfuran marasa lafiya domin kai su dakin gwaje-gwaje a jihar Sokoto.

Zamfara.
Taswirar jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Kwamishinar lafiya ta jihar, Dakta Nafisa Maradun, ta buƙaci mazauna yankunan da lamarin ya shafa da su garzaya asibiti cikin gaggawa idan suka fara jin ɗaya daga cikin alamomin cutar.

Ta kuma gargaɗe su kan shan magani ba tare da umarnin likita ba, tare da ba su shawarar su ba jami’an lafiya cikakken haɗin kai yayin da ake ci gaba da bincike da ɗaukar matakan shawo kan lamarin.

Kara karanta wannan

An tura fitacciyar fim kurkuku kan zargin fitar da hoton tsiraici

Yadda cutar diphtheria ke yaduwa

Kun ji cewa hukumar NCDC ta bayyana cewa galibin wadanda suka kamu da cutar mashako watau diphtheria ba su yi rigakafi ba.

Ta kuma jero jihohi takwas da cutar ta fi yaduwa, wadanda ta ce 98% na masu dauke da wannan cuta suna wadannan jihohi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262