Sojoji Sun Yi Barin Wuta kan 'Yan Ta'adda, Sun Tarwatsa Maboyarsu

Sojoji Sun Yi Barin Wuta kan 'Yan Ta'adda, Sun Tarwatsa Maboyarsu

  • Dakarun sojin Najeriya sun lalata wata maboyar waɗanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne a dajin Edimogbo da ke jihar Kogi
  • Sojojin sun kwato harsasai 1,000, babura shida, wayar hannu da wasu kayayyaki daga sansanin da suka kai samame
  • Rundunar sojin ta ce ana ci gaba da bincike a yankin domin gano waɗanda ake zargin sun tsere bayan ganin dakarun

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kogi – Dakarun sojin Najeriya da ke aiki ƙarƙashin rundunar 21 Battalion Quick Reaction Force (QRF) sun lalata wata maboyar waɗanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne a dajin Edimogbo, ƙaramar hukumar Igalamela/Odolu ta jihar Kogi.

Mukaddashiyar daraktar hulɗa da jama'a ta rundunar sojin Najeriya, Kanal Appolonia Anele, ce ta bayyana hakan ga manema labarai ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Mutane 17 da ƴan bindiga suka sace a wurin ibada sun rasa rayukansu

Sojojin Najeriya a bakin aiki
Wasu dakarun Najeriya a bakin aiki. Hoto: Kwara State Government
Source: Facebook

A sakon da rundunar sojin Najeriya ta wallafa a Facebook, Anele ta ce dakarun sun kuma kwato tarin harsasai da wasu kayayyaki yayin samamen da suka kai sansanin.

Yadda sojoji suka kai samame

Kanal Anele ta bayyana cewa samamen ya biyo bayan samun sahihan bayanan sirri daga jama'a da ke nuna cewa wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun fake a cikin dajin.

Ta ce bayan samun bayanan, dakarun sun gaggauta tashi domin gano waɗanda ake zargin tare da cafke su ko kuma dakile ayyukansu.

A cewarta, lokacin da sojojin suka kusanci maboyar, waɗanda ake zargin sun hango su, suka harba bindiga domin sanar da sauran mambobin ƙungiyarsu, sannan suka tsere zuwa cikin dajin.

Ta ƙara da cewa sojojin sun bi sawun waɗanda suka tsere zuwa cikin dajin, amma ba su yi karo da su ba. Duk da haka, sun lalata sansanin da dukkan gine-ginen da ake amfani da su a wurin.

Kara karanta wannan

Donald Trump ya sa sojojin Amurka kai sababbin hare hare Iran

Taswirar jihar Kogi
Taswirar jihar Kogi a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Kayayyakin da aka kwato

Kakakin rundunar ta ce daga cikin kayayyakin da sojojin suka kwato akwai harsasai 1,000 masu girman 7.62mm da manyan cokula biyu na tona ƙasa.

Daily Trust ta rahoto cewa sauran kayayyakin sun haɗa da famfon hannu guda ɗaya, wayar hannu, na'urar haɗa intanet ta Glo, sabulu da jarkar man fetur.

Haka kuma, sojojin sun kwato tufafi, takalma da babura guda shida daga sansanin da suka fatattaki 'yan ta'addan.

Kanal Anele ta ce har yanzu dakarun na ci gaba da bincike a sauran sassan yankin domin gano inda waɗanda ake zargin suka nufa bayan tserewa.

Ta bayyana cewa manufar binciken ita ce gano mutanen tare da kawo ƙarshen ayyukan laifuffukan da ake zargin suna aikatawa.

An kashe 'yan sanda a Zamfara

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu 'yan bindiga sun kashe jami'an 'yan sanda biyar bayan sun yi wa motar da suke ciki kwanton ɓauna a hanyar Sokoto zuwa Gusau.

Kara karanta wannan

An kama mutum 3 kan zargin ƙona motar yan tawagar yakin neman zaben jam'iyyar APC

Jami'an suna tafiya ne a cikin motar sufuri ta jama'a ta jihar Zamfara a ranar Litinin da yamma, lokacin da maharan suka tare motar tare da buɗe musu wuta.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan, Abdullahi Faruk, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an kai gawarwakin jami'an zuwa ɗakin ajiyar gawa a Sokoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng