Mutane 17 da Ƴan Bindiga Suka Sace a Wurin Ibada Sun Rasa Rayukansu

Mutane 17 da Ƴan Bindiga Suka Sace a Wurin Ibada Sun Rasa Rayukansu

  • Kungiyar CSW ta bayyana cewa akalla masu ibada 17 da aka sace yayin harin coci-coci uku a Ariko, Kaduna, sun mutu
  • An saki wasu mutane takwas bayan shafe watanni biyar a hannun masu garkuwa, yayin da wasu 12 suka tsere a lokuta daban-daban
  • Kungiyar ta kuma bayyana yadda ake cin zarafin mata da yara a hannun masu garkuwa, tare da kira ga gwamnati ta dauki mataki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna – Akalla masu ibada 17 da aka sace yayin wani hari kan coci-coci a garin Ariko, karamar hukumar Kachia da ke jihar Kaduna, sun mutu a hannun masu garkuwa da mutane.

Kungiyar Christian Solidarity Worldwide (CSW) reshen Najeriya ce ta bayyana hakan, inda ta ce an saki wasu mutum takwas bayan sun shafe watanni biyar a hannun masu garkuwa.

Kara karanta wannan

Da gaske an ɗaure mace kirista saboda ta sa musulmi ya yi ridda? An samu bayani

Yan bindiga sun kashe masu ibada 17 da suka sace a Kaduna
Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna. Hoto: Senator Uba Sani.
Source: Facebook

Babban jami'in gudanarwar kungiyar CSW a Najeriya, Fasto Dr Yunusa Nmadu, ne ya bayyana hakan yayin wani taro a cocin ECWA Goodnews da ke Kaduna, cewar Vanguard.

Yaushe aka sace mutanen?

An gudanar da taron ne domin bikin Ranar Addu'a ta Duniya ga Kiristocin da ake zalunta (IDOP).

Nmadu ya ce wadanda abin ya shafa na cikin masu ibada 37 da aka sace lokacin da 'yan bindiga suka kai hari kan coci-coci uku a garin Ariko.

Ya ce harin ya faru ne a ranar Lahadi, 5 ga Afrilu, 2026, lokacin da masu ibada ke gudanar da ayyukan ibada.

Masu ibada 17 sun mutu a hannun yan bindiga
Taswirar jihar Kaduna da ke fama da matsalar tsaro. Hoto: Legit.
Source: Original

An saki mutum 8, wasu 17 sun mutu

A cewar Nmadu, mutane 12 daga cikin wadanda aka sace sun samu damar tserewa a lokuta daban-daban, yayin da 17 suka mutu.

Ya kara da cewa daga bisani an saki sauran mutane takwas bayan sun shafe watanni biyar a hannun masu garkuwa da su.

Kara karanta wannan

An kama mutum 3 kan zargin ƙona motar yan tawagar yakin neman zaben jam'iyyar APC

Ya ce an sace mutum 11 a kauyen Awon, wanda shi ma yake cikin karamar hukumar Kachia, ranar 20 ga Afrilu, 2026.

A cewarsa, daya daga cikin wadanda aka sace ya tsere, yayin da aka tabbatar da mutuwar mutum shida, cewar Punch.

Ya bayyana cewa sauran mutum hudu na ci gaba da kasancewa a hannun masu garkuwa, watanni shida bayan sace su, kuma rahotanni sun nuna suna cikin mawuyacin hali.

An sace masu ibada 177 a Kajuru

Nmadu ya kuma tuna da sace masu ibada 177 daga coci-coci uku a garin Kurmin Wali, karamar hukumar Kajuru, jihar Kaduna.

Ya ce lamarin ya faru ne ranar Lahadi, 18 ga Janairu, 2026, lokacin da masu ibada ke gudanar da ayyukan addininsu.

A cewarsa, gwamnati ta fara musanta faruwar lamarin, amma daga baya ta amince da shi bayan kungiyoyi daban-daban, ciki har da CSW, sun shiga tsakani.

Cikin mata ya zube a hannun yan bindiga

An ji cewa wata mata mai juna biyu mai suna Jamila, wadda ’yan bindiga suka sace a Millennium City da ke Kaduna, ta shafe mako uku a hannun masu garkuwa da mutane.

Kara karanta wannan

An bude wa Tinubu dakin Ka'aba ya shiga, 'yan Najeriya sun yi martani

Wata majiya ta ce Jamila ta sanar da iyalanta cewa ta zubar da cikin da take ɗauke da shi, yayin da masu shiga tsakani ke ci gaba da ƙoƙarin ganin an kuɓutar da ita.

Satar mutane na ci gaba da addabar Millennium City, inda wasu iyalai ke zaman jiran dawowar ’yan uwansu da aka sace a hare-hare daban-daban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.