'Yan Bindiga Sun Tafka Barna bayan Yi Wa 'Yan Sanda Kwanton Bauna a Zamfara
- ’Yan bindiga sun yi wa wasu jami’an ’yan sanda kwanton ɓauna a lokacin da suke tafiya cikin motar haya ta Bazamfara zuwa Gusau
- Majiyoyi sun ce wasu jami’an sun rasa rayukansu, yayin da aka yi garkuwa da wasu daga cikinsu
- ’Yan sandan na kan hanyarsu ne domin samar da tsaro a zaɓen fidda gwani na APC na mazabar Sanatan Zamfara ta Arewa a Kaura Namoda
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Zamfara - 'Yan bindiga sun kai wa wasu jami’an ’yan sanda hari a ranar Litinin, 2 ga watan Nuwamba yayin da suke tafiya cikin motar sufuri ta gwamnatin jihar Zamfara, wadda aka fi sani da Bazamfara.
'Yan bindigan sun yi wa 'yan sandan kwanton bauna ne a kan hanyarsu ta zuwa Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

Source: Facebook
Tashar Channels tv ta ce wata majiya da ke wajen da lamarin ya faru ta bayyana cewa wasu daga cikin jami’an ’yan sandan da ke cikin motar sun rasa rayukansu sakamakon harin kwanton ɓaunar.

Kara karanta wannan
Dubu ta cika: Mai garkuwa da mutane ya shiga hannu yana kokarin karbar kudin fansa
Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a iya tabbatar da ainihin adadin waɗanda suka mutu ko suka jikkata ba.
An sace 'yan sanda a kan hanya
Wasu majiyoyi a rundunar ’yan sanda sun bayyana cewa jami’an na kan hanyarsu ne domin samar da tsaro a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC na mazabar Sanatan Zamfara ta Arewa.
Ana gudanar da zaɓen ne a ƙaramar hukumar Kaura Namoda ta jihar Zamfara.
Majiyoyin sun ƙara da cewa baya ga jami’an da aka ruwaito sun mutu a harin, maharan sun kuma yi garkuwa da wasu daga cikin ’yan sandan da ke cikin motar.
Mutum na wa harin ya ritsa da su?
Har yanzu ba a fayyace cikakken yadda harin ya faru ba, haka kuma ba a bayyana sunayen jami’an da abin ya shafa ba.
Wannan na zuwa ne yayin da bayanai kan adadin waɗanda suka mutu da kuma waɗanda aka yi garkuwa da su ba su fito fili ba.

Kara karanta wannan
Aminu Abdulsalam ya bayyana mutanen da yake zargi da yunkurin hana shi takara a Kano
Lokacin da aka tuntubi jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar Zamfara, ya ce ba su da ikon yin magana kan lamarin saboda yana ƙarƙashin ikon rundunar ’yan sanda ta shiyya.
Rundunar Zone 10 ta tabbatar da harin
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sanda ta Zone 10, Abdullahi Ambursa, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Sai dai Ambursa ya ce a lokacin da aka tuntube shi yana asibiti, saboda haka ba zai iya yin ƙarin bayani kan harin ba. Ya yi alƙawarin cewa rundunar za ta fitar da sanarwa a hukumance daga baya domin bayyana ƙarin bayanai kan lamarin.
Asali: Legit.ng