Rigiji Gabji: Dakarun Sojoji Sun Yi Kazamin Fada da 'Yan Ta'adda, an Kashe Mayaka da Dama

Rigiji Gabji: Dakarun Sojoji Sun Yi Kazamin Fada da 'Yan Ta'adda, an Kashe Mayaka da Dama

  • Dakarun Operation Hadin Kai sun dakile harin ‘yan ta’adda kan Kukawa, inda suka kashe mayaka 26 tare da tilasta wa sauran maharan ja da baya.
  • Sojojin sama sun kai hare-hare kan ‘yan ta’addan da ke tserewa, inda aka kashe 25 tare da lalata babura 10.
  • Dakarun sojojin sun kwato babura biyu da harsasai daban-daban bayan ci gaba da binciken wuraren da aka yi arangamar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Kukawa, Borno - Aƙalla sojoji huɗu sun jikkata yayin da dakarun Operation Hadin Kai suka dakile wani harin ‘yan ta’adda a garin Kukawa da ke Jihar Borno.

‘Yan ta’addan sun kai harin ne da misalin ƙarfe 10:50 na daren Juma’a kan sojojin Bataliya ta 101 Special Forces da aka jibge a Kukawa.

Sojoji sun kashe 'yan ta'adda a Borno
Dakarun sojojin Najeriya a fagen daga Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Getty Images

Mukaddashin Jami’in Yaɗa Labarai na Hedikwatar Joint Task Force (North East), Operation Hadin Kai, Kyaftin Mohammed Goni, ya bayyana hakan a wata sanarwa, a shafin Facebook.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun harbe shugaban jam'iyyar APC, sun tafi da mutumin da suke tare

Ya ce sojojin sun mayar da martani cikin gaggawa ta hanyar amfani da harbin bindigogi kai tsaye da kuma na manyan makamai.

Sojoji sun tilasta musu ja da baya

Goni ya ce ƙarfin harbin sojojin ya tilasta wa ‘yan ta’addan janyewa daga yankin zuwa hanyar Cross Kauwa.

Ya ce yayin artabun, an kashe wasu daga cikin maharan, yayin da wasu kuma aka ga suna tserewa da raunukan harbin bindiga.

Bayan haka, sojojin sun gudanar da bincike a yankin tare da gano gawarwakin wasu daga cikin ‘yan ta’addan, abin da ya tabbatar da asarar da suka yi.

An kashe ‘yan ta’adda 25 daga sama

Yayin da ‘yan ta’addan ke ja da baya zuwa Cross Kauwa a kan babura, rundunar sama ta Operation Hadin Kai ta samu umarnin dakile musu hanyar tserewa.

Kyaftin Goni ya ce duk da matsalar yanayi, jiragen saman sojojin sun yi nasarar kai hari kan wasu daga cikin maharan da suka fake a ƙarƙashin bishiyoyi. A cewarsa, harin saman ya kashe kimanin ‘yan ta’adda 10.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun tarfa yan ta'adda fiye da 20 a daji, sun yanke masu hukunci nan take

Haka kuma, na’urorin leƙen asiri, sa ido da gano ababen da ke cikin iska na MNJTF sun gano wasu babura kusan 20 da ke ɗauke da ‘yan ta’addan da ke tserewa zuwa yankin Tunbuns/Kangarwa.

Bayan samun bayanan, rundunar sama ta kai wani sabon harin da ya kashe ƙarin ‘yan ta’adda 15 tare da lalata babura 10.

An kwato babura da harsasai

A yayin binciken da sojojin ƙasa suka ci gaba da yi, sun gano babura biyu tare da kashe wani ɗan ta’adda guda.

Sojojin sun kuma kwato harsasai iri-iri da wasu kayayyakin da ake zargin maharan na amfani da su wajen gudanar da ayyukansu.

Rundunar ta ce haɗin gwiwar sojojin ƙasa da na sama ya taimaka wajen tarwatsa harin, dakile hanyar tserewar maharan da kuma hana su sake haɗuwa domin ci gaba da kai hare-hare.

Sojoji sun hallaka 'yan ta'adda a Borno
Taswirar jihar Borno, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ta ƙara da cewa aikin ya ƙara raunana ƙarfin ‘yan ta’addan da kuma ikon su na sake tattara ƙarfi ko gudanar da hare-haren daɗaɗɗu a yankin.

Sojoji sun kashe 'yan ISWAP, Boko Haram

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun rundunar hadin gwiwa ta Operation Hadin Kai sun kashe sama da ’yan ta’addan Boko Haram da ISWAP 21 a jihar Adamawa.

Dakarun sojojin sun kashe 'yan ta'addan ne a wani samame da suka kai kan sansanin ’yan ta’addan a yankin tsaunin Kopre Mountain da ke karamar hukumar Hong ta jihar Adamawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng