Donald Trump Ya Sa Sojojin Amurka kai Sababbin Hare Hare Iran
- Amurka ta kai hare-haren soji kan tsibirin Qeshm na Iran da ke mashigar ruwan Hormuz, a cewar wasu jami'an gwamnatin Amurka
- Rahotanni sun nuna cewa hare-haren sun zo ne bayan dakarun IRGC na Iran sun kai hari kan wani jirgin saman Amurka
- Lamarin ya faru ne gabanin zaɓen tsakiyar wa'adin Amurka, yayin da Shugaba Donald Trump ke fuskantar matsin lamba kan yaƙi da Iran
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America – Amurka ta ƙaddamar da hare-haren soji kan tsibirin Qeshm na Iran da ke mashigar ruwan Hormuz, yayin da rikicin da ke tsakanin ƙasashen biyu ke ci gaba da ɗaukar sabon salo.
Jami'an gwamnatin Amurka sun tabbatar da kai hare-haren, inda suka bayyana cewa matakin martani ne ga harin da dakarun rundunar juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) suka kai kan wani jirgin saman Amurka.

Source: Facebook
BBC ta ruwaito cewa hare-haren sun zo ne a daidai lokacin da ake tunkarar zaɓen tsakiyar wa'adin Amurka, wanda zai tantance ko jam'iyyar Republican ko Democrat ce za ta mallaki rinjayen kujerun Majalisar Dokokin ƙasar.
Me ya sa Amurka kai hari Iran?
Hukumomin Amurka sun bayyana hare-haren da aka kai kan tsibirin Qeshm a matsayin waɗanda ba su da faɗi sosai, inda suka ce martani ne ga harbin da dakarun IRGC suka yi kan wani jirgin saman Amurka.
A nata ɓangaren, kamfanin dillancin labaran gwamnatin Iran, IRNA, ya tabbatar da cewa an samu fashe-fashe da dama a tsibirin a ranar Litinin.
Trump na fuskantar matsin lamba
Hare-haren sun zo ne a daidai lokacin da Shugaba Donald Trump ke fuskantar raguwar goyon baya a sakamakon zaɓe da kuma matsin lamba daga wasu 'yan jam'iyyarsa ta Republican da ke son ya kawo ƙarshen yaƙin.
Trump ya bayyana wa manema labarai a ranar Litinin cewa ba ya cikin gaggawar ƙara tsananta hare-haren da Amurka ke kaiwa Iran.

Kara karanta wannan
An kama mutum 3 kan zargin ƙona motar yan tawagar yakin neman zaben jam'iyyar APC
A wata hira da ya yi, Al Jazeera ta rahoto ya ce:
"Ko ta wace hanya, za mu ɗauki wani mataki, amma babu gaggawa. Mun raunana su ta fuskar kuɗi. Ba su da kuɗi, ba su da man fetur, kuma jama'arsu sun fara gajiya da wannan hali."
Haka kuma, Trump ya bayyana cewa Amurka na iya kai hari kan wani wuri mai suna Pickaxe, wanda ake dangantawa da shirin nukiliyar Iran.
Ya bayyana hakan ne yayin wata hira, inda ya ce kai harin ba wani babban abu ba ne, kuma za a iya kammala shi cikin awa guda.

Source: Getty Images
Sai dai lokacin da wani ɗan jarida ya tambaye shi ko Amurka na shirin komawa kai manyan hare-hare kan Iran bayan zaɓen tsakiyar wa'adin, Trump ya musanta hakan.
Carlson ya gargadi Trump
A wani labarin, kun ji cewa fitaccen mai sharhi kan siyasar Amurka kuma ɗan jarida, Tucker Carlson, ya yi gargaɗin cewa Shugaba Donald Trump na iya amfani da makamin nukiliya a Iran.
Carlson ya yi zargin cewa Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, na matsa wa gwamnatin Trump lamba domin ta sake dawo da manyan hare-haren soji kan Iran.
Ya bayyana cewa wurin da ake zargin za a iya kai wa hari shi ne tsaunin Pickaxe da ke tsakiyar Iran, wanda ake dangantawa da shirin nukiliyar ƙasar.
Asali: Legit.ng

